Monday, 14 March 2022

RUBUTU NA 10: TARIHIN QARI'AI GOMA 10 DA RIWAYOYINSU 20 | تاريخ القراء العشرة ورواتهم

 رِوايةُ السُّوسي

عَن أبِـي عَمرو البَصري
TARIHIN QARI'AI GOMA 10 DA RIWAYOYINSU 20
تاريخ القراء العشرة ورواتهم
RUBUTU NA: 10
Rubutawar
✍Habibu Muhammad shugaba
ABUBUWAN DA KE KARKASHIN WANNAN RUBUTUN
👇👇👇👇👇
1- WANENE AL-IMAM AL-SUSI
2- MALAMAN AL-IMAM AL-SUSI
3- DALIBAN AL-IMAM AL-SUSI
4- BAYANI AKAN USUL NA RIWAYAR AL-IMAM AL-SUSI
1-WANENE AL-IMAM AL-SUSI?
SUNANSHI:- Salih bn ziyad bn Abdullahi bn Isma'il bn Ibrahim bn Al-jarud ibn masrah Al-rustaby.
ALKUNYARSHI:- Abu shua'ib
LAKABINSHI:- Al-susi
Al-imam Al-susi Babban malamin Qur'ani ne da Hadisi da Kuma Nahawu
Jagora ne Shugaban Makaranta Qur'ani a Garin Riqqah( Riqqah Gari ne daya Daga cikin Garuruwan Kasar Sham)
A dan nawa binciken banga inda aka anbaci Rana da kuma Wurinda aka Haifi Al-imam Al-susi ba
Al-imam Al-susi Ya rasu A garin Riqqah A shekara ta 261 Bayan Hijrah Yanada Shekaru kusan 70 wasu kuma sunce Yanada Shekaru Kusan 90 A Rayuwarshi رحمه الله رحمة واسعة
2- MALAMAN AL-IMAM AL-SUSI
Daga Cikin malaman Al-imam Al-susi Da malaman Tarihi suka Anbata akwai
1- Yahya ibn Al-mubarak Al-yazidiyyi
2- Sufyan Ibn uyainah
3- Abdullahi bn numair
4- Asbad bn muhammad
Da sauran malumanshi na Hadisi, Fiqhu da Nahawu da sauran ilmuka
3- DALIBAN AL-IMAM AL-SUSI
Al-imam Al-susi yanada Dalibai da yawa Ga kadan daga Cikin su
👇👇👇👇
1- Dan Al-imam Al-susi mai suna Abul-ma'asum muhd
2- musa bn Jarir Al-nahwi
3- musa bn Jamhur
4- Ahmad bn shuaib Al-nasa'i
5- Ahmad ibn muhammad Al-rifqi
6- ja'afar bn Sulaiman Al-khurasani
7- Al-hussain ibn Aliy Al-khayyad
8- muhammad bn said Al-harrani
9- Aliyu bn muhammad Al-si'idy
10- Aliyu bn Al-hussain Al-riqqi
Da sai Sauran su
4-BAYANI AKAN USUL NA RIWAYAR AL-IMAM AL-SUSI
Abunda ake cewa Usul shine Abubuwan da Riwaya ke Ginuwa akansu musamman Abunda da kaji anyishi kaitsaye zaka iya Fahimtar Riwayar da ake karantawa Misali
👇
= Idgamulkabir Ga Riwayar Susi
= Kamar Sak'tah السَّكْتَة ga riwayar khalaf
= Taglizin Lamun da Tarqiqin Ra'un Ga riwayar Warshu
= Silar HA'UL-KINAYAH Ga Qira'ar ibn kathir
Da dai sauransu
Wadannan dama wasun su su ake kira Usul na Riwayoyi
Riwayar Dury Itace Ake Gabatarwa Akan Riwayar susi A wurin Jerantawa
GA WANI BAYANI MAI MUHIMMANCI DA YA KAMATA MU SANI
👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇
mu sani cewa Duriy da Susiy Basuyi Karatu Kaitsaye (Baki da baki) Ga Abu Amr ba, sunyi karatu ne ga Yahya ibn Al-mubarak Al-yazidiy ( يَحْيَى اليَزِيدي) wanda Imamus-shadibiy yake cewa Game da shi :
= أَفَاضَ عَلى يَحْيَى اليَزِيديِّ سَيْبَهُ
فَأَصْبَحَ بِالعَذْبِ الفُرَاتِ مُعَلَّلا
= أبُو عُمَرَ الدُّوري وَصَالِحُهمْ أبو
شُعَيبٍ هُو السُّوسِيُّ عَنهُ تَقبَّلا
Fassara
= Abu Amr Al-basry ya Zubawa yahyal-yazidiyyi Baiwarshi (iliminshi) yahya ya kasance kosasshe saboda ingantaccen ilimin da ya kwankwada daga Abu Amr.
= Abu umar Ad-dury da kuma salihu mai Alkunya Abu Shu'ai wanda shine Ake kira Susi, Sun karbi Qira'ar Abu Amr a gareshi (يَحْيَى اليَزِيديِّ).
Ma'ana dai Akwai wasida a tsakanin su da Abu Amr
Nayi bayani a rubutu na na farko cewa
Wadanda ake Jinginawa riwayoyi (Masu Riwaya) Sun kasu gida uku
1- akwai wadanda sukayi karatu baki da baki ga QARI'AI da ake jinginawa riwayarsu zuwa garesu kamar
- Qalun da warsh sunyi karatu baki da baki ga Nafi'u
2- Akwai wadanda A tsakaninsu da QARI'AN akwai wasidar Mutun Daya kamar
- Dury da susi Sunyi karatu ga Yahyal-Yazidiyyi shi kuma yahya yayi karatu ga Abu Amr Al-basry
-Kamar Khalaf da khallad Sunyi karatu ga Sulaim shi kuma sulaim Yayi Karatu Ga Hamzah
3- Akwai wadanda akwai fiye da mutun daya a tsakaninsu da QARI'IN DA sukayi riwaya a gareshi kamar
- Bazzi da Qumbul basuyi karatu kai tsaye ga ibn kathir ba Akwai fiye da mutun daya a tsakanin su
Abun da yasa hakan ta faru shine
A lokacin da wannan ilimin na riwayoyi yayi yawa ya fadada riwayoyin sunyi yawa Kasancewar kowane Qari'i yanada dalibai masu dinbin yawa kuma kowane daga cikin su yana jingina riwayar shi zuwaga wannan Qari'in
Sai akayi niyyar Takaita Riwayoyin Akace kowane QARI'I zaa fitar da mutun biyu daga cikin Rawiyanshi (Dalibanshi) Wadanda sukafi kwarewa da kuma tsoron Allah Da tsantseni domin a jingina riwayar shi zuwa garesu
Sai a bincika Idan an samu wanda ya cika sharudan daga cikin Daliban QARI'IN, haka kuwa akayi Zabin Ya fada Ga Duriy da Susi sai aka aka cigaba da jingina Qira'ar Abu Amr Al-basry zuwa garesu, Riwayar su kuma ake jinginata kai tsaye zuwa gareshi (Abu Amr Al-basry) Sabanin asalin Malaminsu ( yahyal-yazidiyyi)
Wannan shine Ma'anar Fadar Shadibiyy
تَخَيرَهم نُقَّادُهُم كلَّ بَارِعٍ
وَلَيسَ عَلى قُرءَانِه مُتَأَكِّلا
Adadin Ayoyin Qur'ani na wannan Riwayar 6214
An sanya adadin Al-madany Al-auwal ( wato tsarin Kirga Ayoyin Al-madany na farko) dama tsarin Qirga Ayoyin Qur'ani akwai
المَدَني الأول
المدني الثاني
Akwai na makkah da sham da kufa da Basrah,
جَعلتُ المَدينِي أَولاً ثم ءاخِرا
وَمَكٍ إلى شَامِِ وكوفٍ إلى بَصْري
Haka Shadibiyy yace a cikin littafinshi ناظمة الزهر في عد آي السور
عد المدني الأول
Shine kafatanin Mutanen basrah ke aiki dashi a mushaf na Abu Amr da ya'akub
Adadin ayoyin su sune Dubu shida da dari biyu da sha hudu 6214
RAMZIN QIRA'AR ABU AMR AL-BASRY
Al-imam As-shadibiy ya yiwa Qira'ar Abu Amr Ramzi ( wato alamar da zai rika yin nuni akan Qira'ar Abu Amr da ita), Ramzin shine
HUDDI (حُطِّي)
wato idan akaga Ramzi na harafin ح a cikin Shadibiyyah to yana nuni ne akan Abu Amr Al-basry
Idan akaga Ramzi na harafin ط yana nufin Duri an Abi Amr
Idan akaga Ramzi na harafin ي to yana nufin Susi
Duk da cewa zai iya kiran kowane daga cikin su da sunanshi ko lakabinshi kai tsaye idan wazanin wakar ya bayar da damar yin haka.
Muna yin rubutun ne a takaice da sai mu bayar da misalin ko wanne daga cikin su, amma idan an koma Shadibiyyah zaa samu misallansu da yawa.
GA ABUBUWAN DA ZAMUYI BAYANINSU NA USUL DIN WANNAN RIWAYAR
1- BISIMILLAH DAKE ZUWA TSAKANIN SURORI BIYU ما جاء بين السورتين
2-AL-IDGAMUL-KABIR (الإدغام الكبير)
3- HA'UL KINAYAH (هَاء الضمير)
4- MADDODI المدود
5- HUKUNCE-HUKUNCEN HAMZA
6- NAQLU DA SAKT النقل والسكت
7- IDGAMI الإدغام
8- IMALAH الإمالة والتقليل
9- WAQAFI AKAN WASU HARUFFA DA SABANIN YADDA AKA RUBUTASU
10- YA'ATUL IDAFAH
11- YA'ATUL-ZAWA'ID
1- BISIMILLAH DAKE ZUWA TSAKANIN SURORI BIYU ما جاء بين السورتين
Al-imam Al-susi yanada Fuska 5 a wurin bisimillah dake Zuwa Tsakanin surori
1- قطع الجميع
Shine Ka kare sura Ka tsaya Kayi bisimillah ka tsa sai ka shiga wata sura
Misali
ولم يكن له كفوا أحد، بسم الله الرحمن الرحيم، قل أعوذ برب الفلق
2- وَصلُ الجميع
Shine ka hade karshen sura da bisimillah da kuma farkon surar da take gaba Ba tareda ka tsaya ba
Misali
ولم يكن له كفوا أحدٌ بِسم الله الرحمن الرحيمِ قُل أعوذ برب الفلق
3- قطع الأول ووصل الثاني بالثالث
Shine Ka kai karshen sura ka tsaya Sai kuma ka hade Bisimillah da farkon surar da take gaba
Misali
ولم يكن له كفوا أحد، بسم الله الرحمن الرحيمِ قُل أعوذ برب الفلق
4- الوصل بلا بسملة
Shine ka sadar da karshen surar da ka gama da surar da take a gaban ta ba tareda kayi bisimillah ba
Misali
ولم يكن له كفوا أحدٌ قُل أعوذ برب الفلق
Sai kuwa Akwai wasu surori guda hudu da suka sabawa Wannan tsarin ana kiransu da suna أربَعُ الزُّهُهر
Sune :-
1- سورة القيامة
2- سورة المطففين
3- سورة البلد
4- سورة الهمزة
A nemi littafan Riwayoyi domin neman Karin Bayani
5- السكت بلا بسملة
Shine idan ka gama Sura sai ka dan tsaya kadan ba tareda kayi nunfashi ba sai ka shiga surar da take gaba ba tareda kayi bisimillah ba
Misali
ولم يكن له كفوا أحدْ (س) قُل أعوذ برب الفلق
Sai kuwa Akwai wasu surori guda hudu da suka sabawa Wannan tsarin ana kiransu da suna أربَعُ الزُّهُهر
Sune :-
1- سورة القيامة
2- سورة المطففين
3- سورة البلد
4- سورة الهمزة
A nemi littafan Riwayoyi domin neman Karin Bayani
2-AL-IDGAMUL-KABIR (الإدغام الكبير)
Abunda Ake kira AL-IDGAMUL-KABIR (الإدغام الكبير) shine A samu Guda biyu masu kama da juna kamar ع da ع ko هـ da هـ ko ك da ك da dai sauran Haruffa irin haka sai a shigar da na farko a cikin na biyu
Misalinsu shine
1- فيهِ هُدى
2- يَعلمُ مَا بين
3- قالَ لَو أَنَّ لـي بكم قوة
4- مَا سَلَكَكُم في سقر
5- مَنَاسِكَكُم
Da dai sauransu
A duk inda aka samu ire-iren wadannan to Al-imam Al-susi yan yin Idgamin harafin farko a cikin na biyu
Sai dai kuma Akwai kalmomin da yakeda Fuska biyu 1- idgami 2- Izhari
Kamar
= وَمَن يَبتَغِ غَير الإسلــم دينا
= يَخْلُ لَكم وجهُ أبيكم
= وَإن يَكُ كَاذِبًا
= ءَالَ لُوطِِ
= idan an samu Kalmar هُوَ wacce هُـ takeda dwamma tana tareda harafin وَ sai kuma kalmar da keda وَ A farkonta sai ta biyo baya kamar
هُوَ وَالذين
هُوَ وَمن يامُرُ
Da sauransu
Susi yanada Fuska biyu a wadannan kalmomin
Abunda mukeso a fahimta anan shine
= Akwai wuraren da yakeyin idgami
= Akwai wurarenda yakeyin izhari
=haka kuma Akwai wurarenda yakeda Fuska biyu
Wannan Takaitaccen rubutun bazai bamu damar rubuta komai da komai ba
A nemi Littafan Qira'at domin neman Karin bayani
Haka kuma Susi yana yin Idgami idan aka samu Haruffa biyu sunyi kusanci a wurin mafita kamar ق da ك,
ج da ت
ع da ح
د ت ط
د ذ
ت ج
د ظ
د ج
ن ر
ن ل
ث س
ة ث
ث ش
Da dai sauransu
Misalinshi shine
1- وَشَهِد شَّاهِد
2- وَمَا نَحْن لَّكَ
3- مِن بَعد ضَّرَّاء
4- يَكَاد زَّيتُها
5- أَخْرَج شَّطئَه
6- إلى ذِى العَرْش سَّبيلا
7- والله أعلم بِما
8- وَوَرِث سُّلَيمن
9- قَال رَّبِّ
10- وَرَثَة جَّنَّة
Akwai kalmomin da yakeda Fuskoki biyu a wurinsu ko idgami ko izhari
👇
* الزكوة ثُمَّ
* التوراة ثُمَّ
* لَقَد جِئتِ شَيئًا
* طَلَّقكنَّ
Abunda mukeso a fahimta anan shine
= Akwai wuraren da yakeyin idgami
= Akwai wurarenda yakeyin izhari
=haka kuma Akwai wurarenda yakeda Fuska biyu
Wannan Takaitaccen rubutun bazai bamu damar rubuta komai da komai ba
A nemi Littafan Qira'at domin neman Karin bayani
Ga wani muhimmin bayani
Mu sani cewa koda a lokacin da zaayi imala ne indai hukuncin ya cika sharadin Idgami to zaayi idgami kuma ayi imala a lokaci daya misali
= والنَّهَارِ لآيت
= من النارِ رَّبنا
Da sauransu zaayi imala kuma ayi idgami
Ha kuma idan aka samu harafin Lin ko madda yazo kafin harafin da Zaayi idgami ln shi a cikin harafin da ke gabanshi Misali
= فِيهِ هُدى
= قَالَ لَوْ أن لي
= قَالَ رب
=قِيلَ لَها
= يَقُولُ لَهُ
To anan Susi yanada Fuska Uku ne
1- idgami tareda yin madda 2
2- idgami tareda yin madda 4
3- idgami tareda yin madda 6
والله أعلم
3- HA'UL KINAYAH (هَاء الضمير )
Ha'ul-kinayah Ha'un ce Da ke nuni akan wani abu daya namiji (المُذَكَّر) Wanda bayanan الغَائِب Kamar عليه da فيه da sauran su
Akwai sabanin riwayoyi a wurare da dama a wurin wannan Ha'un din kamar haka
1- wasu suna Daure ta a wasu wuraren kamar. يُؤَدِّهْ إِلَيك
2- wasu kuma Wasu suna Yimata Wasali ba tare da anja mata Madda Ba (Sila) kamar. يُؤَدِّهِ إِلَيك
3- wasu kuma Suna Yimata Wasali tareda Silar ta wato jan Madda Gareta kamar يُؤَدِّهِ> إِلَيك
A nemi littafan Riwayoyi domin sanin matsayin kowace riwaya a wannan Babin
Al-imam Al-susi yana Karanta wadannan Ha'un din tareda daureta (skun) gasu kamar haka
يُؤَدِّهْ إِلَيك
نُؤْتِهْ منها.
نُوَلِّهْ ما تولى.
نُصْلِهْ جهنم.
وَيَتَّقِّهْ فأولئك هم الفائزون
يَرْضَهْ لكم
Yana Cire madda A wurin
فيهِ مُهَانًا
Sabanin yadda hafs da ibn kathir ke karantawa
Yana mayar da Dwammar Ha'un Ta dawo Kas'ra a wurin wadannan kalmomin
وَمَــــا أَنسَـــٰـــنِيهِ إلا الشيطـن
عَلَيهِ اللهَ
Sabanin yadda Hafs ke karantawa
Haka ma yana kara Harafin Hamzah ء Tareda yin Dwammar Ha'un هُ saidai ba tareda yin sila gareta
👇👇👇👇👇
أَرْجِئْهُ وَأَخَاهُ
4- MADDODI (المُدود)
Maddah Itace Jan Sauti Saboda zuwan Daya daga Cikin Haruffan Madda Guda Uku sune. ا da و da ي
Alif Daurarra Idan Harafin da ke gabaninta kamar قَالَ
Wawun Daurarra idan Harafin da ke Gabaninta yanada Dwwmma ُ kamar نُوح
Ya'un Daurarra idan Harafin da ke Gabaninta yazo da Kas'ra ِ kamar قِيلَ
Al-imam Al-susi yana Ja 4 a wurin Maddul-wajib
المَد الواجب المتصل
Haka kuma yanaja biyu ga Al-maddul-ja'iz المُنفَصِل
ج5- HUKUNCE-HUKUNCEN HAMZA
Wannan babin Kuma munada babi uku 3 da zamuyi bayanin Hamzah dake a cikin wadannan babukan
1- الهمزتين من كلمة
2- الهمزتين من كلمتين
3-الهمز المُفرد
1- الهمزتين من كلمة
Sune Hamza biyu أأ dake Zuwa tare a cikin kalma daya
Misali
ءأنذرتهم ءألد ءأمنتم
Da sauransu
Al-imam Al-susi yana yin Tas'hiln Hamzah ta biyu Tareda yin Id'khali (Abunda Ake cewa Id'khali shine Ayi madda Tsakanin Hamza guda biyu) idan aka samu Hamzah biyu sunzo a cikin kalma daya kamar haka
ءَ ٰاْنذرتهم
ءَ ٰاْلد
ءَ ٰاْمنتم
Saidai kuma Akwai Hamzar da Tas'hili kawa yake yi banda Id'khali
Haka kuma yana Kara harafin Hamza A wadannan Kalmomin Kuma yayi Tas'hilin Hamzah ta biyu
👇
أَينَّ لَنَا لأَجرا Cikin Suratul A'arof
أينَّكم لتأتون الرجال A'arof da Ankabut kissar Annabi Lud
Yana Tashilin Hamzah a wannan kalmar da Ta maimaitu sau uku
ءَاْ ٰمَنتُم لَه قبل أن
ءَاْ ٰمَنتُم به قبل أن
Haka kuma yana yin Tas'hilin
ءاْ ٰلِهَتُنَا خير أم هو
Haka kuma yana sanya Wa wannan Kalmar Madda
مَاجِئْتُم بِهِ ءَآلسِّحْر
Maimakon
مَاجِئْتُم بِهِ السِّحْر
Yadda Hafs da sauran riwayoyi ke karantawa
A nemi Littafan Qira'o'i domin neman Karain Bayani
2- الهمزتين من كلمتين
Sune a samu Hamza tazo A karshen kalma ta farko جآء sai kalmar dake biye da ita ta fara d a harafin Hamzah 👉أمة
(جَاءَ أُمة)
Misali
جَاءَ أُمة
نَشاء أصبناهم
من السماء أو ائتنا
Da sauransu
Al-imam Al-susi Yana Cire Hamza ta Biyu ko ta Farko a duk inda Aka samu Hamza Biyu sunzo cikin kalmomi biyu Kuma Sukayi ittifaqi a wurin wasali MISALI
جَآءَ أَجَلُها
هؤلاءِ إِن كنتم صدقين
أولياءُ أُولئك
Idan muka dubi wadannan misalai uku zamuga cewa Duka Hamzar da ke cikin kowace kalma wasalinsu daya
To susi yana cire Hamza daya Daga cikin wadannan Hamzojin ya bar daya sai ya karanta
جَا أَجَلُها
هؤلا إِن كنتم صدقين
أوليا أُولئك
Saidai malamai sunyi magana Akan Maddar dake wurin sukace
Idan Hamza Ta farko akan cire kamar جَا أَجَلُها to yanada Ja 2 wurin madda Domin ta dawo المد الجائز
Idan kuma Hamza ta biyu aka Cire kamar جَآءَجَلُها to Yanada Ja 4 kawai Saboda Tana nan akan Maddul-wajib
A koma littafai domin neman karin bayanin
Amma idan wasullan wadannan Hamzojin sun banbanta misali ta farko tanada dwamma ءُ ta biyu tanada fataha ءَ Misali
نَشَآءُ أَصَبنَــٰــهم
Ko kuma a samu ta farko tanada kasra ءِ ta biyu tanada fataha ءَ Misali
مِنَ السََّمَآءِ ءَاية
Da dai sauransu
To idan aka samu sun sa6a a wurin wasali To susi yana Yin Tas'hilin Hamza ta biyu kamar haka
👇👇
نَشَآءُ اْصَبنَــٰــهم
مِنَ السََّمَآءِ °َاية
Da sauransu
3- الهَمز المُفرد
Itace Hamzah da take zuwa guda daya a cikin Kalma daya
Misali
يؤمن جِئت هِئتَ. شِئتَ يأت يؤتَونَ يأجوج ومأجوج
Da sauransu
Mazhabar Susi a wannan Babin itace Ibdali (الإِبدَل) shine canja wani abu da wani abu misli يُؤْمِن sai a cire harafin Hamzah a karanta da harafin madda 👉يُومِن
جِيت
هِيتَ.
شِيتَ
يات
يوتَونَ
ياجوج وماجوج
Da sauransu
Al-imam Al-susi yana yin Ibdalin Kaso mai yawa a wannan Babin
Sai dai kuma Akwai wadanda ya togace baya yin ibdalinsu yana karantasu kamar yadda hafs yake karantawa
👇👇👇
* ما ننسخ من ءاية أو نَنسَئْهَا haka Qira'ar shi take
* تَسُؤْهم
*تَسُؤْكُم
* يَشَأْ mai Daurarren Hamzah
* ويُهَيِّئْ لكم
* أم لم يُنَبَّأْ
* أنبِئْهُم
* نَبِّئْنَا
*نَبِّئْهُم
* نَبِّئْ عِبَادى
* أَرجِئْهُ وَأَخَاه haka Qira'ar shi take
* هَيِّئْ لَنا
* اقْرَأْ
* وَتُئْوِي
* التي تُئْوِيه
* أثاثا وَرِئْيًا
* عليهم مُّؤْصَدَة
Gaba daya susi baya ibdalin wadannan Kalmomin
A nemi littafin Qira'at domin neman karin bayani
1- akwa wurinda Hafs ke saka Hamza Shi kuma susi ya Cire kamar
يُضَـــٰـــهُونَ قَول الذين كفروا
الَّــــــٰٓــــــيْ a surar Ahzab da Mujadalah da Dalaq
Yana yin Tashilin wannan hamzar ko kuma yayi ibdalin ta zuwa ya'un ي Daurarra kuma ya ja madda
هَـــــٰـــــاْنتُم
Duk inda tazo yana tashilin wannan hamzar tareda jan Madda 2 ko 4
2- Akwai wurin da hafs Ke Cire Hamza Shi kuma susi ya Saka Hamzar kamar
بَادِئَ الرَّأْيِ. Suratu Hud
وءاخَرُون مُرْجَئُونَ لِأمر الله
تُرْجِئُ مَن تَشَآء منهن
لَا يَأْلِتْكُم من أعمالكم شيئا suratul Hujurat
Idan muka Duba Dakyau zamuga Karara Sun Saba A wadannan Kalmomin da muka kawo
والله أعلم
6- NAQLU DA SAKT النقل والسكت
Abunda ake cewa NAQLU shine Cirato wani abu Zuwa wani abu, Anfi amfani da wannan isdilahin Ga Hamza a wurin maluman Qira'o'i kamar ace
نقل حركة الهمزة إلى الساكن قبلها
Wato cirato Wasalin Hamza a dorashi kan Harafin da ke Gabaninshi kamar ace
قَدَ افْلَحَ
مَنُ اوتِـيَ
Da sauransu
Warshu shine mai wannan Babin
To Al-imam Al-susi yana NAQLU a wuri daya A cikin Qurani mai Girma suratul-Najm
عَادًا الُّاولـى
Idan muka duba zamuga cewa an shafe Hamza
SAKTAH:- Tana nufin Tsayawa dan lokaci kadan a yayin Karatu ba tareda Shedawa (nufashi) ba sannan a wuce kamar كَلَّا بَل رَان sananne a Riwayar Hafs
To Al-imam Al-susi bayada Saktah Ko daya don Haka duk wuraren nan Da hafs keyinta wuri 4 shi bayayi, Ga wuraren kamar Haka
1- ولم يجعَل له عِوَجا(١) قيما لينذر بأسا شديدا
2- من بَعَثَنَا من مرقَدِنا هذا ما وَعَدَ الرحمن
3- وقِيلَ مَن رَاق
4- كلا بل ران على قلوبهم
Baya yin Sak'tar wadannan wuraren
7- AL-IDGAM الإدغام
Shine Shigar da Wani Abu a cikin wani abu
Akwai wasu Haruffa da ke Shiga cikin wasu kuma Riwayoyi sunyi sabani a garesu wato wasu suna Izhari wasu kuma Suna Idgami
Akwai
(إِذْ) ت ز ص د س ج harafi 6
(قَدْ) harafi 8 س ذ ض ظ ز ج ص ش
(تَاء التأنيث) harafi 6 س ث ص ز ظ ج
(هَل) ( بَل) harafi 8 ت ث ظ ز س ن ط ض
Akwai haruffan Da ke shiga cikin wadannan Haruffan musali
إِذْ
Haruffa 6 ke shiga cikin إِذْ sune
ت ز ص د س ج
Kamar
إِذ تَّمشِي أُختُكَ
إِذ سَّمِعْتُمُوهُ
Da sauransu
Al-imam Al-susi yana Yin idgamin wadannan Haruffan gaba daya Saidai wurin هَل da بَل yana Idgamin
هَل تَّرى من فطور
هَل تَّرى لهم من باقية
Kawai
Haka kuma Yana Idgamin wadannan Kalmomin da zan jero
Idgamin Ba'un Mai Jazama (Dauri) Misali
يَغْلِب فَّسَوفَ
Da kuma
عُذتُّ بربـي
فَنَبَذتُّهَاَ
Da kuma
أَخَذتَّ أَخَذتُّم
اتَّخَذتَّ. اتَّخَذتُّم
لَبِثتَّ. لَبِثتُّم
أُورِثتُّمُوهَا بما كنتم
كهيعصٓ ذِّكرُ idan zaa wuce
مَن يُرِدثَّوَابَ
وَيُعَذَِب مَّن يشاء karshen Baqara
وَاصْبِرلِّحكم ربك
Da ire-iren shi
8- IMALAH الإمالة والتقليل
Nan Kuma Zamuyi bayani a takaice Matsayin Al-imam Al-dury akan Wannan Babin
Riwayoyi sun kasu Gida Uku gameda abunda ya shafi Wannan Babin
1- Akwai wadanda Basuda Imala Ko Taq'lili ko daya Kamar Qira'ar Ibn Kathir da Abu Ja'afar
2- Akwai wadanda Imalah Daya Kawai Garesu Kamar, QALOON, warshu, Hafs,
Saidai kuma Warsh Yanada Taq'lili da yawa
3- Akwai masu Imaloli da Yawa kamar, Hamza da Kisa'i, Abu Amr da sauransu
Al-imam Al-susi Yana Daya Daga Cikin Riwayoyi masu imaloli da yawa Saboda haka saidai mu danyi karin Haske Bazamu samu damar Kawo imalolinshi gaba daya ba
Ga Tsarinshi
1- Akwai kalmomin da yakeyin Imala a garesu kamar
أسرى بُشرى
الدارِ النارِ
قَرَارِِ الأبرَارِ
كافِرين الكفرين mai ya'un ي ba mai wawun ba
التورىة
الٓـــــــــر. الٓــــــمٓـــر
Haka kuma yana Imala Ga Harafin أ na Kalmar رَأَى idan an Samu Harafi mai Wasali yazo Gaba kamar رَأَى كَوكبًا Yana yin imala ne ga harafin Hamzah yayi Fataha ga Harafin رَ
Amma idan Harafi mai Dauri ne to bayayi kama
رَأَى القَمر رَأَى الشمسَ
Haka Kuma yana yin imala ga kalma أَعْمَى ta farko wurin fadar Allah.
ومن كان في هذه أَعْمَى فهو في الآخرة أَعْمَى
Yayi Fat'ha ga أَعْمَى ta biyu
Haka kuma yana yin imala ga harafin هَ farkon Suratu Maryam
كهيعص
2- Akwai kalmomin da yakeda Fuskoki biyu Ko fat'ha Ko imala
تَتْرََا
Wurin fadar Allah
ثم أرسلنا رُسْلَنا تَتْرََا
Da kuma
يَـــٰـــبُشرَ ٰيَ هَذَا غُــلـٰم
Ko Imalah ko Taq'lili ko fat'ha
3- akwai wuraren da yakeyin Taq'lili kamar
Idan an samu Kalma Tazo bisa Wazanin فَعْلى kamar
سَلْوى مَرضى.
Ko wazanin فُعْلَى kamar
طُوبَـى مُوسَى
Ko wazanin فِعْلَى kamar
عِيسَى. إِحْدَى
Da dai makamantansu
Haka kuma Akwai wasu surori goma sha daya 11 da yakeyin Taq'lilin Karshen Ayoyin su رءوس الآي idan wurin ya cika Sharadin Taq'lilin ko yayi Imalah idan wurin ya cika Sharadin Imala
Ga surorin kamar haka
طه النجم. المعارج القيامة. النازعات. عبس. الأعلى. الشمس. اليل الضحى. العلق.
Duk kalmar da ake yin imalarta ko Taq'lilinta a halin wucewa da karatu وَصْلًا to ko wurin tsayawa وَقْفًا hakanan zaa karantata
Haka kuma idgami baya hana ayi Imalah kamar yadda bayami ya gabata a wurin bayanin Idgamul-kabir
Haka kuma susi yanada Fuska biyu idan Alif da lam ال sukazo bayan Harafin ر da ya yiwa imalah kamar
قُرَى التي
وَترى الشمس
وَترى الناس
Da sauransu
Yanada Fuska biyu
= Fat'ha
= Imalah
Amma idan Sunan Allah ne ya biyo bayan Harafin ر wacce akayiwa imalah Kamar
👇👇👇👇👇
حتى نَرى الله
فسيرى الله عملكم
Da sauransu
To nan kuma susi yanada Fuska uku
= Fat'ha da kuma Tafkhimin ر da kuma sunan Allah
= Imalah Ga Ra'un ر tareda Yin Tarqiqin sunan Allah
= Imalah Ga Ra'un ر tareda Yin Tafkhimin sunan Allah
A nemi littafan Riwayoyi domin Karin Bayani
9- WAQAFI AKAN WASU HARUFFA
Hukunce-hukuncen tsayawa akan Ha'utta'anith wacce aka rubuta ta a harafin ت (budaddar ت)
Idan muna Bibiyar Qurani zamuga wasu wurare ana rubuta ت budadda a wurin da ya kamata ace an Rubuta ة rufafa Misali
قرت عين لي ولك
وَجَنَّتُ نَعيم
فطرتَ الله
إلا سُنَّتَ الأولين
لسنتِ الله
ومعصيت الرسول
بَقِيَّت الله
كَلِمَتُ رَبك
أولئك يَرجُونَ رَحمَتَ الله
To wannan Babin Shi zai yimuna bayanin Matsayin Susi akan yin Waqafi akan wannan ت
A duk wurin da aka ga irin wannan تTo mu sani Cewa susi yana yin waqafi tare da Daure Ha'un هْ ne Misali
قرت عين لي ولك. 👈 قُرَّهْ. ( idan zaa tsaya )
وَجَنَّتُ نَعيم. 👈 وَجَنَّهْ ( idan zaa tsaya )
فطرتَ الله. 👈 فطرهْ ( idan zaa tsaya )
إلا سُنَّتَ الأولين. . 👈 سُنَّهْ ( idan zaa tsaya )
ومعصيت الرسول 👈 معصيَهْ. ( idan zaa tsaya )
بَقِيَّت الله. 👈 بَقِيَّهْ. ( idan zaa tsaya )
كَلِمَتُ رَبك 👈 كَلِمَهْ ( idan zaa tsaya )
أولئك يَرجُونَ رَحمَتَ الله. 👈رَحمَهْ ( idan zaa tsaya )
PDa dai sauransu
Sai dai a wadannan kalmomi da zan Kawo yana Tsayawa akan تْ ne ba akan هْ ba
👇👇
أفرأيتم اللَّتَ وَالعُزى 👈اللَّتْ( idan zaa tsaya )
مَرضاتِ الله. 👈مَرضاتْ( idan zaa tsaya )
ذَاتَ بَهْجَةٍ 👈ذَاتْ( idan zaa tsaya )
ولاتَ حِينَ مَنَاص. 👈ولاتْ( idan zaa tsaya )
Ya na daure تْ ne a wurin tsayawa akan wadannan kalmomin dama wasunsu da bazamu samu damar kawosu gaba dayaba
والله أعلم
Haka kuma yana waqafi akan harafin Ya'un ي idan Tsayawa ta kama a kan wannan Kalma
كَأَي
Wurin kalma
وكأين da فكأين
Da sauransu a duk inda sukazo
Hakama yana tsayawa akan harafin Alif ا kalam
أَيُّهَ
Guda uku da sukazo Suratul Nur da Zukhruf da Rahman
وتوبوا إلى الله جميعا أَيُّهَ
وقالوا يأَيُّهَ الساحر
سنفرغ لكم أَيُّهَ
Sai ya tsaya a kansu
أَيُّهَا
Da alif na madda
Haka kuma yana tsayawa akan harafin ك idan tsayawa ta kama a kalamr
وَيكَأن الله da وَيكَأنه لا يفلح
Sai ya tsaya
وَيْكْ
والله أعلم
A Nemi Littafin Qira'at domin neman Qarin bayani
10-YA'ATUL IDAFAH الياءات الإضافة
Ya'ul Idafah itace ya'un Ce Da mai magana keyin anfani da ita domin Jingina wani abu zuwa gareshi
Wannan Ya'un Ta kasu Kashi-kashi
Kamar haka:-
= Akwai wace harafin Hamzah أإ mai fataha ko kasra ko Dwamma yake zuwa a gabanta
إِنِّــيٰٓ أَعلَم
إِنِّــيٰٓ أُرِيد
دُعَآءِىٰٓ إلا فرارا
= Akwai kuma wacce lamu-Al ( لام ال. التعريف ) ke zuwa a gabanta kamar haka
- لا ينال عَهدِى الظلمين
- عبادى الصلحون
- إنما حرم ربـى الفواحش
Da dai sauransu
= Akwai kuma wacce Hamzatu-waslin (الهَمزَةُ الوَصل) ke zuwa Gabanta kamar
- إنـى اْصطفَيتُك على الناس
- إن قومى اتخذوا
- يأتـى من بعدى اْسمه أحمد
= Akwai kuma wacce Haruffa ke zuwa a gabanta ba Hamzah أ ko Lamu-Al ba Misali
- أين شركآءِى قالوا
- من وراءِى وكانت امرأتي عاقرا
- لكم دينكم ولى دين
- إن أرضِى واسعة
Da sauransu
= A duk Wadannan Sassa Na Ya'atul Idafah akwai wuraren da Susi keyimata Fat'ha Akwai kuma Wuraren da yakeyin Skun (Dauri) Wannan Rubutun Bazai Isa mu Bayyana komai Da komai Ba
Domin neman Bayani A nemi Littafan Da sukayi Bayani Akan Wannan Riwayar Domin neman Karin Bayani
GA WANI MUHIMMIN RUBUTU DA YA SHAFI YA'ATUL IDAFA
👇👇👇👇
Akwai Ya'atul Idafah 212 Dari biyu da sha biyu A cikin Qurani mai Girma
= Wadanda harafin Hamzah أَ mai fat'ha yazo a gabanta 99 ne
= Wadanda harafin Hamzah إِ mai kasra 52 ne
= Wadanda harafin Hamzah أُ mai Dwamma 10 ne
= Wadanda Lam-Al لام التعريف tazo a gabanta 14 ne
= Wadanda Hamzatul-wasli tazo gabansu 7 ne
= Wadanda wasu haruffa na daban sukazo gabansu 30 ne
Wannan shine Takaitaccen jawabi gameda Wannan babin
11- Ya'atuzzawa'id الياءات الزوائد
Ita kuma wannan Itama ya'un ce da Asalinta ba arubuce take ba a cikin Qur'ani, Anyi Ilhakinta ne a cikin Mushafi
Qurra'u sunyi sabani a wurin karanta ta Da kuma Waqafi akanta, sun kasu kashi uku
1- Akwai masu karanta ta A kowane irin yanayi ( lokacin tsayawa (WAQAFI) a kanta, ko lokacin wucewa da karatu a kanta) kamar Ibn Kathir
2- Akwai Wadanda basu karantawa da ita A kowane irin yanayi Na karatu ( lokacin tsayawa (WAQAFI) a kanta, ko lokacin wucewa da karatu a kanta) Kamar Hafsu
3- Akwai wadanda ke Tabbatar da ita a lokacin wucewa da Karatu, suna cireta wurin WAQAFI Kamar warsh Da Al-imam Al-dury
Al-imam Al-susi yana Tabbatar da wannan Ya'un ne kawai A lokacin sadar da karatu
Akwai wuraren da yake saka Ya'un din haka kuma Akwai inda baya sakawa
Sai a nemi littafai domin akarin bayani
Ya'atuz-zawa'id Tana zuwa ne a cikin wadannan kalmomin da ire-iren su
👇👇👇👇
إلى الداع
إذا دَعَان
واليل إذا يَسر
=الجَوَار
الجَواب
يناد المناد
Da sauransu
Domin neman Karin Bayani a Bincika cikin littafan da sukayi magana akan Wannan Riwayar.
Anan zamu tsaya sai a taremu a rubutu na gaba inda zaa jimu da wata Qira'ar ta daban insha Allah
JAN HANKALI
👇👇👇👇
Duk wanda Zaiyi sharing ko Kwafi Na wannan Rubutun nawa To ya yi Sharing Dinshi A yadda Na Rubutashi Kar ya kara komai kuma Kar ya canja komai abar shi yadda nayishi
Duk wanda yakeda Taaliki ko gyara Ko shawara ko Mulahaza akan Wannan Rubutun to ya atuntubeni nizan gyara Da kaina Amma Kar A canja Min rubutu.
Ga lambar da zaa tuntubeni da ita +2348034468543
✍️WANDA YA RUBUTA
Habibu Muhammad Shugaba
+2348034468543
Monday
19-02-1443
27-09-2021

No comments:

Post a Comment