Monday, 14 March 2022

RUBUTU NA 6: TARIHIN QARI'AI GOMA 10 DA RIWAYOYINSU 20 | تاريخ القراء العشرة ورواتهم

 رِوايةُ البَزِّي

عَن الإِمَامِ ابن كَثِيرٍ المَكي
TARIHIN QARI'AI GOMA 10 DA RIWAYOYINSU 20
تاريخ القراء العشرة ورواتهم
RUBUTU NA: 6️⃣
Rubutawar
✍Habibu Muhammad shugaba
ABUBUWAN DA KE KARKASHIN WANNAN RUBUTUN
👇👇👇👇👇
1- TAKAITACCEN TARIHIN BAZZY
2- WASU DAGA CIKIN MALAMAN BAZZY
3- WASU DAGA CIKIN DALIBAN BAZZY
4-BAYANI GAME DA USUL NA RIWAYAR BAZZY
1- TAKAITACCEN TARIHIN BAZZY
SUNANSHI :- Ahmad bn Muhammad bn Abdullah bn Qasim bn Nafi'u bn Abi Bazzah
LAQABINSHI :- Al-Bazzy
Sunan Bazzy nisba ce Zuwaga daya daga cikin kakanninshi Mai suna Abu Bazzah
Al-AHWAZY YACE :- Abu Bazzah wanda Ake jingina Sunan Bazzy Zuwa gareshi, Sunanshi BASSHAR Dan Qasar Farisa ne daga Cikin Ah'lu Hamzan, ya musulunta ne A hannun Assa'ib bn Abissa'ib Almakhzumy.
MAANARA kalmar Al-bazzah a yaren Farisa shine (QARFI) Abu Bazzah maana Baban QARFI.
ALKUNYARSHI :- Abul Hassan
Al-imamul Bazzy Yayi Ladanci (kiran sallah) a masallacin Ka'abah har tsawon Shekara 40 Arba'in
Kuma masanin Qur'ani ne makarancin ne, mai koyar da Qurani ne a Garin Makkah رحمه الله
An haifi Al-imamul Bazzy a shekara ta 170 dari da saba'in bayan Hijrah
Ya Rasu A shekara ta 250 dari biyu da Hamsin bayan Hijrah
Yanada Shekara 80 a rayuwarshi رحمه الله
2- WASU DAGA CIKIN MALAMAN BAZZY
Kasancewar an haifi Bazzy a lokacin da ilmuka suke cikin Bunkasa da kuma yawaita, wannan ne yasa yakeda malamai da yawa
Daga cikinsu akwai :-
1- muhammad bn Abdullah (mafaifin Bazzy)
2- Abdullahi bn Ziyad
3- Ikrimatu bn Sulaiman
4- Wahb bn Wadih
Da dai sauransu
GA WANI BAYANI MAI MUHIMMANCI DA YA KAMATA MU SANI
👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇
mu sani cewa Bazzy da Qumbul Basuyi Karatu Kaitsaye (Baki da baki) Ga ibn kathir ba
Akwai mutane a tsakaninsu da ibn kathir
Koda ibn Kathir ya rasu baa ma Haifesu ba
Saboda ibn kathir ya rasu a shekara ta 120
An haifi Bazzi a shekara ta 170
An haifi Qumbul a shekara ta 195
Nayi bayani a rubutu na na farko cewa
Wadanda ake Jinginawa riwayoyi (Masu Riwaya) Sun kasu gida uku
1- akwai wadanda sukayi karatu baki da baki ga QARI'AI da ake jinginawa riwayarsu zuwa garesu kamar
- Qalun da warsh sunyi karatu baki da baki ga Nafi'u
2- Akwai wadanda A tsakaninsu da QARI'AN akwai wasidar Mutun Daya kamar
- Dury da susi Sunyi karatu ga Yahyal Yazidiyyi shi kuma yahya yayi karatu ga Abu amr Al-basry
-Kamar Khalaf da khallad Sunyi karatu ga Sulaim shi kuma sulaim Yayi Karatu Ga Hamzah
3- Akwai wadanda akwai fiye da mutun daya a tsakaninsu da QARI'IN DA sukayi riwaya a gareshi kamar
- Bazzi da Qumbul basuyi karatu kai tsaye ga ibn kathir ba Akwai fiye da mutun daya a tsakanin su
Abun da yasa hakan ta faru shine
A lokacin da wannan ilimin na riwayoyi yayi yawa ya fadada riwayoyin sunyi yawa Kasancewar kowane Qari'i yanada dalibai masu dinbin yawa kuma kowane daga cikin su yana jingina riwayar shi zuwaga wannan Qari'in
Sai akayi niyyar Takaita Riwayoyin Akace kowane QARI'I zaa fitar da mutun biyu daga cikin Rawiyanshi (Dalibanshi) Wadanda sukafi kwarewa da kuma tsoron Allah Da tsantseni domin a jingina riwayar shi zuwa garesu
Sai a bincika Idan an samu wanda ya cika sharudan daga cikin Daliban QARI'IN to الحمد لله idan kuma baa samu ba sai a duba cikin Daliban daliban QARI'IN haka kuwa akayi har Zabin Yazo Ga Bazzi da Qumbul Da ire irensu
Wannan shine Ma'anar Fadar Shadibiyy
تَخَيرَهم نُقَّادُهُم كلَّ بَارِعٍ
وَلَيسَ عَلى قُرءَانِه مُتَأَكِّلا
Wannan RIWAYA Tanada Ayoyi 6220 Dubu shida da dari biyu da Ashirin
Wannan Adadin Na Ganshi ne a mus'hafin da nike dashi Na QIRA'AR IBN KATHIR 6220
Sai dai kuma Naga wani Adadin da ya sabawa wannan Adadin a wani littafi na QIRA'AR IBN KATHIR
Sunce Adadin Ayoyin Qira'ar ibn kathir sune 6210 dubu shida da dari biyu da goma
Wannan adadin shine Adadin da Abu Amr Addany ya riwaito Da sanadinshi Zuwa ga ibn kathir shi kuma ibn kathir ya Riwaito shi zuwa Ga mujahid ibn Jabr shi kuma mujahid Daga Abdullahi ibn Abbas رضي الله عنهما shi kuma Ibn Abbas Daga Ubayyu Ibn ka'ab رضي الله عنه
MU SANI CEWA Al-imamul Bazzy Baiyi karatu Kai tsaye (Baki da baki) ga Ibn kathir ba
Ga yadda Abun yake :-
Akwai wasidar wadannan mutanen tsakanin Bazzy da Ibn kathir
👇👇👇
Ikrimatu bn Sulaiman, Isma'il bn Abdullah Al-Qusd, Shibl bn Abbad, ABDULLAHI BN KATHIR. رحمهم الله
Wannan shine Maanar Fadar Al-imam As'shadiby
رَوَى أحمَد البَزِّي لَه وَمحَمدٌ
عَلَى سَنَد وَهْوَ الملَقَّبُ قُنبُلا
Ahmad Al-Bazzy da Kuma Muhammad sunyu Riwaya Gareshi(ibn kathir) da Sanadi (wasida) shi wannan Muhammad din Shine Akeyiwa Lakabi da QUMBUL
والله أعلم
KABBARORIN DA BAZZY YAKEYI IDAN ZAI SHIGA KOYACE SURAH DAGA سورة الضحى HAR ZUWA KARSHEN QURANI
Bazzy ya Koyar Da Dalibanshi Qur'ani tareda Yin Kabbara (الله أكبر) idan Zaa shiga Kowace Sura daga سورة الضحى Har zuwa Karshen QURANI
Ya kasance yana Cewa: Naji Malamina Ikrimah bn Sulaiman yana cewa : Nayi karatu ga Isma'il bn Abdullah bn Qusdandin, a lokacin da Nazo zan Shiga سورة الضحى yace dani : Yi kabbara a karshen Kowace sura, Saboda Ni nayi karatu ga Abdullahi bn Kathir, A lokacin da nazo Zan shiga سورة الضحى sai (ibn kathir) yace dani : Yi kabbara Har ka kai karshen QURANI, Ibn kathir ya bashi Labari cewa yayi Karatu Ga Mujahid, Mujahid ya Umarceshi da yin Haka (Kabbara) Shi kuma Mujahid ya sanar da Ibn kathir cewa: malamin shi Abdullahi bn Abbas رضي الله عنهما shine ya Umarceshi da yin Haka: Shi kuma Ibn Abbas رضي الله عنهما yacewa Mujahid : Ubayyu bn Ka'ab رضي الله عنه ne ya Umarceshi Da yin Haka, Shi kuma Ubayyu bn Ka'ab رضي الله عنه yace da ibn Abbas رضي الله عنهما : Annabi صلى الله عليه وسلم ne ya umarceshi da yin Haka
Wannan Shine Asalin Kabbarar Da Bazzy keyi Daga سورة الضحى zuwa Nasi
Ga Yadda Akeyinta
Idan Mutun ya Kare سورة اليل kafin ya shiga سورة
sai yace
الله أكبر، بسم الله الرحمن الرحيم، والضحى.....
Haka mutun zaiyi idan zai shiga Kowace sura har yakai Nasi
والله أعلم
3- WASU DAGA CIKIN DALIBAN BAZZY
Haka kuma Al-imamul Bazzy yanada dalibai masu Dinbin yawa daga cikinsu akwai :-
1- Al-hassan ibn Al-hubab
2- Ahmad bn Farh
3- muhammad bn ishaq Abu Rabi'ah
4- muhammad ibn Harun
5- musa bn Haru
6- mudar ibn Muhammad Addabbi
7- Abu Aliyu Al-haddad
8- Abu ma'amar Al-jumahi
9- Ishaq bn Muhammad Al-khuza'iy
10- muhammad bn Aliy Al-khadib
Da sauransu
4- BAYANI GAMEDA USUL NA RIWAYAR BAZZY
Wannan Sashen Kuma insha Allah Zai kunshi bayani Akan wadannan abubuwan da zan jero
👇👇👇👇👇
1- Bisimillah dake zuwa tsakanin surori
2- mimul-jam'i
3- Ha'ul-kinayah
4- Maddodi
5- Hukunce-hukuncen Hamzah
6- Hukuncin tsayawa akan Ha'utta'anis Wacce Aka Rubuta ta a harafin ت budadda
7- matsayin Bazzy akan Saktah السكتة da Hafs yakeyi a wurare 4 hudu
8- Al'izhar da Al'idgam
9- Ya'atul Idafah
10- Ya'atul zawa'id
1- BISIMILLAH DA KE ZUWA A TSAKANIN SURORI البسملة بين السورتين
Al-imamul Bazzy bai sabawa Hafs ba a wannan Babin wato yadda Hafs yakeda Fuskoki 3 haka shima Bazzy yakeda uku
Fuskokin da muka sani na hafs Awurin basmalah to sune Bazzy yakeda su
👇👇👇
1- قطع الجميع
Shine idan Ka gama sura Ka tsaya, Kayi bisimillah ka tsaya, sai ka shiga wata sura
Misali
ولم يكن له كفوا أحد، بسم الله الرحمن الرحيم، قل أعوذ برب الفلق
2- وَصلُ الجميع
Shine ka hade karshen sura da bisimillah da kuma farkon surar da take gaba ba tareda ka tsaya ba
Misali
ولم يكن له كفوا أحدٌ بِسم الله الرحمن الرحيمِ قُل أعوذ برب الفلق
3- قطع الأول، ووصل الثاني بالثالث
Shine idan ka gama sura ka tsaya, Sai kuma ka hade Bisimillah da farkon surar da take gaba ba tare da ka tsaya ba.
Misali
ولم يكن له كفوا أحد، بسم الله الرحمن الرحيمِ قُل أعوذ برب الفلق
Haka ma tsakanin Anfal da taubah Yanada fuskoki uku kamar sauran Riwayoyi
1- idan ya gama Anfal Zai tsaya sannan ya shiga Taubah ba tareda yayi basmalah ba
2- idan ya gama Anfal zai yi sakt السَّكْت ( wato ya dan tsaya kadan ba tare da yayi numfashi ba) sai ya shiga Tauba kuma bazaiyi basmalah ba
3- Ya hade tsakanin Anfal da tauba ba tareda yayi basmalah ba
والله أعلم
2- mimul-jam'i. مِيمُ الجَمْع
mimul-jam'i itace Mimun Dake nuni akan Jam'i wato adadin da yake daga uku zuwa sama
Al-imamul Bazzy yana karanta Wannan Mimul-jam'i din da sila (wato ayimata dwamma kuma a ja ta ja biyu) mislali
صراط الذين أنعمت عليهِمُ, غير المغضوب عليهِمُ, ولا الضآلّين
A duk inda mimul-jam'i tazo a cikin Qurani
3- Ha'ul-kinayah هَاءُ الكِنَايَة Ko kuma muce هاء الضمير
Ha'ul-kinayah Ha'un ce Da ke nuni akan wani abu daya namiji (المُذَكَّر) Wanda bayanan الغَائِب Kamar عليه da فيه da sauran su
Al-imamul Bazzy yana karanta Wannan Ha'ul-kinayah din da yin Silar ta ( wato jan ta ja biyu da yimata Kasra ِ a wurin da ake yimata kasra da yimata Dwamma ُ a wurin da ake yimata Dwamma) Misali
فِيهِ>هُدًى للمتقين
اجتَبَـٰـهُ, وَهَد ــٰـهُ, إلى صراط مستقيم
A duk inda tazo cikin Qurani mai Girma
4- Maddodi المُدُود
Al-imamul Bazzy yana Ja 2 biyu Ga maddul ja'iz
Haka kuma yana ja 4 hudu Ga Maddul wajib
5-Hukunce-hukuncen Hamzah
Wannan babin Kuma munada babi uku 3 da zamuyi bayanin Hamzah dake a cikin wadannan babukan
1- الهمزتين من كلمة
ة2- الهمزتين من كلمتين
3-الهمز المُفرد
1- الهمزتين من كلمة
Sune Hamza biyu أأ dake Zuwa tare a cikin kalma daya
Misali
ءأنذرتهم ءألد ءأمنتم
Da sauransu
Al-imamul Bazzy yana yin Tas'hiln Hamzah ta biyu idan aka samu Hamzah biyu sunzo a cikin kalma daya kamar haka
ءاْنذرتهم
ءاْلد
ءاْمنتم
2- الهمزتين من كلمتين
Sune a samu Hamza tazo A karshen kalma ta farko جآء sai kalmar dake biye da ita ta fara d a harafin Hamzah 👉أمة
(جَاءَ أُمة)
Misali
جَاءَ أُمة
نَشاء أصبناهم
من السماء أو ائتنا
Da sauransu
Al-imamul Bazzy yana yin Is'qadin الإسقاط (wato cire) Hamza ta farko a duk inda aka samu Hamzataini da sukazo kamar yadda nayi bayani a sama idan sukazo da fat'ha fat'ha (الهَمزَتان من كلمتين المَفتُوحتَينِ) kamar
جَآءَ أَجَلُها
شَآءَ أَنشَرَه
Da dai sauransu
To Bazzy yana cire hamza ta farko a duk ire-iren wadannan
Sai ya karanta haka
👇👇
جَا أَجَلُها
شَا أَنشَرَه
Kuma ja biyu kawai yakeyi na madda
Amma idan wasullan wadannan Hamzojin sun banbanta misali ta farko tanada dwamma ءُ ta biyu tanada fataha ءَ Misali
نَشَآءُ أَصَبنَــٰــهم
Ko kuma a samu ta farko tanada kasra ءِ ta biyu tanada fataha ءَ Misali
مِنَ السََّمَآءِ ءَاية
Da dai sauransu
To idan aka samu sun sa6a a wurin wasali To Bazzy yana Yin Tas'hilin Hamza ta biyu kamar haka
👇👇
نَشَآءُ اْصَبنَــٰــهم
مِنَ السََّمَآءِ °َاية
Da sauransu
3- الهَمز المُفرد
Itace Hamzah da take zuwa guda daya a cikin Kalma daya
Misali
يؤمن. جِئت هِئتَ شِئتَ يأت يؤتَونَ يأجوج ومأجوج
Da sauransu
Al-imamul Bazzy Yana Tare da Hafs a wannan babin yadda Hafs yake karantasu haka shima yake karantawa
Sai dai ya sa6awa Hafs A wannan kalmomin
يأجوج ومأجوج مُؤصَدَة
Bazzy yana yin Ibdalin wannan hamzar
ta dawo Harafin Madda
👇👇
ياجوج وماجوج مُوصَدَة
Amma idan ba a wadannan Kalmomin ba to suna tareda Hafs
Sai dai kuma a wadannan Kalmomin Bazzy yana saka harafin Hamzah a wurin da Hafs baya sakawa
وَمَنَاةَ الثالثة yana saka Hamza وَمَنَآءَةَ الثالثة
تلك إَذًا قسمة ضِيزى yana sa Hamza تلك إَذًا قسمة ضِئزى
والله أعلم
A nemi littafin da yayi magana akan wannan Riwayar Domin neman karin bayani
6- Hukunce-hukuncen tsayawa akan Ha'utta'anith wacce aka rubuta ta a harafin ت (budaddar ت)
Idan muna Bibiyar Qurani zamuga wasu wurare ana rubuta ت budadda a wurin da ya kamata ace an Rubuta ة rufafa Misali
قرت عين لي ولك
وَجَنَّتُ نَعيم
فطرتَ الله
إلا سُنَّتَ الأولين
لسنتِ الله
ومعصيت الرسول
بَقِيَّت الله
كَلِمَتُ رَبك
أولئك يَرجُونَ رَحمَتَ الله
To wannan Babin Shi zai yimuna bayanin Matsayin Bazzy akan yin Waqafi akan wannan ت
A duk wurin da aka ga irin wannan تTo mu sani Cewa Bazzyi yana yin waqafi tare da Daure Ha'un هْ ne Misali
قرت عين لي ولك. 👈 قُرَّهْ. ( idan zaa tsaya )
وَجَنَّتُ نَعيم. 👈 وَجَنَّهْ ( idan zaa tsaya )
فطرتَ الله. 👈 فطرهْ ( idan zaa tsaya )
إلا سُنَّتَ الأولين. . 👈 سُنَّهْ ( idan zaa tsaya )
ومعصيت الرسول 👈 معصيَهْ. ( idan zaa tsaya )
بَقِيَّت الله. 👈 بَقِيَّهْ. ( idan zaa tsaya )
كَلِمَتُ رَبك 👈 كَلِمَهْ ( idan zaa tsaya )
أولئك يَرجُونَ رَحمَتَ الله. 👈رَحمَهْ ( idan zaa tsaya )
Da dai sauransu
Sai dai a wadannan kalmomi da zan Kawo yana Tsayawa akan تْ ne ba akan هْ ba
👇👇
أفرأيتم اللَّتَ وَالعُزى 👈اللَّتْ( idan zaa tsaya )
مَرضاتِ الله. 👈مَرضاتْ( idan zaa tsaya )
ذَاتَ بَهْجَةٍ 👈ذَاتْ( idan zaa tsaya )
ولاتَ حِينَ مَنَاص. 👈ولاتْ( idan zaa tsaya )
Ya na daure تْ ne a wurin tsayawa akan wadannan kalmomin 4
والله أعلم
Haka kuma Al-imamul Bazzy yana tsayawa akan Harafin هْ daurarra a duk inda Kalmar يَــٰــأَبَتِ tazo
Idan zai tsaya a kan wannan kalmar yana Daure هْ ne a duk inda tazo a Qur'ani
Misali
يَــٰــأَبَتِ إني رَأيت أحد عشر كَوكَبًا
يَــٰــأَبَتِ. 👈. يَــٰــأَبَهْ. ( idan zaa tsaya)
Akwai Wasu Ta'at Da ake kira Ta'at Na Bazzy kusan 31 Da sukazo A cikin Qurani mai Girma
Kamar
- ولآ تَّيَمموا الخبيث
- ولآتَّجسسوا
- وَلآتَّنَابزوا
Da dai sauransu
A nemesu cikin فرش الحروف
7- matsayin Bazzy akan Sak'tah (السكت) da hafs keyi akan wadansu Kalmomi hudu a Alqurani mai Girma
Sak'tah itace Mutun yana Karatu sai ya dan tsaya kadan akan wani Harafi Ba tareda yayi numfashi ba sai ya wuce
Bazzy baya yin Sak'tah ko daya a Qur'ani
A wurare Hudu ma Da hafs yakeyin Sak'tar Bazzyi Bayayi Ga wuraren kamar Haka
1- ولم يجعَل له عِوَجا(١) قيما لينذر بأسا شديدا
2- من بَعَثَنَا من مرقَدِنا هذا ما وَعَدَ الرحمن
3- وقِيلَ مَن رَاق
4- كلا بل ران على قلوبهم
Baya yin Sak'tar wadannan wuraren
8- Izhari Da Idgami الإظهار والإدغام
Bazzy yana tare da Hafs A wannan Babin wuraren da hafs yake IZ'HARI to Bazzy shima Yanayi inda Hafs keyin idgami Bazzy ma idgami yakeyi
Hakama a wurin izhari ko idgamin wadannan Haruffan
👇👇👇
إذْ، قَد، تاء التأنيث، هَلْ، بَل.
Sai dai a wadannan kalmomin
- يَلهَثْ ذَلك مثل القوم
- اركَب مَعَنا
A wurin يَلهَثْ ذَلك Bazzy yana yin IZ'HARI ne sabanin Hafs da yake idgami
Haka kuma a wurin kamar اركَب مَعَنا Bazzy yanada Fuska biyu izhari da idgami
1- اركَبْ مَعَنا. (izhari)
2- اركَب مَّعَنا. (idgami)
والله أعلم
9-Ya'atul Idafah الياءات الإضافة
Ya'atul Idafah itace ya'un Da Mutun Zaiyi amfani da ita wurin Jingina Wani abu zuwa Gareshi
Wannan Ya'un Ta kasu Kashi-kshi
Kamar haka:-
Akwai wace harafin Hamzah أإ mai fataha ko kasra ko Dwamma yake zuwa a gabanta
إِنِّــيٰٓ أَعلَم
إِنِّــيٰٓ أُرِيد
دُعَآءِىٰٓ إلا فرارا
Akwai kuma wacce lamu-Al ( لام ال. التعريف ) ke zuwa a gabanta kamar haka
- لا ينال عَهدِى الظلمين
- عبادى الصلحون
- إنما حرم ربـى الفواحش
Da dai sauransu
Akwai kuma wacce Hamzatu-waslin (الهَمزَةُ الوَصل) ke zuwa Gabanta kamar
- إنـى اصطفَيتُك على الناس
- إن قومى اتخذوا
- يأتـى من بعدى اسمه أحمد
Akwai kuma wacce Haruffa ke zuwa a gabanta ba Hamzah أ ko Lamu-Al ba Misali
- أين شركآءِى قالوا
- من وراءِى وكانت امرأتي عاقرا
- لكم دينكم ولى دين
- إن أرضِى واسعة
Da sauransu
A duk Wadannan Sassa Na Ya'atul Idafah akwai wuraren da Bazzy keyimata Fat'ha Akwai kuma Wuraren da yakeyin Skun (Dauri) Wannan Rubutun Bazai Isa mu Bayyana komai Da komai Ba
Domin neman Bayani A nemi Littafan Da sukayi Bayani Akan Wannan Riwayar Domin neman Karin Bayani
GA WANI MUHIMMIN RUBUTU DA YA SHAFI YA'ATUL IDAFA
👇👇👇👇
Akwai Ya'atul Idafah 212 Dari biyu da sha biyu A cikin Qurani mai Girma
= Wadanda harafin Hamzah أَ mai fat'ha yazo a gabanta 99 ne
= Wadanda harafin Hamzah إِ mai kasra 52 ne
= Wadanda harafin Hamzah أُ mai Dwamma 10 ne
= Wadanda Lam-Al لام التعريف tazo a gabanta 14 ne
= Wadanda Hamzatul-wasli tazo gabansu 7 ne
= Wadanda wasu haruffa na daban sukazo gabansu 30 ne
Wannan shine Takaitaccen jawabi gameda Wannan babin
10- Ya'atuzzawa'id الياءات الزوائد
Ita kuma wannan Itama ya'un ce da Asalinta baarubuce take ba a cikin Qur'ani,
Qurra'u sunyi sabani a wurin karanta ta, sun kasu kashi uku
1- Akwai masu karanta ta A kowane irin yanayi ( lokacin tsayawa (WAQAFI) a kanta, ko lokacin wucewa da karatu a kanta) kamar Ibn Kathir
2- Akwai Wadanda basu karantawa da ita A kowane irin yanayi Na karatu ( lokacin tsayawa (WAQAFI) a kanta, ko lokacin wucewa da karatu a kanta) Kamar Hafsu
3- Akwai wadanda ke Tabbatar da ita a lokacin wucewa da Karatu, suna cireta wurin WAQAFI Kamar warsh
Bazzy yana Tabbatar da wannan Ya'un din a hali biyu na Karatunshi ( lokacin Wucewa da karatu ko lokacin tsayawa)
Ya'atuz-zawa'id Tana zuwa ne a cikin wadannan kalmomin da ire-iren su
👇👇👇👇
إلى الداع
إذا دَعَان
واليل إذا يَسر
الجَوَار
الجَواب
يناد المناد
Da sauransu
Sai dai Yana tabbatar da Ya'atu zawa'id da sukazo a cikin wadannan kalmomin A lokacin da zai tsayawa da karatu kawai
Ga kalmomin kamar haka
👇👇
مِن وَالٍ. 👈 وَالِ>
فما له من هادٍ. 👈هادِ>
مِن واقٍ. 👈 واقِ>
ومَا عندَ الله بَاقٍ. 👈 بَاقِ>
Domin neman Karin Bayani a Bincika cikin littafan da sukayi magana akan Wannan Riwayar.
Anan zamu tsaya sai a taremu a rubutu na gaba inda zaa jimu da wata Riwayar ta daban insha Allah
JAN HANKALI
👇👇👇👇
Duk wanda Zaiyi sharing ko Kwafi Na wannan Rubutun nawa To ya yi Sharing Dinshi A yadda Na Rubutashi Kar ya kara komai kuma Kar ya canja komai abar shi yadda nayishi
Duk wanda yakeda Taaliki ko gyara Ko shawara ko Mulahaza akan Wannan Rubutun to ya atuntubeni nizan gyara Da kaina Amma Kar A canja Min rubutu.
Ga lambar da zaa tuntubeni da ita +2348034468543
✍️WANDA YA RUBUTA
Habibu Muhammad Shugaba
+2348034468543
Thursday
05-12-1442
15-07-2021

No comments:

Post a Comment