TARIHIN QARI'AI GOMA 10 DA RIWAYOYINSU 20
تاريخ القراء العشرة ورواتهم
RUBUTU NA: ![2️⃣](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/t99/1/16/32_20e3.png)
![2️⃣](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/t99/1/16/32_20e3.png)
الإِمَـــــامُ نَــــافِــــعٍ الــــمَـــــدَنِـــــي
![✍](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/te2/1/16/270d.png)
ABUBUWAN DA KE KARKASHIN WANNAN RUBUTUN
![👇](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/t4f/1/16/1f447.png)

1- Wanene Al-imam Nafi'u
2-Suwaye Maluman Al-imam Nafi'u
3-Maganar Malamai Akan Al-imam Nafi'au
4- Suwaye Daliban Al-imam Nafi'u
4- Takaitaccen Bayani Akan Qira'ar Al-imam Nafi'u
1- WANENE AL-IMAM NAFI'U
SUNANSHI:- Nafi'u Dan Abdulrahman Dan Abu Nu'aim, Ana Yimishi Al-kunya Da ABU RUWAIM
Shidai Nafi'u Daya ne daga Cikin القراء العشرة Kuma daya ne Daga cikin manyan Maluman zamaninshi, shi Sika ne mai Gaskiya, Launin shi Bakar Fata ne, Yanada Kyakkyawar Mu'amalah Da halaye masu kyau, Masani ne Akan Qira'o'i Da kuma Larabci, Shine Shugaban QARI'AI Makaranta Qur'ani A garin Madinah Bayan Wucewar أبو جعفر المدني.
Al-imam Nafi'u ya kasance idan yana karatu ko yana magana Anajin Kamshin Turare Yana Fita Daga Bakinshi, Sai aka Tambayeshi aka ce mishi " Shin Kana Shafa Turare ne A duk Lokacin da zaka Fito Karatu? Sai yace: Aa Ni bana Sanya Turare, Sai dai ni wata rana Nayi Mafarkin Annabi صلى الله عليه وسلم yana Karatu A cikin Bakina Tun daga lokacin Bakina Yake Kamshin Turar"
Wannan shine Ma'nar Fadar الإمام الشاطبي da yake cewa :
فَأَمَّا الكَريمُ السرِّ في الطِّيبِ نَافعٌ
فَذاكَ الذي اخْتارَ المَدِينةَ مَنزِلا
An haifi Al-imam Nafi'u A shekara ta 70 bayan Hijrah
Ya Rasu A garin Madinah A shekara ta 169 Bayan Hijrah Yanada Shekara 99 A duniya (رحمه الله رحمة واسعة )
2-SUWAYE MALUMAN AL-IMAM NAFI'U
An Ruwaito Cewa Al-imam Nafi'u Yayi karatu Ga mutane 70 Daga cikin Tabi'ai
Daga cikin su Akwai
![👇](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/t4f/1/16/1f447.png)
![👇](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/t4f/1/16/1f447.png)
![👇](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/t4f/1/16/1f447.png)
![👇](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/t4f/1/16/1f447.png)
1- Abu ja'afar Al-madany ( Qari'i na 8 Daga cikin القراء العشرة)
2- Abdulrahman ibn Hurmuz Al-A'araj
3- Shaibah ibn Nisah
4- muslim ibn Jundub Al-huzali
5- Yazidu Ibn Ruman
6- Salih ibn khuwat
7- Al-asbag ibn Abdulazeez Al-nahwi
8- Al-zuhri muhammad ibn muslim ibn Shihab
9- Abdulrahman ibn Qasim Ibn muhammad ibn Abubakar Assiddiq
wannan itace Silsilar Qira'ar Al-imam Nafi'u Har zuwa Ga Annabi صلى الله عليه وسلم
Al-imam Nafi'u yayi Karatun Qurani Ga Abu ja'afar Al-madany ( Qari'i na 8 Daga cikin القراء العشرة) da kuma Abdulrahman ibn Hurmuz Al-A'araj, da kuma Shaibah ibn Nisah, da kuma muslim ibn Jundub Al-huzali, Da kuma Yazidu Ibn Ruman,
Duka Wadannan Biyar da na Jero sunayensu a sama Sunyi karatu A wurin Sayyidina Abu Hurairah رضي الله عنه da kuma Abdullahi ibn Abbas رضي الله عنهما da kuma Abdullahi Ibn Ayyash, Daga ubayyu ibn Ka'ab رضي الله عنه . Shi kuma Ubayyu Yayi Karatu Ga Annabi صلى الله عليه وسلم
3-MAGANAR MALAMAI AKAN AL-IMAM NAFI'U
Malamai Daban Daban-daban magabata Sunyi Maganganu da dama gameda Al-imam Nafi'u
Ga kadan Daga Cikinsu
![👇](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/t4f/1/16/1f447.png)
![👇](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/t4f/1/16/1f447.png)
![👇](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/t4f/1/16/1f447.png)
![👇](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/t4f/1/16/1f447.png)
IBN MUJAHID YACE : " Al-imam Nafi'u shine ya kasance Shugaban Masu Karatun Qurani A garin Madinah bayan Wucewar Tabi'ai" ya kara da cewa " Al-imam Nafi'u ya kasance masani a fannin Ilimin QIRA'AT, ya kasance mai biya akan Tafarkin magabata( Sahabbai Da Tabi'ai) na garin Madinah.
SA'ID IBN MANSUR YACE: Naji Malik dan Anas Yana Cewa Qira'ar mutanen madinah Sunnah ce, sai aka tambayeshi: Qira'ar Nafi'u yake nufi? Yace Eh.
ABDULLAHI IBN AHMAD IBN HAMBAL YACE: Na tambayi babana ( Ahmad bn Hambal) Wace Qira'a Tafi Soyuwa Agareka? Sai yace: Qira'ar mutanen Madinah, sai nace dashi, Bayan ita kuma fa? Sai yace: Qira'ar Asim.
QALOON YACE : Nafi'u ya kasance Daga cikin mafi tsarkin mutane Halaye na gari, Daga cikin Mafi Iya karatu daga cikin mutane, Haka kuma ya kasance mai Zuhudu kuma mai yawan kyauta, Ya yi Limanci A masallacin Annabi صلى الله عليه وسلم
Har tsawon Shekaru sittin 60
LAITH IBN SA'AD YACE : Nayi aikin hajji a shekara ta 113 bayan hijra Kuma Nafi'u shine Limamin masallacin Annabi صلى الله عليه وسلم a lokacin.
AL-IMAM MALIK YACE : a lokacin da aka tambayeshi gameda Basmalah sai yace: ku tambayi Nafi'u Domin kowane ilimi ana tambayarshi ga ma'abotanshi, Shi kuma Nafi'u shine Shugaban Mutanen Madinah a wurin Karatun Qurani.
AN HAKAITO CEWA: A lokacin da Ciwon ajali ya kama Nafi'u yayan shi sun nemi yayimusu wasiyyah sai yace dasu
اتقوا الله وأصلحوا ذات بينكم وأطيعوا الله ورسوله إن كنتم مؤمنين
Wato Kuji tsoron Allah Kuyi Sulhu a tsakaninku, kuyi da'a ga Allah da manzonshi idan ku kasance Muminai.
Al-imam Nafi'u ya Rasu a shekara ta 169 Bayan Hijrah Yanada Shekara 99 A duniya.
4- SUWAYE DALIBAN AL-IMAM NAFI'U?
An ruwato cewa Al-imam Nafi'u yayi shekara Sittin 60 Yana karantar da Qurani, wannan Yasa Dole zai tara Dalibai da yawa kusan ma zaace bazasu lissafu ba
Amma ga wasu daga cikin Daliban shi
1- Qalun
2- warsh
3- Isah ibn wardan ( Rawin Abu jaafar)
4- Sulaiman ibn jammaz( Rawin Abu jaafar)
5- malik bn Anas
6-khalid bn makhlad
7- Abdullahi bn wahab
8- Lais bn sa'ad
9- Ash'hab bn Abdulazeez
10- Musa bn DariQ
Da dai sauransu
5- TAKAITACCEN BAYANI AKAN QIRA'AR AL-IMAM NAFI'U
Qira'ar Nafi'u haka Take kamar sauran Qira'o'i Akwai wuraren da tayi muwafaqa da wasu Qira'o'in haka kuma akwai wuraren da suka sa6a
Haka kuma Akwai wuraren da QIRA'AR ta ke6anta ta karanta wasu kalmomi da wannan Sigar ma'ana Akwai kalmominda Nafi'u ya Sa6awa kowace Qira'a a wurin karanta su.
Qira'ar Nafi'u Tanada Riwayoyi biyu Kamar sauran Qira'o'i
![👇](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/t4f/1/16/1f447.png)
![👇](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/t4f/1/16/1f447.png)
![👇](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/t4f/1/16/1f447.png)
![👇](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/t4f/1/16/1f447.png)
![👇](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/t4f/1/16/1f447.png)
1- Qalun
2-Warsh
Kuma Su biyu Din dukansu sunyi karatu a gareshi Mushafahatan Baki da baki Har ma an riwaito cewa shine ya sakawa QALOON sunan QALOON Haka kuma shi ya sakawa Warsh sunan Warsh.
Ga Kadan daga Cikin Kalmomin da Qira'ar Nafi'u Ta Sa6awa kowace Qira'a a wurin Karantasu
![👇](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/t4f/1/16/1f447.png)
![👇](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/t4f/1/16/1f447.png)
![👇](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/t4f/1/16/1f447.png)
![👇](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/t4f/1/16/1f447.png)
Kalmomin da Nayiwa Wasali su nake nufin ya sabawa sauran Qira'o'i kuma yadda nayi wasalin Haka yake karantawa
![👇](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/t4f/1/16/1f447.png)
![👇](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/t4f/1/16/1f447.png)
![👇](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/t4f/1/16/1f447.png)
![👇](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/t4f/1/16/1f447.png)
1-حتى يَقُولُ الرسول والذين آمنوا معه
2- هل عَسِيتُمْ (سورة البقرة وسورة محمد صلى الله عليه وسلم )
3- قال الله هذا يَوْمَ ينفع الصـدقين صدقهم
4- فنظرة إلى مَيْسُرَةٍ
5- وإن تدعوهم إلى الهدى لا يَتْبَعُوكُمْ
6- ويقول أين شركاءي الذين كنتم تُشَآقُّونِ فيهم
7- والخـمسة أَنْ غَضِبَ اللهُ عليها
8- فأرسله معى رِدًا يصدقني
9- وما تَذْكُرُونَ إلا أن يشاء الله
10- في لوح مَّحْفُوظٌ
Wadannan sune wasu daga Cikin su
Kuma insha Allah zamu tsaya anan Ba don Abunda zaa fada Ya kare ba sai don takaitawa.
JAN HANKALI
![👇](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/t4f/1/16/1f447.png)
![👇](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/t4f/1/16/1f447.png)
![👇](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/t4f/1/16/1f447.png)
![👇](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/t4f/1/16/1f447.png)
Duk wanda Zaiyi sharing ko Kwafi Na wannan Rubutun nawa To ya yi Sharing Dinshi A yadda Na Rubutashi Kar ya kara komai kuma Kar ya canja komai abar shi yadda nayishi
Duk wanda yakeda Taaliki ko gyara Ko shawara ko Mulahaza akan Wannan Rubutun to ya atuntubeni nizan gyara Da kaina Amma Kar A canja Min rubutu.
Ga lambar da zaa tuntubeni da ita +2348034468543
![✍️](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/te2/1/16/270d.png)
Habibu Muhammad Shugaba
+2348034468543
Friday
01-11-1442
11-06-2021
No comments:
Post a Comment