قِرَاءَةُ ابن عَامِر
اليَحْصَُِبِــي المَازِنِيُّ الدِّمَشْقِي الشَّامِيُّ
TARIHIN QARI'AI GOMA 10 DA RIWAYOYINSU 20
تاريخ القراء العشرة ورواتهم
RUBUTU NA: 11
Rubutawar
![✍](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/te2/1/16/270d.png)
ABUBUWAN DA KE KARKASHIN WANNAN RUBUTUN
![👇](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/t4f/1/16/1f447.png)

1- WANENE AL-IMAM IBN AMIR
2- MATSAYIN AL-IMAM IBN AMIR
3- YABO DA KUMA MAGANAR MALAMAI GAMEDA AL-IMAM IBN AMIR
4- WASU DAGA CIKIN SAHABBAN DA AL-IMAM IBN AMIR YA HADU DASU
5- MALAMAN AL-IMAM IBN AMIR
6- DALIBAN AL-IMAM IBN AMIR
7- KALMOMINDA QIRA'AR IBN AMIR TA SABAWA DUKKAN QIRA'O'I WURIN KARANTASU
8- RUFEWA
1- WANENE AL-IMAM IBN AMIR?
Sunanshi:- Abdullahi ibn Amir ibn yazid ibn tamin ibn Rabi'ah ibn Amir ibn Abdillahi ibn Imron Al-yahsubi
Ana Ce mishi Al-yahsabi ne Nisbah Zuwaga Daya daga cikin kakanninshi mai suna YAHSIB ibn Dahman ibn Amir ibn Himyar ibn Saba'i
Yadda ake karanta Kamar
Al-yahsabi
![👉](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/t51/1/16/1f449.png)
Zaa iya Karanta wannan Sunan Da yiwa harafin ص dukkanin wasulla guda uku wato Fat'ha ko Kas'ra ko dwamma
Kamar Haka
![👇](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/t4f/1/16/1f447.png)
![👇](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/t4f/1/16/1f447.png)
![👇](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/t4f/1/16/1f447.png)
![👇](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/t4f/1/16/1f447.png)
اليَحْصَبِي Al-yahsabi
اليَحْصِبِي Al-yahsibi
اليَحْصُبِي. Al-yahsubi
Al-kunyarshi:- Anyi Sabani akan Hakikanin Al-kunyarshi amma mafi inganci daga cikinsu Shine ABU IMRAN
LAKABINSHI:- Al-imam As-shadibiyy Ya kira ibn Amir Da sunanshi da kuma Lakubba Da yawa a cikin Shadibiyya
Ga wasu daga ciki
![👇](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/t4f/1/16/1f447.png)
![👇](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/t4f/1/16/1f447.png)
![👇](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/t4f/1/16/1f447.png)
عَبْدُ الله Abdullahi
ابن عامر Ibn Amir
الشََّامِي As-shami
الدِّمَشْقِي Al-dimashQi
اليَحْصَُِبِي Al-yahsabi
المَازِنِيُّ Al-maziniyy
An haifeshi a shekara ta 8 Bayan Hijrah magana Mafi inganci Kamar Yadda shi Ibn amir din ya tabbatar da kanshi
Khalid ibn Yazid yace: Naji Abdullahi ibn Amir yana cewa "An haifeni a shekara ta 8 bayan Hijrah, koda Manzon Allah صلى الله عليه وسلم ya Rasu inada Shekaru 2"
Ibn Al-jazari yace Wannan Itace Magana Mafi inganci gameda Ranar Haihuwar ibn Amir.
Kasancewar wasu na cewa an haifeshi a shekara ta 21 Bayan Hijrah
والله أعلم
Ya Rasu A garin Dimashqa Ranar Ashura Shekara ta 118 Bayan Hijrah
2- MATSAYIN AL-IMAM IBN AMIR
Al-imam ibn Amir Tabi'i ne Kuma thiqa ne Amintacce mai Gaskiya
Al-imam ibn Amir Shine Shugaban Masu Karatun Qur'ani da kuma karantar Dashi A kasar Sham a zamanin shi
Yayi Limanci Shekaru Masu Yawa a masallacin da ake kira Al-jami'ul umawiyy dake Sham Tun kafin Khalifancin khalifah UMAR IBN ABDUL-AZIZ Da kuma bayan wucewarshi
Khalifah umar ibn Abdul-aziz ya Hadamishi Mukaman Limanci Da kuma Al-kalanci Da Jagorancin Makaranta Qur'ani
Mutane sun kasance suna Zuwa Sham Daga Kasashen Duniya Domin Suyi Karatun Qurani Ga Al-imam ibn Amir
3- YABO DA KUMA MAGANAR MALAMAI GAMEDA AL-IMAM IBN AMIR
ABU ALIY AL-AHWAHI YACE :- "Abdullahi ibn Amir ya kasance Imami, Masani, siqa ne akan duk abunda yazo mishi, Hafizi mai (kiyayewa)ne ga Abunda ya rawaito, Mai kyautawa ne ga abunda duk ya kiyaye, Masani ne mai tsayuwa kyam ne akan abunda yazo dashi, mai Gaskiya ne akan Abunda ya nakalto, Yana cikin masu Falala daga cikin Musulmi, Daya daga cikin Zababbun Tabi'ai, Daya daga cikin manyan marawaita, Ba'a tuhumarshi Ga addininshi, Baa shakka a cikin Yakininshi, Ba'a tababa ko tantama akan Amanar shi, Ba'a sukar shi Ga Riwayar shi, Abunda ya Rawaito Ingantaccene, Maganar shi cike take da Fasaha, Mai babban matsayi ne, wanda ake yiwa Da'a ne, Ya shahara da ilimi, Wanda ake Komawa ga fahimtar shi ne, Baya Kaucewa Ingantaccen Asari, Baya Fadar maganar Da ta sabawa Hadisi"
YAHYA IBN AL-HARIS YACE: " ibn Amir Limamin masallacin jumaa ne الجامع الأموي Baya Barin Duk wata Bidi'a idan yaga ana yinta face sai ya canta ta"
AL-IMAM AL-ZAHABI YACE:- " Babban Jagora, Malamin Qur'ani ne a kasar Sham, Daya daga cikin mayyan Malamai, Abu imran, Al-yahsubi Al-shami"
4- WASU DAGA CIKIN SAHABBAN DA AL-IMAM IBN AMIR YA HADU DASU
An rawaito cewa Ibn Amir ya Hadu da wssu daga cikin Sahabban Annabi صلى الله عليه وسلم har ma yaji Karatun wasu daha cikinsu
Ga Kadan daga cikin wadanda ya hadu dasu
1- Mu'awiyah Bn Abi Sufyan رضي الله عنهما
2- Al-nu'uman bn Bashir رضي الله عنه
3- Wasilah bn Al-Asqa'a رضي الله عنه
4- Fadalah ibn Ubaid رضي الله عنه
5- Abul-Dar'da'a رضي الله عنه
6- usman bn Affan رضي الله عنه
Da wasun Wadannan رضي الله عنهم أجمعين
5- MALAMAN AL-IMAM IBN AMIR
Al-imam ibn Amir yanada malamai da yawa waau ma daga cikin malamanshi Sahabban Annabi صلى الله عليه وسلم ne
Ga kadan daga Cikinsu
1- Al-mugirah bn Shihab صاحب عثمان بن عفان رضي الله عنه
2- Abul-Dar'da'a
Abu Amr Al-dani ya tabbatar da wannan maganar Ta cewa yayi karatu gareshi
![👉](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/t51/1/16/1f449.png)
3- Fadalah ibn ubaid
Isnadin wannan Maganar Jayyid ne
![👉](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/t51/1/16/1f449.png)
4- Usmanu bn Affan رضي الله عنه
anyi magana Uku akan Karatun ibn Amir Ga Sayyidina usman
![👉](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/t51/1/16/1f449.png)
![👇](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/t4f/1/16/1f447.png)
![👇](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/t4f/1/16/1f447.png)
![👇](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/t4f/1/16/1f447.png)
= Cewa ibn Amir ya saurari karatun Sayyidina usman, Kuma wannan Mahanar zata iya zama daidai
= cewa ibn Amir ya karanta wani sashe na Qur'ani Ga Sayyidina usman, wannan ma Zai iya yiyuwa
= cewa Ibn Amir Ya karanta Qur'ani gaba daya ga Sayyidina usman, Wannan kuma bai tabbata ba
5- wasilah ibn Al-asqa'
Zamu takaitu da wadannan saboda isnadin Karatun shi ga wasu malaman bai inganta ba
والله أعلم
6- DALIBAN AL-IMAM IBN AMIR
Ga kadan Daga Cikin Daliban ibn Amir wadanda sukayi karatu gareshi Baki-da baki
![👇](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/t4f/1/16/1f447.png)
![👇](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/t4f/1/16/1f447.png)
![👇](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/t4f/1/16/1f447.png)
1- Yahaya ibn Al-haris Al-zimary ( Shine ya zamo halifan ibn amir a Sham)
2- Abdulrahman ibn Amir ( Dan uwan ibn Amir ne)
3- Rabi'ah ibn Yazid
4- Ja'afar ibn Rabi'ah
5- Isma'il ibn Abdillahi ibn Abil-muhajir
6- Sa'id ibn Abdul-aziz
7- Khallad ibn subaih Al-mirry
8- yazid ibn Abi malik
Da wsun wadannan
GA WANI BAYANI MAI MUHIMMANCI DA YA KAMATA MU SANI

Mu sani cewa Hisham Da ibn Zakwan Basuyi karatu kai tsaye ga Ibn amir ba Akwai wasidar maluma a tsakanin su da ibn Amir Su bama Daliban daliban Ibn amir bane
Ga yadda abun Yake
![👇](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/t4f/1/16/1f447.png)
![👇](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/t4f/1/16/1f447.png)
![👇](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/t4f/1/16/1f447.png)
![👇](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/t4f/1/16/1f447.png)
Ibn Amir ya karantar da Yahaya Al-zimary
Shi kuma Yahaya ya karantar da wadannan
![👇](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/t4f/1/16/1f447.png)
![👇](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/t4f/1/16/1f447.png)
![👇](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/t4f/1/16/1f447.png)
= Ayyub ibn Tamin
= Irak ibn khalid
= Sadakatu ibn khalid
= Suwaid ibn Abdul-aziz
![👆](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/tce/1/16/1f446.png)
![👆](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/tce/1/16/1f446.png)
![👆](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/tce/1/16/1f446.png)
Hisham Yayi karatu ga wadannan Hudu 4 da na ambata a sama![👆](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/tce/1/16/1f446.png)
![👆](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/tce/1/16/1f446.png)
Shi kuma ibn amir yayi karatu ga biyu daga cikinsu
![👇](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/t4f/1/16/1f447.png)
![👇](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/t4f/1/16/1f447.png)
![👇](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/t4f/1/16/1f447.png)
= Ayyub ibn Tamin
= Irak ibn khalid
Wannan shine Ma'nar Fadar Al-imam As-shadibiyy
هِشَامٌ وَعَبْدُ الله وَهْوَ انتِسَابُهُ
لِــذَكْوَانَ بِالإِســنَـــادِ عَــنْـه تَــنَـقَّلَا
Fassara
Rawiyan Ibn Amir biyu sune Hisham da kuma Abdullahi shine Ake nasabtawa Zuwa ga Zakwan, Sun Nakalto Qira'ar ibn Amir ne Da isnadi.
Ga Silsilar Riwayar Hisham da larabci
رواية هِشَام بن عمار السُّلَمي، عن عِرَاك بن خالد الدِّمَشْقِي، عن يحيى بن الحارث الذِّمَاري، عن عبدالله بن عامر الشامي، عن أبي الدرداء رضي الله عنه عن النبي صلى الله عليه وسلم
Wannan kuma na Ibn Zakwan ne
![👇](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/t4f/1/16/1f447.png)
![👇](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/t4f/1/16/1f447.png)
رِواية عبدالله بن ذكوان، عَن أبِـي أيوب بن تَميم الدِّمَشْقِي، عن يحيى بن الحارث الذِّمَاري، عن عبدالله بن عامر الشامي، عن أبي الدرداء رضي الله عنه عن النبي صلى الله عليه وسلم
Wadanda ake Jinginawa riwayoyi (Masu Riwaya) Sun kasu gida uku
1- akwai wadanda sukayi karatu baki da baki ga QARI'AI da ake jinginawa riwayarsu zuwa garesu kamar
- Qalun da warsh sunyi karatu baki da baki ga Nafi'u
2- Akwai wadanda A tsakaninsu da QARI'AN akwai wasidar Mutun Daya kamar
- Dury da susi Sunyi karatu ga Yahyal-Yazidiyyi shi kuma yahya yayi karatu ga Abu Amr Al-basry
-Kamar Khalaf da khallad Sunyi karatu ga Sulaim shi kuma sulaim Yayi Karatu Ga Hamzah
3- Akwai wadanda akwai fiye da mutun daya a tsakaninsu da QARI'IN DA sukayi riwaya a gareshi kamar
- Hisham da ibn Zakwan basuyi karatu kai tsaye ga ibn Amir ba Akwai fiye da mutun daya a tsakanin su
Abun da yasa hakan ta faru shine
A lokacin da wannan ilimin na riwayoyi yayi yawa ya fadada riwayoyin sunyi yawa Kasancewar kowane Qari'i yanada dalibai masu dinbin yawa kuma kowane daga cikin su yana jingina riwayar shi zuwaga wannan Qari'in
Sai akayi niyyar Takaita Riwayoyin Akace kowane QARI'I zaa fitar da mutun biyu daga cikin Rawiyanshi (Dalibanshi) Wadanda sukafi kwarewa da kuma tsoron Allah Da tsantseni domin a jingina riwayar shi zuwa garesu
Sai a bincika Idan an samu wanda ya cika sharudan daga cikin Daliban QARI'IN, haka kuwa akayi Zabin Ya fada Ga Duriy da Susi sai aka aka cigaba da jingina Qira'ar Abu Amr Al-basry zuwa garesu, Riwayar su kuma ake jinginata kai tsaye zuwa gareshi (Abu Amr Al-basry) Sabanin asalin Malaminsu ( yahyal-yazidiyyi)
Wannan shine Ma'anar Fadar Shadibiyy
تَخَيرَهم نُقَّادُهُم كلَّ بَارِعٍ
وَلَيسَ عَلى قُرءَانِه مُتَأَكِّلا
Adadin Ayoyin Qur'ani na wannan QIRA'AR 6226
عَدُّ الشََّامِي
Wato Qirgar Ayoyi bisa Qirgar Sham Shine Akayi Aiki dashi wurin kayyade adadin Ayoyin Qur'anin Qira'ar ibn Amir
والله أعلم
Al-imam As-shadibiyy ya sanya Ramzin كَـــلَِـــمْ ya zamo alamar da za'a Gane ibn Amir da ita da kuma Riwayoyin shi biyu Hisham da ibn Zakwan
Ko ince Daya daga cikin Alamomin da zaa ganesu da ita
Ga abunda yake nufi
كَـــلَِـــمْ
1- idan mukaga Ramzin ك a cikin Shadibiyya To Ramzi ne dake Nuni Ga Qira'ar Ibn Amir
2- idan mukaga Ramzin ل a cikin Shadibiyya To Ramzi ne dake Nuni Ga Riwayar Hisham
3- haka kuma idan mukaga Ramzin م a cikin Shadibiyya To Ramzi ne dake Nuni Ga Riwayar ibn Zakwan
Duk da cewa Wani lokacin yana ambatar su da sunayensu ko lakubansu gwargwadon yadda Lalurar waka ta bayar
والله أعلم
7- KALMOMINDA QIRA'AR IBN AMIR TA SABAWA DUKKAN QIRA'O'I WURIN KARANTASU
Kowace Qira'a Tanada Wasu kalmomi da ta Sabawa Sauran Qira'o'i a wurin fadarsu
Ga Kalmomin da Qira'ar ibn Amir ta sabawa Sauran Qira'o'i
Zan kawo Kalmominda Riwayoyinshi biyu sukayi ittifaqi
Bazan kawo wadda daya ke karantawa banda daya ba
Saidai Abun Lura anan Shine Kalmar da nayiwa wasali ita nike nufi a saba gareta Kuma yadda nayi wasalin hakanan yake karantawa duk da cewa Zaa iya samun kalmai mai banbancin Qira'at fiye da biyu To yadda nayi wasali haka nike nufin ibn Amir ya sabawa sauran
Ga kalmomin
![👇](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/t4f/1/16/1f447.png)
1- وقولوا حطة تُغْفَرْ لكم.
2- ما نُنسِخْ من ءاية أو ننسها
3- إن الله سميع عليم (١١٥) قَالُوا اتخذ الله ولدا
Yana cire harafin و dame Farkon wannan Ayar
4- فإنما يقول له كن فيكونَ
Yana yin Fat'ha ga Harafin نَ a wadannan surorin
![👇](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/t4f/1/16/1f447.png)
![👇](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/t4f/1/16/1f447.png)
البقرة. ءاية ١١٧
آل عِمْران ءاية ٤٧
مريم ءاية ٣٥
غافر ءاية ٦٨
Sauran da ban ambata ba Akwai biyu da yakeyin Fat'har su tareda Kisa'i ban anbacesu ba saboda ina kawo abubuwan da ya sabawa kowa ne
Wasu kuma yana karantasu da dwammar harafin نُ
فيكونُ kamar yadda sauran Riwayoyi ke karantawa
![👉](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/t51/1/16/1f449.png)
5- وَبِالكِتَــٰــبِ المنير. سورة آل عمران ءاية ١٨٤
Yana kara harafin و
6- إِبْرَاهَـــــــٰــــمَ
DUK Wadanda sukazo cikin baqara duk da cewa Ibn Zakwan yanada Fuska Biyu a na garesu إِبْرَاهَـــــــٰــــمَ ko إِبْرَاهِـــــيـــــمَ
Sauran surori kuma Hisham ya zabi wasu yana Karanta su إِبْرَاهَـــــــٰــــمَ wasu kuma ya barsu إِبْرَاهِـــــيـــــمَ kamar sauran Qira'o'i
7- فَأُمْتِعُهُ قليلا
8- ولكل وجهة هو مُوَلَّـــــــٰـــــهَا
Da yin fat'ha ga لَ
9- إذ يُرَوْنَ العذاب ان القوة لله جميعا
10- بثلـــٰـــثة ءالـٰــــف من الملئكة مُنَزَّلِينَ
11- الذين قُتِّلُوا في سبيل الله
آل عِمْران ءاية ١٦٩
12- جاءوا بالبينــٰــت وَبِالزُبُرِ
Da kara harafin ب
آل عِمْران ءاية ١٨٤
13- ما فعلوه إلا قَلِيلٌ منهم
14- أفحكم الجـــٰــهلية تَبْغُونَ
15- جعل الله الكعبة البيت الحرام قِيَـمًا للناس
Da cire madda
16- وَلَدَارُ الآخِرَةِ خير للذين يتقون
الأنعام ءاية ٣٢
17- ولا تطرد الذين يدعون ربهم بِالغُدْوَةِ والعشي
18- وإما يُنَسِّيَنَّكَ الشيطــٰــن
19- وما ربك بغفل عما تعملون (١٣٢) وربك الغني
20- وكذلك زُيِّنَ لكثير من المشركين قَتْلُ أَوْلَـــٰــــدَهُمْ شُرَكَآئِهِمْ
21- وإن تَكُنْ مَيْتَةٌ فهم فيه
22- إلا أن تكون مَيْتَةٌ
Duk da cewa Abu ja'afar yanada Qira'a kamar wannan amma sun dan Saba Kadan
23- وأن هذا صِرَاطِـيَ مستقيما
24- قليلا ما يَتَذَكَّرُونَ (٣)
Farko-farkon Surar A'araf
25- مَا كنا لنهتدي لولا أن هدىنا الله
Yana cire harafin و wurin وما كنا
26- يطلبه حثيثا والشمسُ والقمرُ والنجومُ مسخراتٌ بأمره
27- نُشْرََا
A wurin kalmar بُشْرََا a duk inda tazo
28- ولا تعثوا في الأرض مفسدين(٤٣) وَقَالَ الملأ الذين استكبروا
Yana kara harafin و
29- وإذ أَنجَـــٰـــكُم من آل فرعون
سورة الأعراف
30- ويضع عنهم ءَاصَــــٰـــرَهُمْ
31- تغفر لكم خَطِـــيٰٓـــئَتُكُمْ سنزيد المحسنين
32- وأخذنا الذين ظلموا بعذاب بِئْسٍ
33- ولو ترى إذ تَتَوَفَّـى الذين كفروا
34- ولا يحسبن الذين كفروا سبقوا أَنَّهُمْ لا يعجزون
35- إنهم لا إِيمَـــٰـــنَ لهم لعلهم ينتهون
36- وسخر لكم اليل والنهار والشَّمْسُ والقَمَرُ...
37- ثم إن ربك للذين هاجروا من بعد ما فَتَنُوا
38- ولا تُشْرِكْ في حكمه أحدا
39- واصبر نفسك مع الذين يدعون ربهم بِالغُدْوَةِ والعشي
40- أَشْدُدْ به أزري
41- وَأُشْرِكْهُ في أمري
42- قل إنما أنذركم بالوحي ولا تُسْمِعُ الصُّمَّ الدعآء
43- ثم قُتِّلُوا أو ماتوا ليرزقنهم الله
44- وَأَنْ هذه أمتكم أمة واحدة
45- أم تسئلهم خرجا فَخَرْجُ ربك خير
46- وتوبوا إلى الله جميعا أَيُّهُ المؤمنون
47- وقالوا يــٰٓــأَيُّهُ الساحر ادع لنا ربك
سورة الزخرف
48- سنفرغ لكم أَيُّهُ الثقلان
سورة الرحمن
49- فَنَقُولُ ءأنتم أضللتم عبادي هؤلاء
50- يُضَعَّفُ له العذاب يوم القيــٰــمة
51- أولم تَكُنْ لهم ءَايَةٌ أن يعلمه....
52- إنا مُنَزِّلُونَ على أهل هذه القرية رجزا
53- إنّ أَرْضِيَ واسعة فإيـى فاعبون
54- تَظَّــٰــهَرُونَ منهن أمهتكم
55- وقالوا إن هذا إلا سحر مبين (١٦) إِذَا متنا وكنا ترابا وعظما...
سورة الصافات
56- قل أفغير الله تَأْمُرُونَنِـى أعبد
57- كانوا أشد مِنكُمْ قوة وءاثارا في الأرض فأخذهم الله بذنوبهم
Yana sa harafin ك wurin هـ
58- وَالحَبَّ ذَا العَصْفِ وَالرَّيْحَانَ
59- تبارك اسم ربك ذُو الجلــٰـل والإكرام
Yana sa Harafin و wurin ي
60- وَكُــــلٌّ وعد الله الحسنى والله بما تعملون خبير
سورة الحديد
61- يوم القيمة يُفَصَّلُ بينكم والله بما تعملون بصير
62- هل أدلكم على تجارة تُنَجِّيكُم من عذاب أليم
63- لِإِلَـــٰـــفِ قريش
Yana cire harafin ي ta madda
Wadannan sune Abubuwan na samu damar Kawowa a cikin kalmomin da Qira'ar Ibn Amir ta Sabawa Sauran Qira'o'i a wurin fadarsu
A nemi littafan Qira'at domin neman Karin bayani akan Wannan Runutun da nayi
Zai iya yiyuwa ban rubuta abunda Ya kamata in rubuta ba ko kuma Akwai gyara a wasu Wurare da ba'a rasaba
والله أعلم
8- RUFEWA
وَحُــــجَّــــتِــــي قِـــــــرَاءَةُ ابـنِ عَـــــامِــــر
فَـــــكَـــم لَــهَـــا مِـن عَــاضـــدِ وَنَـــــاصِـــــرِ
Anan zamu tsaya sai a taremu a rubutu na gaba inda zamuyi Rubutu akan Riwayar Hisham Daya daga cikin Riwayoyin Ibn Amir
Insha Allah
JAN HANKALI
![👇](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/t4f/1/16/1f447.png)
![👇](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/t4f/1/16/1f447.png)
![👇](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/t4f/1/16/1f447.png)
![👇](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/t4f/1/16/1f447.png)
Duk wanda Zaiyi sharing ko Kwafi Na wannan Rubutun nawa To ya yi Sharing Dinshi A yadda Na Rubutashi Kar ya kara komai kuma Kar ya canja komai abar shi yadda nayishi
Duk wanda yakeda Taaliki ko gyara Ko shawara ko Mulahaza akan Wannan Rubutun to ya atuntubeni nizan gyara Da kaina Amma Kar A canja Min rubutu.
Ga lambar da zaa tuntubeni da ita +2348034468543
![✍️](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/te2/1/16/270d.png)
Habibu Muhammad Shugaba
+2348034468543
Tuesday
27-02-1443
05-10-2021
No comments:
Post a Comment