قِرَاءَةُ الإِمَام عَاصِمٍ
ابن أبِـي النَّجُود الكُوفِـي
TARIHIN QARI'AI GOMA 10 DA RIWAYOYINSU 20
تاريخ القراء العشرة ورواتهم
RUBUTU NA:
Rubutawar
Habibu Muhammad shugaba
ABUBUWAN DA WANNAN RUBUTUN YA KUNSA
1- WANENE AL-IMAM ASIM
2- MALAMAN AL-IMAM ASIM
3- YABO DA KUMA MAGANAR MALAMAI GAMEDA AL-IMAM ASIM
4- DALIBAN AL-IMAM ASIM
5- KALMOMINDA QIRA'AR ASIM TA SABAWA DUKKAN QIRA'O'I WURIN KARANTASU (انفرادت قراءة الإمام عَاصِم)
6- RUFEWA
1- WANENE AL-IMAM ASIM?
SUNANSHI:- Asim Ibn Bahdalah, ibn Abin-najud, Al-kufi, Al-Asadiyy
ALKUNYARSHI:- Abu Bakr wasu kuma Sukace Abu Amr
Ance Abun-najud Shine Sunan Mahaifinshi na Hakika wasu Sunce sunan Abun-najud din Abdullahi
BAHDALAH:- Sunan Mahaifiyarshi ne
Asim Daya Ne daga Cikin QARI'AI 7 Na Qur'ani
Asim Masanin Qur'ani da Hadisi ne
Bayan Rasuwar Abu Abdil-raman As-sulami Asim ne ya zamo Shugaba kuma Jagora a Fannin karatun Qur'ani a garin Kufa
Haka kuma Asim mutum ne mai fasaha, mai dadin sauti, masanin Tajwidin Qur'ani, Masanin Hadisi.
An Haifi Asim A garin Kufa ya rayu a garin kufa haka ma Ya rasu a garin kufa
A dana binciken da Nayi Mafi yawan Littafan da na Duba Maluma Basu Hakaito Ayyanannar Rana ko shekarar da aka Haifi Asim Ba
Sai dai naga Wadanda Sukace An haifeshi a shekara ta 700 miladiyyah
Asim Ya rasu a shekara ta 127 bayan Hijrah dai dai da 745 Miladiyyah
رحمه الله رحمة واسعة
2- MALAMAN AL-IMAM ASIM
1- Zirru Dan Hubaish
Shi kuma Zirru ya yi Karatu ne ga Sahabi Abdullahi Dan Mas'ud رضي الله عنه
2- Abu Abdil-rahman Al-sulami
Shi kuma Abu Abdil-rahman ya yi karatu ne Ga Sahabi Aliyu Bn Abi Dalib رضي الله عنه
3- Abu Amr Sa'ad Ibn Iyas
An Hakaito cewa shi wannan Sa'ad Ibn Iyasdin Ya Riski Zamani Annabi صلى الله عليه وسلم Sai dai Bai Hadu Da Annabi صلى الله عليه وسلم ba ya yi Karatu Ga Sahabi Abdullahi Dan Mas'ud رضي الله عنه
Tsakanin Asim Da Annabi صلى الله عليه وسلم Mutum biyu ne kawai
Saboda haka Zamu iya Cewa Qira'arshi Itace Mafi Gajartar Isnadi Daga Cikin Qira'o'i Goma Idan Aka Cire Qira'ar Ibn Kathir da ta Ibn Amir Domin su sunyi Karatu har ga wasu Daga cikin Sahabbai
GA Silsila ko ince Isnadin Riwayoyi Biyu na Qira'ar Asim
1-Riwayar Shu'ubah An Asim
2- Riwayar Hafs An Asim
1-Riwayar Shu'ubah An Asim
رِواية أبي بكر شعبة بن عَيَّاش ابن سَالِمٍ الأَسَدِي الكُوفِي لقراءة عاصم بن أبي النَّجُود الكُوفِي التَّابعِـي عن زِرِّ بن حُبَيْشٍ عن عبد الله بن مسعود وعثمان بن عفان وعَلِـي بن أبي طالب رضي الله عنهم عن النبى صلى الله عليه وسلم.
2- Riwayar Hafs An Asim
رِواية حَفْص بن سليمان الأَسَدِي الكُوفِي لقراءة عَاصِم بن أبي النَّجُود الكُوفِي التَّابعِـي عن أبي عبد الرحمن السَُلَمِـي عَن عثمان بن عفان وعَلِـي بن أبي طالب وزيد بن ثَابِت وأُبَـيُّ بن كَعْب رضي الله عنهم أجمعين عن النبى صلى الله عليه وسلم.
3- YABO DA KUMA MAGANAR MALAMAI GAMEDA AL-IMAM ASIM
= Shu'ubah Ibn Ayyash Yace:- Asim Ya cemin " Nayi Rashin Lafiya Har Tsawon Shekara Biyu Wata Rana na Karance Qur'ani Ba tareda nayi Kuskuren Koda Harafi Daya ba"
Wannan Shi zai Nuna Muna Karfin Haddar Shi Domin ya yi Rashin Lafiya Bayan Yaji sauki yayi wannan karatun
=Ibn Ayyash Yace:- Sau da yawa nikejin Abu Ishaq Assabi'i yana Cewa " Ban Taba Ganin Wanda yafi Asim ibn Abin-Najud Iya karatu ba"
= Yahya Ibn Adam Ya Riwaito daga Hassan Ibn Salih Yana Cewa " Ban taba ganin sanda Yafi Asim Fasaha ba"
=Abdullahi ibn Ahmad Ibn Hanbal yace :- Na Tambayi Babana (Ahmad Dan Hanbali Daya daga Cikin Malaman Mazhabobi hudu) Na tambayeshi Gameda Asim Yace " Mutumin Kirki ne Siqah Salihi"
4- DALIBAN AL-IMAM ASIM
Asim Yanada Dalibai Da yawa Ga wasu daga Cikinsu
1- Aban Ibn Taglib
2- Aban Ibn Yazid Al-Addar
3- Hassan Ibn Salih
4- Hafs Ibn Sulaiman (mai Riwayah)
5- Al-hakam Ibn Zuhair
6- Hammad ibn Salamah
7- Hammad ibn Abi Ziyad
8- Hammad ibn Amr
9- Sulaiman ibn Mahran Al-A'amash Al-kufi
10- Sallam ibn Sulaiman
11- Abubakar ibn Ayyash Shu'ubah (Mai Riwayah)
12- Abu Amr Al-basry (mai Qira'ah)
13- Khalil ibn Ahmad Alfarahidi( Masanin Nahawu)
14- Hamzah ibn Habib Al-zayyat ( Mai Qira'ah)
15- Al-mugirah Al-dwabbi)
Da dai sauransu
Riwayar Shu'ubah Itace Ake Gabatarwa Akan Riwayar Hafs a wurin Jeranta Riwayoyi Ko Kuma جَمْعُ القِراءَات
Da Sauransu
Shu'ubah Da Hafs Sunyi Karatu Ga Asim Ne kai tsaye Baki-da-Baki
Sabanin wasu riwayoyin wanda Ana iya Samun Tsakanin msu da Qari'in da ake Jingina Riwayar su gareshi Akwai Wasidar Mutun Daya ko biyu wasu ma Sama da haka
GA WANI BAYANI MAI MUHIMMANCI DA YA KAMATA MU SANI
Wadanda ake Jinginawa riwayoyi (Masu Riwaya) Sun kasu gida uku
1- akwai wadanda sukayi karatu baki da baki ga QARI'AI da ake jinginawa riwayarsu zuwa garesu kamar
- Shu'ubah da Hafsu Sunyi karatu Kai tsaye Ga Asim
2- Akwai wadanda A tsakaninsu da QARI'AN akwai wasidar Mutun Daya kamar
- Dury da susi Sunyi karatu ga Yahyal-Yazidiyyi shi kuma yahya yayi karatu ga Abu Amr Al-basry
-Kamar Khalaf da khallad Sunyi karatu ga Sulaim shi kuma sulaim Yayi Karatu Ga Hamzah
3- Akwai wadanda akwai fiye da mutun daya a tsakaninsu da QARI'IN DA sukayi riwaya a gareshi kamar
- Hisham da ibn Zakwan basuyi karatu kai tsaye ga ibn Amir ba Akwai fiye da mutun daya a tsakanin su
Abun da yasa hakan ta faru shine
A lokacin da wannan ilimin na riwayoyi yayi yawa ya fadada riwayoyin sunyi yawa Kasancewar kowane Qari'i yanada dalibai masu dinbin yawa kuma kowane daga cikin su yana jingina riwayar shi zuwaga wannan Qari'in
Sai akayi niyyar Takaita Riwayoyin Akace kowane QARI'I zaa fitar da mutun biyu daga cikin Rawiyanshi (Dalibanshi) Wadanda sukafi kwarewa da kuma tsoron Allah Da tsantseni domin a jingina riwayar shi zuwa garesu
Sai a bincika Idan an samu wanda ya cika sharudan daga cikin Daliban QARI'IN, haka kuwa akayi Zabin Ya fada Ga Duriy da Susi sai aka aka cigaba da jingina Qira'ar Abu Amr Al-basry zuwa garesu, Riwayar su kuma ake jinginata kai tsaye zuwa gareshi (Abu Amr Al-basry) Sabanin asalin Malaminsu ( yahyal-yazidiyyi)
Wannan shine Ma'anar Fadar Shadibiyy
تَخَيرَهم نُقَّادُهُم كلَّ بَارِعٍ
وَلَيسَ عَلى قُرءَانِه مُتَأَكِّلا
Adadin Ayoyin Qur'ani na wannan QIRA'AR 6236
عَدُّ الكُوفِـيـينَ
Wato Qirgar Ayoyin Mutanen Kufa Wanda aka Riwaito daga Abu Abdilrahman Abdullahi ibn Habib As-sulami, shi kuma ya Riwaito daga Sahabi Aliyu ibn Abi Dalib رضي الله عنه
والله أعلم
Al-imam As-shadibiyy ya sanya Ramzin نَـــصَــــعْ ya zamo alamar da za'a Gane Qira'ar Asim da ita da kuma Riwayoyin shi Biyu Shu'ubah Da Hafsu
Ko ince Daya daga cikin Alamomin da zaa ganesu da ita
Ga abunda yake nufi
نَـــصَــــعْ
1- idan mukaga Ramzin ن a cikin Shadibiyya To Ramzi ne dake Nuni Ga Qira'ar Asim
2- idan mukaga Ramzin ص a cikin Shadibiyya To Ramzi ne dake Nuni Ga Riwayar Shu'ubah
3- haka kuma idan mukaga Ramzin ع a cikin Shadibiyya To Ramzi ne dake Nuni Ga Riwayar Hafs
والله أعلم
Za a Iya cewa QIRA'AR ASIM itace Qira'ar da tafi Kowace Qira'a Fice a duniya A wannan Zamani namu
Musamman ma Riwayar Hafs itace Riwaya Mafi Shahara a duniya a wannan Zamanin
5- KALMOMINDA QIRA'AR ASIM TA SABAWA DUKKAN QIRA'O'I WURIN KARANTASU (انفرادت قراءة عاصم)
Kowace Qira'a Tanada Wasu kalmomi da ta Sabawa Sauran Qira'o'i a wurin Karantasu.
Sabanin Zai iya Kasancewa Ta Fuskar Wasali ko canja Harafi da wani Harafi koma cire Harafin Gaba daya
Ga Kalmomin da Qira'ar Asim ta sabawa Sauran Qira'o'i
Zan kawo Kalmominda Riwayoyinshi biyu sukayi ittifaqi
Bazan kawo wadda daya ke karantawa banda daya ba
Saidai Abun Lura anan Shine Kalmar da nayiwa wasali ita nike nufin an saba gareta Kuma yadda nayi wasalin hakanan yake karantawa duk da cewa Zaa iya samun kalma mai banbancin Qira'at fiye da biyu To yadda nayi wasali haka nike nufin Asim ya sabawa sauran
ASIM Bayada انفرادت Da yawa Kamar Sauran Qira'o'i
Ga kalmomin
1- من ذا الذي يقرض الله قرضا حسنا فَيُضَــٰـــعِـفَهُ له
Surar Baqarah da Hadid
2- وأن تَصَدَّقُوا خير لكم
Yana Cire Shadda Ga harafin ص sabanin Sauran Qira'o'i suna Karantawa ne تَصَّدَّقُوا
3- إلا أن تكون تِجَــٰــرَةً حَاضِرَةً
Saura Suna Karantawa ne
تِجَــٰــرَةٌ حَاضِرَةٌ
4- إن نَّعفُ عن طائفة منكم نُعَذِّبْ طائفةً
Sauran Qira'o'i suna Karantawa ne
إن يُعفَ عن طائفة منكم تُعَذَّبْ طائفةٌ
5- بُشْرًا بين يدي....
Surar A'atof da Furqan da Namli
Yana Karantawa da Harafin ب sabanin Sauran Riwayoyi da suke karantawa da ن duk da cewa Sun Saba Wurin Wasulla
6- يَأْجُوجَ ومَأْجُوجَ
Yana Karantawa da Harafin ءْ daurarre
Sauran Kuma Suna Karantawa ne Da yin Ibdalin Hamzar Zuwa Harafin Madda kamar haka يَاجُوجَ ومَاجُوجَ
7- أو جَذْوَةِِ من النار
Yana Yiwa جَ fat'ha
Dama a wurin Wasalin ج ne riwayoyi suka yi sabani a wannan kalmar Har Gida Uku
جَذْوَةِِ
جِذْوَةِِ
جُذْوَةِِ
8- تُظَــٰـهِرُون منهن أمهتكم
9- أُسْوَةٌ حسنة
Yana Yiwa أُ dwamma A duk Wurare Uku da wannan Kalmar tazo a cikin Qurani
Ahzab da Mumtahanah
Sauran kuma Suna yimata Kas'rah إِسْوَةٌ حسنة
10- وَخَاتَمَ النبيين
Da yiwa تَ fat'ha Sauran kuma suna Yimata Kas'ra ne وَخَاتِمَ
11- الذين يُظَــٰـهِرُون منكم من نسائهم
12- والذين يُظَــٰـهِرُون من نسائهم
13- إذا قيل لكم تفسحوا في المَجَــٰــلِسِ
Da yin fat'haDa kuma Maddar ج
Sauran kuma suna Cire Maddar Kuma Su daure جْ
إذا قيل لكم تفسحوا في المَـجْـلِسِ
14- أو يذكر فَتَنفَعَهُ الذكرى
Yana yiwa harafin عَ fat'ha
Sauran Kuma Suna yimishi Dwamma فَتَنفَعُهُ الذكرى
15- وامرأته حَمَّالَةَ الحطب
Da yiwa ةَ fat'ha
Sauran kuma Suna Yimata Dwamma حَمَّالَةُ الحطب
Wadannan Sune Kalmomin da Qira'ar Asim Da Sabawa Dukan Qira'o'i wurin Karantasu
A nemi Littafan Qira'at Domin neman Karin Bayani Zai iya Yiyuwa akwai Abunda ya kamata Mu saka Bamu sa ba ko kuma Wanda muka rubuta bai kamata mu Rubuta ba
والله أعلم
8- RUFEWA
Anan zamu tsaya sai a taremu a rubutu na gaba inda zamuyi Rubutu akan Riwayar Shu'ubah Daya daga cikin Riwayoyin Asim
Insha Allah
JAN HANKALI
Duk wanda Zaiyi sharing ko Kwafi Na wannan Rubutun nawa To ya yi Sharing Dinshi A yadda Na Rubutashi Kar ya kara komai kuma Kar ya canja komai abar shi yadda nayishi
Duk wanda yakeda Taaliki ko gyara Ko shawara ko Mulahaza akan Wannan Rubutun to ya atuntubeni nizan gyara Da kaina Amma Kar A canja Min rubutu.
Ga lambar da zaa tuntubeni da ita +2348034468543
WANDA YA RUBUTA
Habibu Muhammad Shugaba
+2348034468543
Saturday
15-04-1443
20-11-2021
No comments:
Post a Comment