رِوايةُ هِشَام
عَن ابن عَامِر الشََّامِي
TARIHIN QARI'AI GOMA 10 DA RIWAYOYINSU 20
تاريخ القراء العشرة ورواتهم
RUBUTU NA: ![1️⃣](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/t7a/1/16/31_20e3.png)
![2️⃣](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/t99/1/16/32_20e3.png)
![1️⃣](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/t7a/1/16/31_20e3.png)
![2️⃣](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/t99/1/16/32_20e3.png)
Rubutawar
![✍](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/te2/1/16/270d.png)
ABUBUWAN DA KE KARKASHIN WANNAN RUBUTUN
![👇](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/t4f/1/16/1f447.png)
![👇](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/t4f/1/16/1f447.png)
![👇](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/t4f/1/16/1f447.png)
![👇](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/t4f/1/16/1f447.png)
![👇](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/t4f/1/16/1f447.png)
1- WANENE AL-IMAM HISHAM
2- MALAMAN HISHAM
3- MAGANAR MALAMAI GAMEDA HISHAM
4- DALIBAN HISHAM
5- BAYANI AKAN USUL NA RIWAYAR HISHAM
6- RUFEWA
1- WANENE HISHAM
Sunanshi:- Hisham bn Ammar bn Nusair bn Maisarah Assulami, Addimashqi.
ALKUNYARSHI:- Abul-walid
An haifeshi a shekara ta 153 bayan Hijrah
Hisham Shugaba ne kuma jagora a fannin Karatun Qurani a garin sham, Haka kuma limamin Jumu'ah ne, masanin Hadisi ne da Fiqihu, haka kuma Babban Malami ne mai Fatawah.
Hisham Daya ne daga Cikin Rayiyai na Qur'ani mai Girma Ana Jingina Riwayar shi ne Ga Al-imam ibn Amir Qari'i na hudu Daga cikin QARI'AI goma
Hisham shi ake Gabatarwa a wurin jeranta Riwayoyi akan Ibn zakwan
Hisham ya kasance daga cikin Bayin Allah Da ake Karbar Adu'ar su
Ibn Al-jazari ya kawo a cikin littafin shi ( Gayatunnihayah 2/356) Cewa Abu Abdillahi Al-humaidi yace " Wasu daga cikin Masana Hadisi na garin Bagdad Cewa Hisham ibn Ammar yace : Na Roki Allah Abubuwa bakwai 7 Allah ya Bani 6 daga cikin su daya ce kawai bansan Yadda Allah Zaiyi dani a gareta ba,
Gasu kamar haka
![👇](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/t4f/1/16/1f447.png)
![👇](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/t4f/1/16/1f447.png)
![👇](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/t4f/1/16/1f447.png)
![👇](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/t4f/1/16/1f447.png)
1-Hisham yace : Na Roki Allah ya Gafartamin Da ni Da iyayena, wannan Shine Abunda Bansan Makomar wannan Rokon nawa ba
2- yace: Na Roki Allah ya Yimin Arzikin yin Aikin Hajji, Allah ya Bani Dama Nayi Aikin Hajji
3- yace : Na Roki Allah Ya tsawaita rayuwata inkai Shekara dari 100 Allah ya bani wannan
4- Yace : Na Roki Allah ya sanyani in Zamo mai Gasgatawa Ga Annabi صلى الله عليه وسلم ya kuma bani wannan
5- yace :- Na Roki Allah ya sanya Dalibai Su Rika Zuwa wurina wurin neman ilimi, Kuma Allah ya bani wannan
6- yace:- Na Roki Allah yasa in zama Limami mai Khuduba A Garin Dimashq, kuma na zama liman
7- yace:- Na Roki Allah ya Azurtani da Dinari dubu ألف دينار na halal Kuma Allah ya bani
Hisham ya rasu a karshen Watan Muharram a shekara ta 245 bayan Hijrah yanada Shekaru 92 a duniya
رحمه الله تعالى رحمة واسعة
2-MALAMAN AL-IMAM HISHAM
Ga wasu daga Cikin malumanshi
1- Ayyub ibn Tamim
2- Irak ibn khalid
3- Suwaid ibn Abdul-aziz
4- Al-walid ibn muslim
5- Sadaqatu ibn khalid
6- Mudrik ibn Abi Sa'ad
7- umar ibn Abdulwahid
Da sauransu
3- MAGANAR MALAMAI GAMEDA HISHAM
Malamai da dama sunyi Maganganu da ke nuni akan Girma da matsayin Al-imam Hisham ga kadan daga cikinsu
YAHYA ibn Ma'in Yace:- Hisham Sikah ne ثِقَةٌ wato Adili ne ( wannan yaren Maluma Jarhi da Ta'adili nea fannin Ilimin hadisi)
Al-imamul Ijliyy yace :- Hisham Sikah ne ثِقَةٌ wato Adili ne
Al-imam Daraqduni yace:- Mai yawan Gaskiya ne صَدُوقٌ (wannan Yaren Malaman Hadisi ne)
Abu Aliy Al-asbahani yace:- A lokacin da Ayyub ibn Tamin ya rasu Jagoranci da Shugabanci a fannin Karatun Qur'ani ya dawo zuwaga mutum biyu sune IBN ZAKWAN DA KUMA HISHAM
4- DALIBAN AL-IMAM HISHAM
Ga wasu daga Cikin Daliban Hisham
1- Abu Ubaid Al-Qasim ibn Sallam
2- Ahmad ibn yazid Al-hulwani
3- Ahmad ibn Anas
4- Ibrahim ibn Duhaim
5- Ishaq ibn Abi hassan
6- Isma'il ibn Al-huwairis
7- Ibrahim ibn Abbad
8- Musa ibn Jamhur
9- muhammad ibn Sharh
10- Ahmad ibn muhammad ibn bakr Al-bakrawi
Da wasun wadannan
Kamar yadda ibn. Al-jazari ya kawosu a cikin littafin (غَايَةُ النِّهَايَة)
kafin mu shiga bayani akan Usul na Riwayar Hisham![👇](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/t4f/1/16/1f447.png)
![👇](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/t4f/1/16/1f447.png)
GA WANI BAYANI MAI MUHIMMANCI DA YA KAMATA MU SANI
![👇](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/t4f/1/16/1f447.png)
![👇](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/t4f/1/16/1f447.png)
![👇](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/t4f/1/16/1f447.png)
![👇](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/t4f/1/16/1f447.png)
![👇](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/t4f/1/16/1f447.png)
![👇](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/t4f/1/16/1f447.png)
![👇](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/t4f/1/16/1f447.png)
![👇](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/t4f/1/16/1f447.png)
![👇](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/t4f/1/16/1f447.png)
![👇](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/t4f/1/16/1f447.png)
Ka Sani Yakai dan uwa mai Karatu
Hisham da Ibn Zakwan Basuyi Karatu Kaitsaye (Baki da baki) Ga ibn Amir ba.
![👉](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/t51/1/16/1f449.png)
Su Daliban-Daliban-Daliban ibn Amir ne Wato Tsakaninsu da ibn Amir Akwai wasidar Mutun biyu
Idan ma Muka Dubi tarihin haihuwarsu zamuga cewa Koda ibn Amir ya rasu Ba'a haifesu ba
Domin kuwa ibn Amir ya Rasu ne a shekara ta 118 Bayan Hijrah
Hisham kuma an haifeshi ne a shekara ta 153 baywn Hijrah
Ibn Zakwan kuma an haifeshi a shekara ta 173 bayan Hijrah
Ga yadda abun yake
![👇](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/t4f/1/16/1f447.png)
![👇](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/t4f/1/16/1f447.png)
![👇](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/t4f/1/16/1f447.png)
YAHAYA AL-ZIMARI:- Shine ya yi karatu ga ibn Amir
Sai wadannan daliban sukayi karatu gareshi (Yahaya)
1- Ayyub ibn Tamim
2- Irak ibn khalid
3- Sadaqatu ibn khalid
4- Suwaid ibn Abdul-aziz
Shi kuma Hisham yayi karatu ga
1- Ayyub ibn Tamim
2- Irak ibn khalid
3- Sadaqatu ibn khalid
4- Suwaid ibn Abdul-aziz
IBN ZAKWAN kuma Ya yi Karatu ga
1- Ayyub ibn Tamim
2- Irak ibn khalid
Wannan Shine Ma'nar Fadar Al-imam As-shadibiyy
هِـشَـامٌ وَعَـبـدُ اللهِ وَهْوَ انتِسَابُه
لِــذَكْـــوَانَ بِـالإِسْــنَــادِ عَـنْـه تَــنَــقَّــلَا
Fassara:-
Rawiyan Ibn Amir sune Hisham Da kuma Abdullahi (wannan Abdullahin) Shine Ake nasabtawa zuwa ga Zakwan (Zakwan daya ne daga cikin Kakannin ibn Zakwan), Hisham da ibn Zakwan sunyi Riwayar Qira'ar ibn Amir ne Da isnadi.
Wadanda ake Jinginawa riwayoyi (Masu Riwaya) Sun kasu gida uku
1- akwai wadanda sukayi karatu baki da baki ga QARI'AI da ake jinginawa riwayarsu zuwa garesu kamar
- Qalun da warsh sunyi karatu baki da baki ga Nafi'u
2- Akwai wadanda A tsakaninsu da QARI'AN akwai wasidar Mutun Daya kamar
- Dury da susi Sunyi karatu ga Yahyal-Yazidiyyi shi kuma yahya yayi karatu ga Abu Amr Al-basry
-Kamar Khalaf da khallad Sunyi karatu ga Sulaim shi kuma sulaim Yayi Karatu Ga Hamzah
3- Akwai wadanda akwai fiye da mutun daya a tsakaninsu da QARI'IN DA sukayi riwaya a gareshi kamar
- Hisham da ibn Zakwan basuyi karatu kai tsaye ga ibn Amir ba Akwai fiye da mutun daya a tsakanin su
Abun da yasa hakan ta faru shine
A lokacin da wannan ilimin na riwayoyi yayi yawa ya fadada riwayoyin sunyi yawa Kasancewar kowane Qari'i yanada dalibai masu dinbin yawa kuma kowane daga cikin su yana jingina riwayar shi zuwaga wannan Qari'in
Sai akayi niyyar Takaita Riwayoyin Akace kowane QARI'I zaa fitar da mutun biyu daga cikin Rawiyanshi (Dalibanshi) Wadanda sukafi kwarewa da kuma tsoron Allah Da tsantseni domin a jingina riwayar shi zuwa garesu
Sai a bincika Idan an samu wanda ya cika sharudan daga cikin Daliban QARI'IN, haka kuwa akayi Zabin Ya fada Ga Hisham da ibn Zakwan sai aka aka cigaba da jingina Qira'ar ibn Amir zuwa garesu, Riwayar su kuma ake jinginata kai tsaye zuwa gareshi (Ibn Amir) Sabanin asalin Malamansu
Wannan shine Ma'anar Fadar Shadibiyy
تَخَيرَهم نُقَّادُهُم كلَّ بَارِعٍ
وَلَيسَ عَلى قُرءَانِه مُتَأَكِّلا
Adadin Ayoyin Qur'ani na wannan QIRA'AR 6226
عَدُّ الشََّامِي
Wato Qirgar Ayoyi bisa Qirgar Sham Shine Akayi Aiki dashi wurin kayyade adadin Ayoyin Qur'anin Qira'ar ibn Amir
والله أعلم
Al-imam As-shadibiyy ya sanya Ramzin كَـــلَِـــمْ ya zamo alamar da za'a Gane ibn Amir da ita da kuma Riwayoyin shi biyu Hisham da ibn Zakwan
Ko ince Daya daga cikin Alamomin da zaa ganesu da ita
Ga abunda yake nufi
كَـــلَِـــمْ
1- idan mukaga Ramzin ك a cikin Shadibiyya To Ramzi ne dake Nuni Ga Qira'ar Ibn Amir
2- idan mukaga Ramzin ل a cikin Shadibiyya To Ramzi ne dake Nuni Ga Riwayar Hisham
3- haka kuma idan mukaga Ramzin م a cikin Shadibiyya To Ramzi ne dake Nuni Ga Riwayar ibn Zakwan
Duk da cewa Wani lokacin yana ambatar su da sunayensu ko lakubansu gwargwadon yadda Lalurar waka ta bayar
والله أعلم
5- BAYANI AKAN USUL NA RIWAYAR AL-IMAM HISHAM
Malaman Qira'at Suna Kasa Kowace Riwaya zuwa Sashe Biyu Gasu kamar
1- Sashen Usul
2- Sashen Farsh فَرْش
Abunda ake cewa Usul shine Abubuwan da Riwaya ke Ginuwa akansu musamman Abunda da kaji anyishi kaitsaye zaka iya Fahimtar Riwayar da ake karantawa Misali
![👇](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/t4f/1/16/1f447.png)
= Idgamulkabir Ga Riwayar Susi
= Kamar Sak'tah السَّكْتَة ga riwayar khalaf
= Taglizin Lamun da Tarqiqin Ra'un Ga riwayar Warshu
= Silar HA'UL-KINAYAH Ga Qira'ar ibn kathir
Da dai sauransu
Farsh Kuma Shine Bayanin Kalmomin Qur'ani wadanda Qira'o'i sukayi Sabani a wurin karantasu
A cikin Farsh ne Zaayi bayani akan Kalma Ace Wadannan suna karanta ta kamar haka, wadannan kuma ga yadda suke karantawa
A wannan Babin kuma Zamuyi bayani ne akan wadannan Abubuwan da zamu jero insha Allah
![👇](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/t4f/1/16/1f447.png)
![👇](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/t4f/1/16/1f447.png)
1- BISIMILLAH DAKE ZUWA TSAKANIN SURORI BIYU ما جاء بين السورتين
2- HA'UL KINAYAH ko (هَاء الضمير)
3- MADDODI المُدُود
4- HUKUNCE-HUKUNCEN HAMZA
5- NAQLU DA SAKT النقل والسكت
6- IZ'HARI DA IDGAMI الإظهار والإدغام
7- FAT'HA DA IMALAH الفَتحُ والإمالة
8- YA'ATUL IDAFAH الياءات الإضافة
9- YA'ATUL-ZAWA'ID الياءات الزوائد
Akwai Babukan da zamu Tsallake basai munyi bayani akansu ba saboda Hisham da Hafs sunyi muwafaqa a cikinsu ko kuma Hisham bayada banbanci sosai da hafs a cikinsu sai a nemi littafan Qira'at domin neman Qarin bayani
1- BISIMILLAH DAKE ZUWA TSAKANIN SURORI BIYU ما جاء بين السورتين
Kamar yadda muka sani cewa a tsakanin Surorin Qur'ani Akwai Bisimillah dake zuwa idan mutun ya gama wata surah zai shiga wata
Tsakanin Anfal da Taubah ne kawai babu basmalah
Hisham yanada Fuska 5 a wurin bisimillah dake Zuwa Tsakanin surori
1- قطع الجميع
Shine Ka kare sura Ka tsaya Kayi bisimillah ka tsaya sai ka shiga wata sura
Misali
ولم يكن له كفوا أحد، بسم الله الرحمن الرحيم، قل أعوذ برب الفلق
2- وَصلُ الجميع
Shine ka hade karshen sura da bisimillah da kuma farkon surar da take gaba Ba tareda ka tsaya ba
Misali
ولم يكن له كفوا أحدٌ بِسم الله الرحمن الرحيمِ قُل أعوذ برب الفلق
3- قطع الأول ووصل الثاني بالثالث
Shine Ka kai karshen sura ka tsaya Sai kuma ka hade Bisimillah da farkon surar da take gaba
Misali
ولم يكن له كفوا أحد، بسم الله الرحمن الرحيمِ قُل أعوذ برب الفلق
4- الوصل بلا بسملة
Shine ka sadar da karshen surar da ka gama da surar da take a gaban ta ba tareda kayi bisimillah ba
Misali
ولم يكن له كفوا أحدٌ قُل أعوذ برب الفلق
Sai kuwa Akwai wasu surori guda hudu da suka sabawa Wannan tsarin ana kiransu da suna أربَعُ الزُّهُهر
Sune :-
1- سورة القيامة
2- سورة المطففين
3- سورة البلد
4- سورة الهمزة
5- السكت بلا بسملة
Shine idan ka gama Sura sai ka dan tsaya kadan ba tareda kayi nunfashi ba sai ka shiga surar da take gaba ba tareda kayi bisimillah ba
Misali
ولم يكن له كفوا أحدْ (س) قُل أعوذ برب الفلق
Sai kuwa Akwai wasu surori guda hudu da suka sabawa Wannan tsarin ana kiransu da suna أربَعُ الزُّهُهر
Sune :-
1- سورة القيامة
2- سورة المطففين
3- سورة البلد
4- سورة الهمزة
Haka kuma A tsakanin Anfal da Taubah Yanada Fuska Uku kamar sauran Riwayoyi a duk wadannan Fuskokin yana yinsu ba tareda Bisimillah ba
1- الوصل بلا بسملة
2- السكت بلا بسملة
3- القَطع بلا بسملة
Haka kuma Wajibi ne a wurin karatun kowace Riwaya Ayi bisimillah idan An gama سورة الناس kuma anaso a sake dauko karatu daga Fatiha
A nemi littafan Riwayoyi domin neman Karin Bayani
2- HA'UL KINAYAH ko (هَاء الضمير)
Ha'ul-kinayah Ha'un ce Da ke nuni akan wani abu Guda daya namiji (المُذَكَّر) Wanda bayanan الغَائِب Kamar عليه da فيه da sauran su
Akwai sabanin riwayoyi a wurare da dama a wurin wannan Ha'un din kamar haka
1- wasu suna Daure ta a wasu wuraren kamar. يُؤَدِّهْ إِلَيك
2- wasu kuma Wasu suna Yimata Wasali ba tare da anja mata Madda Ba (Sila) kamar. يُؤَدِّهِ إِلَيك
3- wasu kuma Suna Yimata Wasali tareda Silar ta wato jan Madda Gareta kamar يُؤَدِّهِ> إِلَيك
A nemi littafan Riwayoyi domin sanin matsayin kowace riwaya a wannan Babin
Hisham yanada Fuska biyu a wurin Karanta wadannan Ha'un din
1- Yana karantawa da silar ha'un هـ (ja biyu na madda)
2- Yin Kasra Ga Ha'un ba tareda Sila Ba
Ga kalmomin kamar haka
يُؤَدِّهِ إِلَيك ko kuma يُؤَدِّهِ> إِلَيك
نُؤْتِهِ منها ko kuma نُؤْتِهِ>منها
نُوَلِّهِ ما تولى. Ko kuma نُوَلِّهِ> ما تولى.
نُصْلِهِ جهنم ko kuma نُصْلِهِ> جهنم.
وَيَتَّقِهِ فأولئك هم الفائزون ko kum وَيَتَّقِهِ> فأولئك هم الفائزون
فَأَلْقِهِ إلَيهم. Ko kum. فَأَلْقِهِ> إلَيهم
وَمَن يَأْتِهِ مُؤمِنًا. Ko kum وَمَن يَأْتِهِ> مُؤمِنًا
Yanada Fuska biyu a wannan kalmar
يَرْضَهْ لكم. Ko kuma يَرْضَهُ لكم ba tareda Sila Ba
Haka ma yana kara Harafin Hamzah ء Tareda yin Dwammar Ha'un هُ tareda yin sila gareta kamar yadda ibn Kathir ke karantawa
![👇](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/t4f/1/16/1f447.png)
![👇](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/t4f/1/16/1f447.png)
![👇](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/t4f/1/16/1f447.png)
![👇](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/t4f/1/16/1f447.png)
![👇](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/t4f/1/16/1f447.png)
أَرْجِئْهُ, وَأَخَاهُ
Yana Cire madda A wurin
فيهِ مُهَانًا
Sabanin yadda hafs da ibn kathir ke karantawa
Yana mayar da Dwammar Ha'un Ta dawo Kas'ra a wurin wadannan kalmomin
وَمَــــا أَنسَـــٰـــنِيهِ إلا الشيطـن
عَلَيهِ اللهَ
Sabanin yadda Hafs ke karantawa
3- MADDODI المُدُود
Maddah Itace Jan Sauti Saboda zuwan Daya daga Cikin Haruffan Madda Guda Uku sune. ا da و da ي
Alif Daurarra Idan Harafin da ke gabaninta kamar قَالَ
Wawun Daurarra idan Harafin da ke Gabaninta yanada Dwwmma ُ kamar نُوح
Ya'un Daurarra idan Harafin da ke Gabaninta yazo da Kas'ra ِ kamar قِيلَ
Hisham yana yin Ja 4 ne kawai A wurin maddul-munfasil da kuma Muttasil
4- HUKUNCE-HUKUNCEN HAMZA
Hamzah ء dayace Daga Cikin haruffan Hija'iyyah أب ت ث ج ح خ د zuwa karshe.
Riwayoyi sunyi sabani a wurin karanta ta a cikin wasu kalmomi Saboda yadda takeda Wahalar fada ga wani sashe na Larabawa
Wasu sunayin TAS'HILI a wurin wasu kalmomi
Wasu kuma sukanyi TAH'QIQI
Wasu kuma Ibdali ko Hazafi sukeyi a wurin wasu kalmomin
Wannan babin Kuma munada babi Biyar da zamuyi bayanin Hamzah dake a cikin wadannan babukan
1- الهمزتين من كلمة
2- الإِستِفهَامُ المُكَرَّر
3- الهمزتين من كلمتين
4-الهمز المُفرد
5- الوَقفُ على الهمزة
1- الهمزتين من كلمة
Sune Hamza biyu أأ dake Zuwa tare a cikin kalma daya
Misali
ءأنذرتهم ءألد ءأمنتم
Da sauransu
Hisham yana da Fuska biyu a wurin karatun Kalmar da tazo da Hamzah biyu a farkon ta
1- TAS'HILI da kuma idkhali
2- TAH'QIQI da kuma idkhali
Tas'hili shine Sauqaqen Hamza wato a Karanta ta kamar و ko ي ko ا
TAH'QIQI kuma Shine A karanta ta yadda take ba tareda kowane irin sauyi a gareta ba
Abunda Ake cewa Id'khali shine Ayi madda Tsakanin Hamza guda biyu idan aka samu Hamzah biyu sunzo a cikin kalma daya kamar haka
ءَ ٰاْنذرتهم
ءَ ٰاْ سلَمْتم
ءَ ٰاْشْفَقْتم
ءَ ٰأنذرتهم
ءَ ٰأسلَمْتم
ءَ ٰأشْفَقْتم
Saidai akwai wasu kalmomi da yakeda sabani a wurin Karantasu
Wannan rubutun bazai isa mu kawosu gaba daya ba amma zaa iya neman littafan da sukayi magan akan wannan Riwayar
Haka kuma yana Kara harafin Hamza A wadannan Kalmomin
![👇](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/t4f/1/16/1f447.png)
أَئنَّ لَنَا لأَجرا Cikin Suratul A'arof
أءنَّكم لتأتون الرجال A'arof kissar Annabi Lud
ءَأ ٰمَنتُم لَه قبل أن
ءَأ ٰمَنتُم به قبل أن
أَأَذْهَبتُم طيباتكم
أَ'اْن كَانَ ذَا مَالِِ
Sai dai ita Wannan Kalmar ta أَ'اْن كَانَ yana yin Tashilin Hamza ta biyu ne Tareda yin Idkhali a tsakaninsu
Yana karanta wannan kalmar da Hamzah daya
أَعْجَـمِـــيٌّ وَعَرَبي
Haka kuma yana yin Tas'hili ba tareda Idkhali ba a kalmar
ءاْ ٰلِهَتُنَا خير أم هو
2- الإِستِفهَامُ المُكَرَّر
Akwai wasu kalmomi da sukazo a cikin Ayoyin Qur'ani ana Kiransu الإِستِفهَامُ المُكَرَّر wato tambayar da ta maimai tu
Misalinsu
أَءِذَا كُنا تُرَابًا أءِنا لفي خلق جديد
أَءِذَا كُنا تُرَابًا وَءَابَآؤنا أءِنا لَمُخرَجون
Da sauransu
Idan muka duba zamuga akwai sigar tambaya biyu a cikin wadannan Ayoyin to wannan ne ake cewa الإِستِفهَامُ المُكَرَّر
Ana samun irin wannan الإِستِفهَامُ المُكَرَّر din a wadannan Surorin
سورة الرعد
سورة الإسراء
سورة النمل
سورة العنكبوت
سورة الصافات
سورة الواقعة
سورة النازعات
A duk inda sukazo Hisham yana karantasu da Sigar Bada labari a Hamzozi biyu na farko (wato yana cire Hamzah daya) sai yace إِذَا ga ta farko بِالإِخْبَار, ya karanta ta biyu da sigar Tambaya بالإِستِفهَام, kamar أَءِنَّا
Misali
إِذَا كُنا تُرَابًا أءِنا لفي خلق جديد
Sai dai a wuri uku ga yadda yake karantawa
سورة النَّمل
Yana karantawa da sigar tambaya a farko ya karanta ta biyu da sigar Bada labari tareda Kara Harafin ن
![👇](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/t4f/1/16/1f447.png)
![👇](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/t4f/1/16/1f447.png)
![👇](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/t4f/1/16/1f447.png)
أَءِذَا كُنا تُرَابًا وَءَابَآؤنا إِنَّنَا لَمُخرَجون
سورة الواقعة
Yana karantawa da sigar Tambaya a dukkanin kalmomin biyu kamar yadda hafs ke karantawa
![👇](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/t4f/1/16/1f447.png)
![👇](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/t4f/1/16/1f447.png)
وكانوا يقولون أَئذَا متنا وكنا تُرَابًا وعظــٰما أءنا لَمَبعوثونَ
سورة النازعات
Yana karantawa da sigar Tambaya a farko ya karanta na biyu da sigar Dada labari
![👇](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/t4f/1/16/1f447.png)
يقولون أءِنا لَمَردودون في الحَافرة() إِذَا كُنا عظــٰما نخرة
3- الهمزتين من كلمتين
Sune a samu Hamza tazo A karshen kalma ta farko جآء sai kalmar dake biye da ita ta fara d a harafin Hamzah
أمة
![👉](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/t51/1/16/1f449.png)
(جَاءَ أُمة)
Misali
جَاءَ أُمة
نَشاء أصبناهم
من السماء أو ائتنا
Da sauransu
Hisham Bai sabawa Hafs ba a wannan Babin (yana yin TAHQIQI ne
4- الهَمز المُفرد
Itace Hamzah da take zuwa guda daya a cikin Kalma daya
Misali
يؤمن جِئت هِئتَ. شِئتَ يأت يؤتَونَ يأجوج ومأجوج
Da sauransu
Mafi yawan wadannan Kalmomin da Hamzah daya ke zuwa a cikinsu Hisham bai sabawa Hafs a wurin karantasu ba
Sai dai akwai wasu kalmomi da Hafs ke karantasu da Hamzah shi kuma Hisham yana Cire Hamzar kamar
يُضَـــٰـــهُونَ قَول الذين كفروا
مُوصَدَةٌ
يَاجُوج وَمَــــاجُوج
Da sauransu
2- Akwai wurin da hafs Ke Cire Hamza Shi kuma Hisham ya Saka Hamzar kamar
وءاخَرُون مُرْجَئُونَ لِأمر الله
تُرْجِئُ مَن تَشَآء منهن
Idan muka Duba Dakyau zamuga Karara Sun Saba A wadannan Kalmomin da muka kawo
والله أعلم
5- الوَقفُ على الهمزة
Wannan Kuma Babi Ne da Hisham Da Hamzah Suka Sabawa sauran Riwayoyi a cikin
Sabanin Kuwa Shine Idan aka Samu Kalmar Qur'ani Ta kare da Harafin Hamzah ء kamar
السماء الماء يشاء السَُفَهَاء
Da sauransu
Ko kuma A samu kalma a tsakiyarta akwai Harafin Hamzah ء kamar
أؤنبئكم أئنكم شركاؤكم
Da sauransu
Hisham ya sabawa sauran riwayoyi ne a kalmar da ke Karewa da harafin Hamzah kamar
السماء الماء يشاء السَُفَهَاء
Yanada Fuskoki da dama a wadannan Kalmomin da ire-irensu
Bari mu bada misali daya Kalmar السَُفَهَاء
Tanada Fuskoki 5 a lokacin da mai karatu da Riwayar Hisham Zaiyi Waqafi a kanta
![👇](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/t4f/1/16/1f447.png)
![👇](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/t4f/1/16/1f447.png)
![👇](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/t4f/1/16/1f447.png)
1- إبدَالُ الهمزةِ ألفًا مع القصر
Wato idan mutun ya tsaya A kanta ya mayar da Hamzah harafin madda yayi ja biyu kamar
السَُفَهَا
2- إبدَالُ الهمزةِ ألفًا مع التَّوَسط
Wato idan mutun ya tsaya A kanta ya mayar da Hamzah harafin madda yayi ja hudu kamar
السَُفَهَآ
3-إبدَالُ الهمزةِ ألفًا مع المَدّ
Wato idan mutun ya tsaya A kanta ya mayar da Hamzah harafin madda yayi ja shida kamar
السَُفَهَآ
4- تَسْهِيلُ الهَمزة مع المَدِّ والرَّومِ
Tsayawa akanta Tareda yin Tashilin Hamzar da yimata Raum Tareda jan madda 6
5-تَسْهِيلُ الهَمزة مع القَصر والرَّومِ
Tsayawa akanta Tareda yin Tashilin Hamzar da yimata Raum Tareda jan madda 2
Da sauransu
A nemi littafan Riwayoyi domin neman karin bayani
5- NAQLU DA SAKT النقل والسكت
Abunda ake cewa NAQLU shine Cirato wani abu Daga wani wuri Zuwa wani wuri, Anfi amfani da wannan isdilahin Ga Hamza a wurin maluman Qira'o'i kamar ace
نقل حركة الهمزة إلى الساكن قبلها
Wato cirato Wasalin Hamza a dorashi kan Harafin da ke Gabaninshi kamar ace
قَدَ افْلَحَ
مَنُ اوتِـيَ
Da sauransu
Warshu shine mai wannan Babin
SAKTAH:- Tana nufin Tsayawa dan lokaci kadan a yayin Karatu ba tareda Shedawa (nufashi) ba sannan a wuce kamar كَلَّا بَل رَان sananne a Riwayar Hafs
To Hisham bayada Saktah Ko daya a cikin Qurani don Haka duk wuraren nan Da hafs keyinta wuri 4 shi bayayi, Ga wuraren kamar Haka
1- ولم يجعَل له عِوَجا(١) قيما لينذر بأسا شديدا
2- من بَعَثَنَا من مرقَدِنا هذا ما وَعَدَ الرحمن
3- وقِيلَ مَن رَاق
4- كلا بل ران على قلوبهم
Baya yin Sak'tar wadannan wuraren
6- IZ'HARI DA IDGAMI الإظهار والإدغام
IZ'HARI shine Fitar da Harafi daga mafitarshi ba tareda anyimishi Gunnah ba
IDGAMI Shine Shigar da Wani Abu a cikin wani abu
Akwai wasu Haruffa da ke Shiga cikin wasu kuma Riwayoyi sunyi sabani a garesu wato wasu suna Izhari wasu kuma Suna Idgami
Akwai
(إِذْ) ت ز ص د س ج harafi 6
(قَدْ) harafi 8 س ذ ض ظ ز ج ص ش
(تَاء التأنيث) harafi 6 س ث ص ز ظ ج
(هَل) ( بَل) harafi 8 ت ث ظ ز س ن ط ض
Akwai haruffan Da ke shiga cikin wadannan Haruffan musali
إِذْ
Haruffa 6 ke shiga cikin إِذْ sune
ت ز ص د س ج
Kamar
إِذ تَّمشِي أُختُكَ
إِذ سَّمِعْتُمُوهُ
Da sauransu
Hisham yana yin Idgamin إذ a cikin duk wadannan harufan da ke shiga a cikinta guda 6
Haka kuma yana yin Idgamin قد a cikin Duk Haruffan da ke shiga a cikinta guda 8
Yana yin Idgamin تَاء التأنيث a cikin Harafin ث da ط
kamar
كذَّبَت ثَّمود
كَانَت ظَّالمة
yana yin IZ'HARI a ga sauran da ke shiga a cikin تَاء التأنيث
Hisham yana Yin idgamin هَل da بَل a cikin Haruffan( ت ث ز س ط ظ)
Kamar
بَل نَّقذِف بالحق
بَل سَّوَّلَت لكم
بَل ظَّنَنتم
بَل طَّبَع الله عليها
بَل زُّين للذين كفروا
بَل تَّأتيهم بغتة
هَل تَّرى من فطور
هَل تَّرى لهم من باقية
هَل تَّعلم له سميا
هَل ثُّوِّبَ الكفار
Da sauransu
Saidai kuma Hisham yana yin Izharin هَل wurin ت a wuri daya cikin suratu Al-ra'ad أم هَل تَستَوى الظلمت
Haka kuma Yana Idgamin wadannan Kalmomin da zan jero
أَخَذتَّ أَخَذتُّم
اتَّخَذتَّ. اتَّخَذتُّم
لَبِثتَّ. لَبِثتُّم
أُورِثتُّمُوهَا بما كنتم
كهيعصٓ ذِّكرُ idan zaa wuce
مَن يُرِدثَّوَابَ
Haka kuma yana yin IZ'HARIN wadannan Kalmomin
اركَبْ مَعَنا
يَلْهَثْ ذَلك
والله أعلم
7- FAT'HA DA IMALAH الفَتحُ والإمالة
Nan Kuma Zamuyi bayani a takaice Matsayin Hisham a Wannan Babin
Riwayoyi sun kasu Gida Uku gameda abunda ya shafi Wannan Babin
1- Akwai wadanda Basuda Imala Ko Taq'lili ko daya Kamar Qira'ar Ibn Kathir da Abu Ja'afar
2- Akwai wadanda Imalah Daya Kawai Garesu Kamar, QALOON, warshu, Hafs,
Saidai kuma Warsh Yanada Taq'lili da yawa
3- Akwai masu Imaloli da Yawa kamar, Hamza da Kisa'i, Abu Amr da sauransu
Hisham yanada yana yin Imaloli a wurare Kadan A cikin Qur'ani Gasu Kamar haka
Yana imalar Harafin ن na kalmar
إِنـــٰـــهُ
Cikin Suratul-Ahzab
غَيرَ ناظرين إِنـــٰـــهُ
Yana imalar Harafin ش na kalmar
مَشَاربُ
Cikin Suratu Yasin
وَلهم فيها منفع ومَشَاربُ
Yana imalar Harafin ء na kalmar
ءانِية
Cikin Suratul Gashiyah
تُسقى من عين ءانِية
Yana imalar Harafin ع na kalmomi biyu na Suratul kafiruna
عابِدُونَ
عابِدٌ
Ayoyin
وَلا أنتم عابِدُونَ
ولا أناْ عابِدٌ
والله أعلم
8-YA'ATUL IDAFAH الياءات الإضافة
Ya'ul Idafah itace ya'un Da mai magana keyin anfani da ita domin Jingina wani abu zuwa gareshi
Wannan Ya'un Ta kasu Kashi-kashi
Kamar haka:-
= Akwai wace harafin Hamzah أإ mai fataha ko kasra ko Dwamma yake zuwa a gabanta
إِنِّــيٰٓ أَعلَم
إِنِّــيٰٓ أُرِيد
دُعَآءِىٰٓ إلا فرارا
= Akwai kuma wacce lamu-Al ( لام ال. التعريف ) ke zuwa a gabanta kamar haka
- لا ينال عَهدِى الظلمين
- عبادى الصلحون
- إنما حرم ربـى الفواحش
Da dai sauransu
= Akwai kuma wacce Hamzatu-waslin (الهَمزَةُ الوَصل) ke zuwa Gabanta kamar
- إنـى اْصطفَيتُك على الناس
- إن قومى اتخذوا
- يأتـى من بعدى اْسمه أحمد
= Akwai kuma wacce Haruffa ke zuwa a gabanta ba Hamzah أ ko Lamu-Al ba Misali
- أين شركآءِى قالوا
- من وراءِى وكانت امرأتي عاقرا
- لكم دينكم ولى دين
- إن أرضِى واسعة
Da sauransu
Mazhabar Hisham a wannan babin Itace Iskan Wato Daure Ya'un ي
Akwai wasu kalmomi da Hafs yake dauresu shi kuma Hisham yana yimusu Fat'ha
Gasu kamar haka
وما توفيقِيَ إلا بالله
إنما أشكوا بثى وحزنِـىَ إلى الله
كتب الله لأغلبن أنا ورسلىَ إن الله
مالِيَ أدعوكم
دُعاءِيَ إلا فرَارا
لعليَ أرجع إلى الناس
لعليَ ءاتيكم منها طه والقصص
لعليَ أعمل صلحا
لعليَ أطلع إلى إله موسى
لعليَ أبلغ الأسبب
عَهديَ الظلمين
إن أرضِيَ واسعة
صرطِيَ مُستقيمًا فاتبعوه
وجهيَ لله. وجهيَ للذي
ولمن دخل بيتيَ
بيتيَ للطائفين
Wadannan sune Yaat da Hisham yake yiwa fat'ha
Akwai wasu kalmomi da Hafs yake yimusu Fat'ha shi kuma Hisham yana Daure su
Gasu kamar haka
سأصرف عن ءايــٰــتي الذين يتكبرون في الأرض
مَعِي. A duk wuraren da hafs ke yimata fataha
بباسط يدي إليك
قل لعبادي الذين آمنوا يقيموا الصلوة
ما كان لـي من علم
ولـي فيها مآرب
ولـي نعجة
يعبادي لا خوف ya kara Ya'un
9- Ya'atuzzawa'id الياءات الزوائد
Ita kuma wannan Itama ya'un ce da Asalinta ba arubuce take ba a cikin Qur'ani, Anyi Ilhakinta ne a cikin Mushafi
Qurra'u sunyi sabani a wurin karanta ta Da kuma Waqafi akanta, sun kasu kashi uku
1- Akwai masu karanta ta A kowane irin yanayi ( lokacin tsayawa (WAQAFI) a kanta, ko lokacin wucewa da karatu a kanta) kamar Ibn Kathir
2- Akwai Wadanda basu karantawa da ita A kowane irin yanayi Na karatu ( lokacin tsayawa (WAQAFI) a kanta, ko lokacin wucewa da karatu a kanta) Kamar Hafsu
3- Akwai wadanda ke Tabbatar da ita a lokacin wucewa da Karatu, suna cireta wurin WAQAFI Kamar warsh Da Al-imam Al-dury
Al-imam Al-susi yana Tabbatar da wannan Ya'un ne kawai A lokacin sadar da karatu
Akwai wuraren da yake saka Ya'un din haka kuma Akwai inda baya sakawa
Sai a nemi littafai domin akarin bayani
Ya'atuz-zawa'id Tana zuwa ne a cikin wadannan kalmomin da ire-iren su
![👇](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/t4f/1/16/1f447.png)
![👇](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/t4f/1/16/1f447.png)
![👇](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/t4f/1/16/1f447.png)
![👇](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/t4f/1/16/1f447.png)
إلى الداع
إذا دَعَان
واليل إذا يَسر
=الجَوَار
الجَواب
يناد المناد
Da sauransu
Hisham Bayada Wannan Ya'un din da yawa saidai kuwa Wurin da yakeda ita to yana tabbatar da ita ne a halaye biyu na karatu (lokacin tsayawa ko wucewa da karatu)
Kamar Wannan kalmar
ثُم كِيدونِ>فلا تنظرون
Haka kuma Hisham yana cire Ya'un din wannan kalmar
فما ءتَــــٰــــنِ اللهُ خير
Domin neman Karin Bayani a Bincika cikin littafan da sukayi magana akan Wannan Riwayar.
5- RUFEWA
وَحُــــجَّــــتِــــي قِـــــــرَاءَةُ ابـنِ عَـــــامِــــر
فَـــــكَـــم لَــهَـــا مِـن عَــاضـــدِ وَنَـــــاصِـــــرِ
Anan zamu tsaya sai a taremu a rubutu na gaba inda zamuyi Rubutu akan Riwayar Ibn Zakwan Daya daga cikin Riwayoyin Ibn Amir
Insha Allah
JAN HANKALI
![👇](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/t4f/1/16/1f447.png)
![👇](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/t4f/1/16/1f447.png)
![👇](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/t4f/1/16/1f447.png)
![👇](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/t4f/1/16/1f447.png)
Duk wanda Zaiyi sharing ko Kwafi Na wannan Rubutun nawa To ya yi Sharing Dinshi A yadda Na Rubutashi Kar ya kara komai kuma Kar ya canja komai abar shi yadda nayishi
Duk wanda yakeda Taaliki ko gyara Ko shawara ko Mulahaza akan Wannan Rubutun to ya atuntubeni nizan gyara Da kaina Amma Kar A canja Min rubutu.
Ga lambar da zaa tuntubeni da ita +2348034468543
![✍️](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/te2/1/16/270d.png)
Habibu Muhammad Shugaba
+2348034468543
Wednesday
27-03-1443
03-11-2021
No comments:
Post a Comment