Monday, 14 March 2022

RUBUTU NA 8: TARIHIN QARI'AI GOMA 10 DA RIWAYOYINSU 20 | تاريخ القراء العشرة ورواتهم

 قِرَاءَةُ الإِمَام

أبِـي عَمرو ابن العلاء البَصري
TARIHIN QARI'AI GOMA 10 DA RIWAYOYINSU 20
تاريخ القراء العشرة ورواتهم
RUBUTU NA: 8️⃣
Rubutawar
✍Habibu Muhammad shugaba
ABUBUWAN DA KE KARKASHIN WANNAN RUBUTUN
👇👇👇👇👇
ABUBUWA 5 DA WANNAN RUBUTUN YA KUNSA
1- WANENE AL-IMAM ABU AMR AMR AL-BASRY
2- SUWAYE MALAMAN AL-IMAM ABU AMR AMR AL-BASRY
3- MAGANAR MALAMAI AKAN AL-IMAM ABU AMR AL-BASRY
4- SUWAYE DALIBAN AL-IMAM ABU AMR AMR AL-BASRY
5- BAYANI AKAN QIRA'AR AL-IMAM ABU AMR AL-BASRY
1- WANENE AL-IMAM ABU AMR AMR AL-BASRY
Anyi Sabani akan Asalin sunan Abu amr al-basry
Wasu sukace Al-kunyarshi shine sunanshi(أبو عمرو), Wasu kuma sukace sunanshi Zabban, wasu suka fadi sunaye sabanin wadannan.
Wanda akafi Rinjayarwa shine ZABBAN
Sunanshi Zabban ibnil-Ala'i ibn ammar ibn Al-aryan ibn Abdullahi ibn Al-hussain ibn Al-haris ibn Jalhamah ibn Hajar ibn khuza'iy ibn Mazin ibn malik ibn Umar ibn tamim ibn murr ibn add ibn dabikhah ibn ilyas ibn mudar ibn ma'ad ibn Adnan.
Abu Amr Attaimy Al-maziniy Al-basry, Daya ne daga cikin القُرَّاء السبعة ( Wato QARI'AI 7 na Qur'ani)
Al-hafiz Abul-ala'i Al-hamzaniy yace: Wannan itace ingantacciyar nasabar Abu Amr Al-basry wacce masana Nasaba suka Tabbatar.
Abh Amr Al-basry ya kasance mafi sanin mutane Al-Qur'ani Mai Girma da kuma larabci
Abh Amr Al-basry ya kasance mai Gaskiya, mai Zuhudu, Mai Amana, mai yawan riko da Addini
An haifeshi a garin Makkah a shekara ta sittin da shida 68 bayan Hijrah.
An haifi Al-imam Abu Amr Al-basry a garin makkah, ya rayu a garin Basrah, ya Rasu a garin kufa.
Abu amr al-basry ya rasu a garin kufah, sai dai anyi sabani akan shekarar da ya rasu, wasu sukace ya rasu a shekara ta 154 bayan Hijrah, wasu sukace a shekara ta 155 bayan Hijrah, wasu sukace a shekara ta 157 bayan Hijrah, mafi nisan abunda aka fada akan shekarar da ya rasu itace shekara ta 158 bayan Hijrah.
Amma kuma maganar mafi yawan maluma itace ya rasu a shekara ta 154 bayan Hijrah, رحمه الله رحمة واسعة
2- SUWAYE MALAMAN AL-IMAM ABU AMR AL-BASRY
Al-imam Abu Amr Al-basry yafi kowa yawan Maluma daga cikin القُراء السبعة
Ga kadan daga Cikin Maluman shi:-
1- Anas ibn Malik رضي الله عنه
2- Hasanul-basriy
3- Humaid ibn 'Kais Al-a'araj
4- Sa'id ibn Jubair
5- Shaibah ibn nisah
6- Asim ibn Abin-najud Al-kufiy القارئ
7- Abdullahi ibn kathir Al-makky القارئ
8- Ada'u ibn Abi Rabah
9- Ikrimah Maula ibn Abbas رضي الله عنهما
10- mujahid ibn Jabr
Nan wasu ne kadan daga cikin maluman Abu Amr Al-basry da yayi karatu a gunsu baki-da-baki wasu kuma ta hanyar sauraro (سَمَاعًا)
3- MAGANAR MALAMAI AKAN ABU AMR AL-BASRY
Duk wanda ya tara wadannan ilmuka da kuma dabi'u na gari kamar yadda Abu Amr Al-basry ya tarasu dole ya samu yabo na kwarai daga malamai masana addini
Ga kadan daga Cikin Abubuwan da malamai suka Fada game da shi (Abu Amr Al-basry )
Abu Ubaidah yace:- Abu Amr Al-basry Ya dorawa kanshi cewa duk bayan kwana uku sai yayi saukar Al-Qur'ani Mai Girma.
Al-asma'iy yace:- Ban taba ganin wanda yafi abu Amr ilimi ba bayan wucewar shi.
Al-asma'iy yace:- Abu Amr yace min: "Da nasan yadda zanyi in kwashi ilimin dake kirjina in zubashi a kirjinka da nayi haka, Hakika na haddace ilmuka da dama da suka shafi ilmukan Al-Qur'ani wanda yakai da za'a Rubutasu Al-a'amash ( سليمان بن مهران الأعمَش) Bazai iya Daukar su ba, Da ba don Bazai yiyu inyi karatu ba sai da abunda magabata suka karanta Na Qur'ani (Qira'o'i) Da nayi karatu kala kaza da kala kaza! " Ya anbaci wasu harrufa daban na karatu.
Al-a'amash yace:- Wata rana Al-Hasanul-basriy ya zo zai wuce ta wurin Halkar Abu Amr ya isko mutane sunyi cikar kwari sun taru sun Dukufa ba abunda sukeyi illa karatu, sai Hasanul-basriy ya tambaya yace: wanene mai wannan Halkar? Sai akace dashi : Abu Amr ne, sai yace: لا إله إلا الله saura kiris maluma sun zamo iyayen jigi, Duk daukakar da ba'a Yimata ginshiki da katanga da ilimi ba to Kaskanci ne Karshenta".
SUFYAN IBN UYAINAH YACE : Nayi mafarkin Annabi صلى الله عليه وسلم sai na ce da manzon Allah صلى الله عليه وسلم : ya manzon Allah, Nau'i-Nau'i Na Qira'o'i sun Yawaita a gareni, Da Qira'ar wa kake umarta ta inyi karatu? Sai Annabi صلى الله عليه وسلم yace dashi : Da Qira'ar Abu Amr ibn Al-ala'.
Al-imam Ahmad ibn Hanbal yace: Qira'ar Abu Amr itace Mafi soyuwar Qira'a a gareni, Abu Amr yayi karatu ga ibn kathir da Mujahid da sa'id ibn Jubair, Su kuma sunyi karatu da ibn Abbas رضي الله عنهما shi kuma yayi karatu ga Ubayyu ibn ka'ab رضي الله عنه، shi kuma ubayyu yayi karatu ga Annabi صلى الله عليه وسلم.
Ibn mujahid yace: Malamai sun bamu labari daga Wahab ibn Jarir yace : Shu'ubah ( شعبة ابن الحجاج البصري) yace dani : Kayi riko da Qira'ar Abu Amr Domin Zata Kasance is'nadi (Abun riko) ga mutane.
IBN AL-JAZARIY YACE: Hakika abunda Shu'ubah ya fada ya Tabbata, Domin Kuwa Qira'ar da mafi yawan mutane suke karatu da ita a yau (yana nufin zamaninshi da yake wannan Maganar) a a garin Sham da Hijaz da Yemen da Misra itace Qira'ar Abu Amr al-basry, yana ma da wahala yana koya Qur'ani bada Qira'ar shi ba, musamman A bangaren فرش الحروف ( ban-bancin Hadaka na Qira'o'i) Duk da cewa suna sabawa a bangaren الأصول ( banbancin daidaiku na Qira'o'i), mutanen Sham Sun kasance suna Karatu da Qira'ar IBN AMIR tun zamanin ibn Amir Har zuwa wuraren shekara ta dari biyar 500 bayan Hijrah, Sai suka bar Karatu da Qira'ar ibn Amir din, saboda wani daga cikin Malamai yazo sham daga Iraq, ya cigaba da karantar da Mutane Qira'ar Abu Amr A masallacin AL-UMAWIY, mutane kuwa suka taru a wajenshi ana koyon wannan Qira'ar, wannan Qira'ar ta shahara a wannan Garin, ya kuma dade yana koyar dasu tsawon Shekaru, IBN AL-JAZARIY Yace wannan shine labarin da ya zomin dangane da sanadin barin Qira'ar Ibn Amir da mutanen sham sukayi suka koma suna Karatu da Qira'ar Abu Amr, idan ba wannan ba kuma Bansan sanadin da yasa suka barta ba, IBN AL-JAZARIY yace ina kirga wannan a daya daga cikin Karamomin Shu'ubah.
ABU AMR AL-ASADIY YACE :- A lokacin da labarin Rasuwar Abu Amr yazomin naje wurin Yayanshi na yimusu ta'aziyyar rasuwarshi, ina wurin sai YUNUS IBN HABIB yazo yace dasu (yayan abu Amr): muna yimuku Ta'aziyya haka kuma muna yiwa kanmu Ta'aziyya ta wanda bamu taba ganin irinshi ba a wannan zamani (yana nufin Abu Amr), yace : wallahi da za'a Rabawa mutane 100 Ilimin Abu Amru da Zuhudun shi Da duk sun kasance Malamai kuma masu Zuhudu, Wallahi da Annabi صلى الله عليه وسلم zaiga (Abu Amr) Da yayi farin ciki Dashi saboda yadda yake.
Wannan shine wani yanki daga cikin maganar maluma akan Abu Amr da rayuwar shi
والله أعلم
4- SUWAYE DALIBAN AL-IMAM ABU AMR AL-BASRY
Haka Kuma idan muka dawo ta gefen Daliban shi zamu fahimci cewa Al-imam Abu Amr Al-basry yanada dalibai masu dinbin yawa duba da lokacin da ya rayu lokaci ne na neman ilimi da yadashi.
Ga kadan daga Cikin Daliban shi
1- Ahmad ibn musa Al-lu'ulu'iy
2- Hussain ibn Ali Al-ju'ufiy
3- kharijah ibn mus'ab
4- khalid ibn Jabalah Al-yashkuriy
5- Sahl ibn Yusuf
6- Abdulrahim ibn musa
7- Abdullahi ibn Al-mubarak
8- Abdulmalik ibn Kuraib Al-asmu'iy
9- ubaid ibn Akil
10- yahya ibn Al-mubarak Al-yazidiy ( يَحْيى اليَزِيدِيّ)
Kadan kenan daga cikin Daliban Al-imam Abu Amr al-basry
5- TAKAITACCEN BAYANI AKAN QIRA'AR AL-IMAM ABU AMR AL-BASRY
Qira'ar Abu Amr Al-basry dayace daga cikin Qira'o'in Al-Qur'ani mai girma kuma itace ta uku 3 a jerin Qira'o'in, daga Qira'ar Al-imam Nafi'u sai Qira'ar Al-imam ibn kathir sai Qira'ar Abu Amr Al-basry.
AL-IMAM AHMAD IBN HAMBAL yace: Qira'ar Abu Amr itace Mafi soyuwar Qira'a a gareni, Abu Amr yayi karatu ga ibn kathir da Mujahid da sa'id ibn Jubair, Su kuma sunyi karatu da ibn Abbas رضي الله عنهما shi kuma yayi karatu ga Ubayyu ibn ka'ab رضي الله عنه، shi kuma ubayyu yayi karatu ga Annabi صلى الله عليه وسلم.
QIRA'AR Abu Amr tanada riwayoyi biyu kamar yadda sauran Qira'o'i suke da biyu-biyu, Ga su kamar haka
1- Riwayar Abu umar Hafs Al-duriy 150-246A.H
2- Riwayar Abu shu'aib Salih ibn Ziyad As-susiy, wanda ya rasu a shekara ta 261A.H
GA WANI BAYANI MAI MUHIMMANCI DA YA KAMATA MU SANI
👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇
mu sani cewa Duriy da Susiy Basuyi Karatu Kaitsaye (Baki da baki) Ga Abu Amr ba, sunyi karatu ne ga Yahya ibn Al-mubarak Al-yazidiy ( يَحْيَى اليَزِيدي) wanda Imamus-shadibiy yake cewa Game da shi :
= أَفَاضَ عَلى يَحْيَى اليَزِيديِّ سَيْبَهُ
فَأَصْبَحَ بِالعَذْبِ الفُرَاتِ مُعَلَّلا
= أبُو عُمَرَ الدُّوري وَصَالِحُهمْ أبو
شُعَيبٍ هُو السُّوسِيُّ عَنهُ تَقبَّلا
Fassara
= Abu Amr Al-basry ya kwaranyawa yahyal-yazidiyyi Baiwarshi ( iliminshi) yahya ya kasance kosasshe saboda ingantaccen ilimin da ya kwnkwada daga Abu Amr.
= Abu umar Ad-dury da kuma salihu mai Alkunya Abu Shu'ai wanda shine Ake kira Susi, Sun karbi Qira'ar Abu Amr a gareshi (يَحْيَى اليَزِيديِّ).
Ma'ana dai Akwai wasida a tsakanin su da Abu Amr
Nayi bayani a rubutu na na farko cewa
Wadanda ake Jinginawa riwayoyi (Masu Riwaya) Sun kasu gida uku
1- akwai wadanda sukayi karatu baki da baki ga QARI'AI da ake jinginawa riwayarsu zuwa garesu kamar
- Qalun da warsh sunyi karatu baki da baki ga Nafi'u
2- Akwai wadanda A tsakaninsu da QARI'AN akwai wasidar Mutun Daya kamar
- Dury da susi Sunyi karatu ga Yahyal Yazidiyyi shi kuma yahya yayi karatu ga Abu Amr Al-basry
-Kamar Khalaf da khallad Sunyi karatu ga Sulaim shi kuma sulaim Yayi Karatu Ga Hamzah
3- Akwai wadanda akwai fiye da mutun daya a tsakaninsu da QARI'IN DA sukayi riwaya a gareshi kamar
- Bazzi da Qumbul basuyi karatu kai tsaye ga ibn kathir ba Akwai fiye da mutun daya a tsakanin su
Abun da yasa hakan ta faru shine
A lokacin da wannan ilimin na riwayoyi yayi yawa ya fadada riwayoyin sunyi yawa Kasancewar kowane Qari'i yanada dalibai masu dinbin yawa kuma kowane daga cikin su yana jingina riwayar shi zuwaga wannan Qari'in
Sai akayi niyyar Takaita Riwayoyin Akace kowane QARI'I zaa fitar da mutun biyu daga cikin Rawiyanshi (Dalibanshi) Wadanda sukafi kwarewa da kuma tsoron Allah Da tsantseni domin a jingina riwayar shi zuwa garesu
Sai a bincika Idan an samu wanda ya cika sharudan daga cikin Daliban QARI'IN, haka kuwa akayi Zabin Ya fada Ga Duriy da Susi sai aka aka cigaba da jingina Qira'ar Abu Amr Al-basry zuwa garesu, Riwayar su kuma ake jinginata kai tsaye zuwa gareshi (Abu Amr Al-basry) Sabanin asalin Malaminsu ( yahyal-yazidiyyi)
Wannan shine Ma'anar Fadar Shadibiyy
تَخَيرَهم نُقَّادُهُم كلَّ بَارِعٍ
وَلَيسَ عَلى قُرءَانِه مُتَأَكِّلا
Adadin Ayoyin Qur'ani na wannan Qira'ar 6214
An sanya adadin Al-madany Al-auwal ( wato tsarin Kirga Ayoyin Al-madany na farko) dama tsarin Qirga Ayoyin Qur'ani akwai
المَدَني الأول
المدني الثاني
Akwai na makkah da sham da kufa da Basrah,
جَعلتُ المَدينِي أَولاً ثم ءاخِرا
وَمَكٍ إلى شَامِِ وكوفٍ إلى بَصْري
Haka Shadibiyy yace a cikin littafinshi ناظمة الزهر في عد آي السور
عد المدني الأول
Shine kafatanin Mutanen basrah ke aiki dashi a mushaf na Abu Amr da ya'akub
Adadin ayoyin su sune Dubu shida da dari biyu da sha hudu 6214
RAMZIN QIRA'AR ABU AMR AL-BASRY
Al-imam As-shadibiy ya yiwa Qira'ar Abu Amr Ramzi ( wato alamar da zai rika yin nuni akan Qira'ar Abu Amr da ita), Ramzin shine
HUDDI (حُطِّي)
wato idan akaga Ramzi na harafin ح a cikin Shadibiyyah to yana nuni ne akan Abu Amr Al-basry
Idan akaga Ramzi na harafin ط yana nufin Duri an Abi Amr
Idan akaga Ramzi na harafin ي to yana nufin Susi
Duk da cewa zai iya kiran kowane daga cikin su da sunanshi ko lakabinshi kai tsaye idan wazanin wakar ya bayar da damar yin haka.
Muna yin rubutun ne a takaice da sai mu bayar da misalin ko wanne daga cikin su, amma idan an koma Shadibiyyah zaa samu misallansu da yawa.
WASU KALMOMI DA ABU AMR AL-BASRY YA KEBANTA DASU DAGA CIKIN QARI'AI 10
Wannan babin kuma zai yi muna magana akan wasu kalmomi da Qira'ar Abu Amr ta sabawa sauran Qira'o'i a wurin Fadar su.
Gasu kamar haka:-
Abun lura a nan shine:- Harufan da nayiwa wasali su nikeso inyi nuni akansu da kuma Haruffan da na canjawa digo,
Zan rubuta kalmar da ya sabawa Qira'o'i akanta in kuma biyota da wasu kalmomi ta yadda za'a fahimci ayar da nike nufi,
Wata kalmar kuwa ita kadai zan kawo ina nufin Duk inda tazo a cikin Qurani mai Girma
👇👇👇
1- Duk inda wadannan Kalmomin sukazo a Al-Qur'ani Abu Amr yana karantasu tareda Daure harafin Ra'un رْ da ke cikinsu Ga Kalmomin
يامُرْكم يامُرْهم تامُرْهم ينصُرْكم يشعِرْكم
Haka kuma yana daure Harafin Hamza ءْ a wannan بارِئْكم
Sai dai riwayoyin shi biyu (Dury da susi) sunada sabanin fuskoki a wadannan Haruffan, a nemi littafai domin neman karin bayani
2- وإنه للحق من ربك وما الله بغــٰفل عما يَعملون
3- ويسئلونك ماذا ينفقون قل العفوُ
4- لا تُفْتَحُ لهم أبواب السماء ولا يدخلون الجنة
5- أُبْلِغُكم duk inda tazo
6- نغفر لكم خَطَـــٰـــيَــــٰــكُم سنزيد المحسنين
7- مما خَطَـــٰـــيَــــٰــهُم أغرقوا فأدخلوا نارا
8- أن يَقولوا يوم القيامة إنا كنا عن هذا غفلين
9- أو يَقولوا إنما أشرك ءباؤنا من قبل
10- وما نرىك اتبعك إلا الذين هم أراذلنا بادئَ الرأي
11- قلن حــٰشَا لله su uku, tareda yin madda ga Harafin ش duk da cewa ba yadda na rubutashi ake rubutashi a Qur'ani ba anayin Ilhakin Harafin Madda ne a wurin ش ٰ
12- ألا يَتخذوا من دوني وكيلا
13- وكان له ثُمْرٌ فقال لصاحبه
14- وأحيط بثُمْرِه فأصبح يقلب كفيه
15- قالوا إن هَــٰذَيْنِ لسحران yana daure ya'un يْ duk da cewa ba yadda na rubuta ta ake rubuta ta Qur'ani ba ana yin ilhakin ta ne
16- فاْجْمَعُوا كيدكم ثم ائتوا صفا
17- يوم نَنفُخ في الصور ونحشر المجرمين
18- وما عند الله خير وأبقى أفلا يَعقلون
19- إن الله كان بما يَعملون خبيرا (2). سورة الأحزاب
20- وكان الله بما يَعملون بصيرا () إذ جاءوكم من فوقكم..
21- جنت عدن يُدخَلونها يحلون فيها
22- كذلك يُجزَىٰ كُلُّ كفور
23- الشيطـن سول لهم وأُمْلِيَ لهم
24- من بعد عن أظفركم عليهم وكان الله بما يَعملون بصيرا ()
25- والذين ءامنوا وَأََتْبَعْنَـــٰــهُم ذُرِّيَّــــٰـــتِهم بإيمان
25- وقد أُخِذَ مِيثَـــٰــقُكم إن كنتم مؤمنين
26- فأصدق وَأَكُونَ من الصدقين () ولن يؤخر الله نفسا...
27- وإذا الرسل وُقِّتَت
28- بل يُؤثرون الحيوة الدنيا
Yadda na rubuta wadannan Kalmomin abu Amr ne kadai ke karantawa haka, kar a manta da sharadin da na bayar cewa Wurin wasulla ne da Digagga sabanin yake
والله أعلم
A Nemi littafan da sukayi magana akan Wannan Riwayar domin neman karin bayani ta yiyu kila akwai abunda ya kamata mu saka bamu saka ba.
Anan zamu tsaya sai a taremu a rubutu na gaba inda zaa jimu da Bayani akan Riwayar Dury An abi Amr Al-basry insha Allah
JAN HANKALI
👇👇👇👇
Duk wanda Zaiyi sharing ko Kwafi Na wannan Rubutun nawa To ya yi Sharing Dinshi A yadda Na Rubutashi Kar ya kara komai kuma Kar ya canja komai abar shi yadda nayishi
Duk wanda yakeda Taaliki ko gyara Ko shawara ko Mulahaza akan Wannan Rubutun to ya atuntubeni nizan gyara Da kaina Amma Kar A canja Min rubutu.
Ga lambar da zaa tuntubeni da ita +2348034468543
✍️WANDA YA RUBUTA
Habibu Muhammad Shugaba
+2348034468543
Tuesday
01-01-1443
10-08-2021

No comments:

Post a Comment