رِوايةُ قُنبُل
عَن الإِمَامِ ابن كَثِيرٍ المَكي
TARIHIN QARI'AI GOMA 10 DA RIWAYOYINSU 20
تاريخ القراء العشرة ورواتهم
RUBUTU NA: ![7️⃣](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/t34/1/16/37_20e3.png)
![7️⃣](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/t34/1/16/37_20e3.png)
Rubutawar
![✍](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/te2/1/16/270d.png)
ABUBUWAN DA KE KARKASHIN WANNAN RUBUTUN
![👇](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/t4f/1/16/1f447.png)

ABUBUWAN DA WANNAN RUBUTUN YA KUNSA
1- WANENE AL-IMAM QUMBUL
2- SUWAYE MALUMAN AL-IMAM QUMBUL
3- SUWAYE DALIBAN AL-IMAM QUMBUL
4- BAYANI AKAN USUL NA RIWAYAR AL-IMAM QUMBUL
1- WANENE AL-IMAM QUMBUL?
SUNANSHI:- muhammad ibn Abdirrahman ibn khalid ibn muhammad ibn Sa'id ibn jurjah, Bararren bawan Banu Makhzum, Al-makky(mutumin makkah).
LAQABINSHI:- Qumbul
Saidai malamai Sunyi sabani gameda Dalilin yimishi Laqabi da Qumbul:-
= wasu sukace Qumbul shine asalin Sunanshi
= wasu kuma sukace an saka mishi wannan laqabin ne domin ya fito daga cikin family na wani gida dake makkah ana Kiransu "QANABILAH" wato jam'in Qumbul kenan
= wasu kuma sukace saboda shi pharmacist ne wato mai bada magani ko maiyin magani
Hakama ance Kalmar Qumbul a yaren larabci tana nufin:- mutum mai Karfi, haka kuma tana nufin, Yaro mai Babban Kai![🙁](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/tcb/1/16/1f641.png)
![🙁](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/tcb/1/16/1f641.png)
ALKUNYARSHI:- Abu Umar
An haifeshi a shekara ta dari da tis'in da biyar bayan Hijrah 195
Al-imam Qumbul malami ne masanin Qurani, Shine Shugaba Jagora na makaranta Qur'ani a Hijaz A zamaninshi
Mutane sun kasance suna zuwa wurinshi domin suyi karatu daga kasashe Daban-daban na duniya
Qumbul daya daga cikin Riwayoyin ibn kathir Saidai an Gabatar da Bazzy akan shi saboda Bazzy ya fishi sanadi madaukaki zuwa ga ibn kathir
Bazzy da Qumbul basu Sa6a sosai a wurin tsarin karatunsu ba Wannan yasa mafi yawan bayanin da mukayi a wurin Tarihin Bazzy shine zamu dauko mu saka a nan saidai wurinda suka sa6a kuma zamuyi bayani insha Allah
Qumbul ya rasu a shekara ta dari biyu da tis'in da Daya bayan Hijrah 291 yanada shekara 96 A rayuwarshi
رحمه الله رحمة واسعة
2- WASU DAGA CIKIN MALAMAN AL-IMAM QUMBUL
Daga cikinsu akwai
1- Ahmad ibn Aun Annabbal
2- Ahmad ibn muhammad Al-Bazzy (Rawin ibn kathir na farko)
3- Abul hassan Ahmad Alqauwas
Da sauransu
GA WANI BAYANI MAI MUHIMMANCI DA YA KAMATA MU SANI

mu sani cewa Bazzy da Qumbul Basuyi Karatu Kaitsaye (Baki da baki) Ga ibn kathir ba
Akwai mutane a tsakaninsu da ibn kathir
Koda ibn Kathir ya rasu baa ma Haifesu ba
Saboda ibn kathir ya rasu a shekara ta 120
An haifi Bazzi a shekara ta 170
An haifi Qumbul a shekara ta 195
Nayi bayani a rubutu na na farko cewa
Wadanda ake Jinginawa riwayoyi (Masu Riwaya) Sun kasu gida uku
1- akwai wadanda sukayi karatu baki da baki ga QARI'AI da ake jinginawa riwayarsu zuwa garesu kamar
- Qalun da warsh sunyi karatu baki da baki ga Nafi'u
2- Akwai wadanda A tsakaninsu da QARI'AN akwai wasidar Mutun Daya kamar
- Dury da susi Sunyi karatu ga Yahyal Yazidiyyi shi kuma yahya yayi karatu ga Abu amr Al-basry
-Kamar Khalaf da khallad Sunyi karatu ga Sulaim shi kuma sulaim Yayi Karatu Ga Hamzah
3- Akwai wadanda akwai fiye da mutun daya a tsakaninsu da QARI'IN DA sukayi riwaya a gareshi kamar
- Bazzi da Qumbul basuyi karatu kai tsaye ga ibn kathir ba Akwai fiye da mutun daya a tsakanin su
Abun da yasa hakan ta faru shine
A lokacin da wannan ilimin na riwayoyi yayi yawa ya fadada riwayoyin sunyi yawa Kasancewar kowane Qari'i yanada dalibai masu dinbin yawa kuma kowane daga cikin su yana jingina riwayar shi zuwaga wannan Qari'in
Sai akayi niyyar Takaita Riwayoyin Akace kowane QARI'I zaa fitar da mutun biyu daga cikin Rawiyanshi (Dalibanshi) Wadanda sukafi kwarewa da kuma tsoron Allah Da tsantseni domin a jingina riwayar shi zuwa garesu
Sai a bincika Idan an samu wanda ya cika sharudan daga cikin Daliban QARI'IN to الحمد لله idan kuma baa samu ba sai a duba cikin Daliban daliban QARI'IN haka kuwa akayi har Zabin Yazo Ga Bazzi da Qumbul Da ire irensu
Wannan shine Ma'anar Fadar Shadibiyy
تَخَيَّرَهْم نُقَّادُهُم كلَّ بَارِِعٍ
وَلَيسَ عَلى قُرءَانِه مُتَأَكِّلا
Wannan RIWAYA Tanada Ayoyi 6220 Dubu shida da dari biyu da Ashirin
Wannan Adadin Na Ganshi ne a mus'hafin da nike dashi Na QIRA'AR IBN KATHIR 6220
Sai dai kuma Naga wani Adadin da ya sabawa wannan Adadin a wani littafi na QIRA'AR IBN KATHIR
Sunce Adadin Ayoyin Qira'ar ibn kathir sune 6210 dubu shida da dari biyu da goma
Wannan adadin shine Adadin da Abu Amr Addany ya riwaito Da sanadinshi Zuwa ga ibn kathir shi kuma ibn kathir ya Riwaito shi zuwa Ga mujahid ibn Jabr shi kuma mujahid Daga Abdullahi ibn Abbas رضي الله عنهما shi kuma Ibn Abbas Daga Ubayyu Ibn ka'ab رضي الله عنه
Kamar yadda nayi bayani a baya cewa Qumbul baiyi karatu kai tsaye ga ibn kathir ba
Yayi karatu ne Ga Ahmad Alqauwas, shi kuma Ahmad yayi karatu ga Abul-ikhrid', Shi kuma Abul-ikhrid' yayi karatu ga Isma'il da Shibl ibn Abbad, da Isma'il da Shibl sunyi karatu ga ibn kathir Almakky.
3- WASU DAGA CIKIN DALIBAN AL-IMAM QUMBUL
Laakari da cewa Qumbul yayi zamani ne a zamanin neman ilimi da kuma yadashi da kuma bayanin da mukayi cewa mutane daga sassa Daban-daban na duniya suna zuwa Wurin shi domin suyi karatu zamu fahimci cewa Dole Daliban shi su kasance masu dinbin yawa
Ga kadan daga Cikin Daliban shi
1-Abu rabi'ah muhammad ibn Ishaq ( shine Mafi daukaka daga cikin Daliban Qumbul)
2- Ishaq ibn Ahmad Alkhuzaiy
3- muhammad ibn Hamdun
4- Abdullahi ibn Hamdun
5- Abdullahi ibn jubair
6- muhammad ibn Amr ibn Aun
7- Ahmad ibn muhammad ibn Harun
8- Ahmad ibn musa ibn mujahid
9- Abdullahi ibn Ahmad Albalkhiy
10- Abdullahi bn Sauban
Da sauransu
4- BAYANI GAMEDA USUL NA RIWAYAR QUMBUL
Wannan Sashen Kuma insha Allah Zai kunshi bayani Akan wadannan abubuwan da zan jero
![👇](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/t4f/1/16/1f447.png)
![👇](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/t4f/1/16/1f447.png)
![👇](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/t4f/1/16/1f447.png)
![👇](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/t4f/1/16/1f447.png)
![👇](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/t4f/1/16/1f447.png)
1- Bisimillah dake zuwa tsakanin surori
2- mimul-jam'i
3- Ha'ul-kinayah
4- Maddodi
5- Hukunce-hukuncen Hamzah
6- Hukuncin tsayawa akan Ha'utta'anis Wacce Aka Rubuta ta a harafin ت budadda
7- matsayin Bazzy akan Saktah السكتة da Hafs yakeyi a wurare 4 hudu
8- Al'izhar da Al'idgam
9- Ya'atul Idafah
10- Ya'atul zawa'id
1- BISIMILLAH DA KE ZUWA A TSAKANIN SURORI البسملة بين السورتين
Al-imamu Qumbul bai sabawa Hafs ba a wannan Babin wato yadda Hafs yakeda Fuskoki 3 haka shima Qumbul yakeda uku,
Fuskokin da muka sani na hafs Awurin basmalah to sune Qumbul yakeda su
![👇](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/t4f/1/16/1f447.png)
![👇](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/t4f/1/16/1f447.png)
![👇](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/t4f/1/16/1f447.png)
1- قطع الجميع
Shine idan Ka gama sura Ka tsaya, Kayi bisimillah ka tsaya, sai ka shiga wata sura
Misali
ولم يكن له كفؤا أحد، بسم الله الرحمن الرحيم، قل أعوذ برب الفلق
2- وَصلُ الجميع
Shine ka hade karshen sura da bisimillah da kuma farkon surar da take gaba ba tareda ka tsaya ba
Misali
ولم يكن له كفؤا أحدٌ بِسم الله الرحمن الرحيمِ قُل أعوذ برب الفلق
3- قطع الأول، ووصل الثاني بالثالث
Shine idan ka gama sura ka tsaya, Sai kuma ka hade Bisimillah da farkon surar da take gaba ba tare da ka tsaya ba.
Misali
ولم يكن له كفؤا أحد، بسم الله الرحمن الرحيمِ قُل أعوذ برب الفلق
Haka ma tsakanin Anfal da taubah Yanada fuskoki uku kamar sauran Riwayoyi
1- idan ya gama Anfal Zai tsaya sannan ya shiga Taubah ba tareda yayi basmalah ba
2- idan ya gama Anfal zai yi sakt السَّكْت ( wato ya dan tsaya kadan ba tare da yayi numfashi ba) sai ya shiga Tauba kuma bazaiyi basmalah ba
3- Ya hade tsakanin Anfal da tauba ba tareda yayi basmalah ba
والله أعلم
2- mimul-jam'i (مِيمُ الجَمْع)
mimul-jam'i itace Mimun Dake nuni akan Jam'i wato adadin da yake daga uku zuwa sama
Al-imamu Qumbul yana karanta Wannan Mimul-jam'i din da sila (wato ayimata dwamma kuma a ja ta ja biyu) mislali
سراط الذين أنعمت عليهِمُ, غير المغضوب عليهِمُ, ولا الضآلّين
A duk inda mimul-jam'i tazo a cikin Qurani
3- Ha'ul-kinayah هَاءُ الكِنَايَة Ko kuma muce هاء الضمير
Ha'ul-kinayah Ha'un ce Da ke nuni akan wani abu daya namiji (المُذَكَّر) Wanda bayanan الغَائِب Kamar عليه da فيه da sauran su
Al-imamu Qumbul yana karanta Wannan Ha'ul-kinayah din da yin Silar ta ( wato jan ta ja biyu da yimata Kasra ِ a wurin da ake yimata kasra da yimata Dwamma ُ a wurin da ake yimata Dwamma) Misali
فِيهِ>هُدًى للمتقين
اجتَبَـٰـهُ, وَهَد ــٰـهُ, إلى سراط مستقيم
A duk inda tazo cikin Qurani mai Girma
4- Maddodi المُدُود
Al-imamu Qumbul yana Ja 2 biyu Ga maddul ja'iz
Haka kuma yana ja 4 hudu Ga Maddul wajib
5-Hukunce-hukuncen Hamzah
Wannan babin Kuma munada babi uku 3 da zamuyi bayanin Hamzah dake a cikin wadannan babukan
1- الهمزتين من كلمة
2- الهمزتين من كلمتين
3-الهمز المُفرد
Kafin Mu shiga bayaninsu akwai Bukatar muyi bayani akan wasu abubuwa 2 da fadarsu zata maimaitu da yawa a wannan babin
Sune:-
1- Tas'hili التَّسْهِيلُ
2- Ibdali الإبدال
1- Tas'hili التَّسْهِيلُ:- Saukakewa maana saukake Hamza zuwa Harafin Alif ا ko Ya'un ي ko wawun و
2- Ibdali الإبدال :- Canja wani abu da wani abu wato Canja hamza zuwa Harafin Alif ا ko Ya'un ي ko wawun و
A tuntubi laittafan QIRA'AT domin neman Karin bayani
1-الهمزتين من كلمة
Sune Hamza biyu أأ dake Zuwa tare a cikin kalma daya
Misali
ءأنذرتهم ءألد ءأمنتم
Da sauransu
Al-imamu Qumbul yana yin Tas'hiln Hamzah ta biyu idan aka samu Hamzah biyu sunzo a cikin kalma daya kamar haka
ءاْنذرتهم
ءاْلد
ءاْمنتم
2- الهمزتين من كلمتين
Sune a samu Hamza tazo A karshen kalma ta farko جآء sai kalmar dake biye da ita ta fara d a harafin Hamzah
أمة
![👉](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/t51/1/16/1f449.png)
(جَاءَ أُمة)
Misali
جَاءَ أُمة
نَشاء أصبناهم
من السماء أو ائتنا
Da sauransu
Irin wannan Hamzar ta kasu kashi biyu
SASHE NA FARKO
1- Akwai Wadanda wasullansu sukayi Ittifaqi kamar masu fat'ha-fat'ha أَأَ ko kasra-kasra إِإِ ko dwamma-dwamma أُأُ wannan sashin ya kasu kashi Uku
أَأَ إِإِ أُأُ
Ga matsayin Qumbul a wannan babin
= Idan Aka samu Hamzah biyu sunzo cikin Kalmomi Biyu Dukkaninsu sunada Fat'ha-fatha أَأَ Qumbul yanada Fuska biyu a garesu
1- Tas'hilin Hamzah ta biyu Baina-baina kamar Alif Misali
أو جَآءَ اْحَدٌ
جَآءَ اْجَلهم
2- Ibdalin Hamza ta biyu zuwa Alif na madda Tareda Jan maddar ja 2 idan Harafin da ya Biyo bayan Hamzah ta biyu yanada wasali Misali
أو جَآءَ احَدٌ
جَآءَ اجَلهم
Amma idan harafin Yanada Dauri (skun) To yana yin ibdali ne kuma yayi madda ja 6 Misali
تِلقآءَ آصْحــٰــب النار
جآءَ آمْرُنا
= Idan Aka samu Hamzah biyu sunzo cikin Kalmomi Biyu Dukkaninsu sunada kasra-kasra إِإِ suma Qumbul yanada Fuska biyu a garesu
1- Tas'hilin Hamzah ta biyu Baina-baina kamar ya'un ي Misali
من السمآءِ >ِلَـى الأرض
ومن وراءِ >ِسْحــٰــقَ يعقوبُ
2- Ibdalin Hamza ta biyu zuwa ya'un ي ta madda Tareda Jan maddar ja 2 idan Harafin da ya Biyo bayan Hamzah ta biyu yanada wasali Misali
من السمآءِ >لَـى الأرض
Amma idan harafin Yanada Dauri (skun) To yana yin ibdali ne kuma yayi madda ja 6 Misali
ومن وراءِ >ٓسْحــٰــقَ يعقوبُ
= Idan Aka samu Hamzah biyu sunzo cikin Kalmomi Biyu Dukkaninsu sunada Dwamm-dwamma أُأُ suma Qumbul yanada Fuska biyu a garesu
1- Tas'hilin Hamzah ta biyu Baina-baina zuwa harafin wauwun و Misali
من دونه أولياءُ اُْولئك
2- Ibdalin Hamza ta biyu zuwa harafin Wawun و ta madda Tareda Jan maddar ja 2 Misali
من دونه أولياءُ اولئك
Misali daya ne kawai a wurin Hamzah biyu masu madda kuma shine wannan babu wani a cikin Qurani saishi
SASHE NA BIYU
(2) - Akwai Wadanda Wasullansu suka Saba kamar a samu ta farko da Dwamma ta byu da
Fat'ha irin نَشَآءُ أَصبنَــٰــهم ko ta farko kasra ta biyu fat'ha irin من السماءِ أَوِ ائتنا
Da ire-iren su
Wannan sashen ya kasu kashi Biyar
= a samu ta farko da fat'ha أَ ta biyu da kasra إِ Misali
عن أشيآءَ إِن تبد لكم
Qumbul yana Tas'hilin ta kamar ya'un ي
= Ta farko mai fat'ha أَ ta biyu mai dwamma أُ misali
كل ما جاءَ أُمَّة
Wannan kuma Qumbul yana Tas'hilin ta biyu kamar wawun و
= Hamzah ta farko tazo da Dwamma أُ ta biyu tazo da fat'ha أَ Misali
أن لو نَشاءُ أَصبنـٰـهم
Yana Ibdalin wannan kamar Wawun و
= Ta farko tazo da Dwamma أُ ta biyu tazo da Kasra إِ misali
يهدي من يشاءُ إِلى سراط مستقيم
Wannan yanada fuska biyu
- Tas'hili Zuwa ya'unي
- ibdali zuwa Wawun و
A nemi littafan Qira'o'i domin neman karin Bayani
والله أعلم
3- الهَمز المُفرد
Itace Hamzah da take zuwa guda daya a cikin Kalma daya
Misali
يؤمن جِئت هِئتَ شِئتَ يأت يؤتَونَ يأجوج ومأجوج
Da sauransu
Al-imamu Qumbul Yana Tare da Hafs a wannan babin yadda Hafs yake karantasu haka shima yake karantawa
Sai dai ya sa6awa Hafs A wadannan kalmomin
يأجوج ومأجوج مُؤصَدَة
Qumbul yana yin Ibdalin wannan hamzar
ta dawo Harafin Madda
![👇](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/t4f/1/16/1f447.png)
![👇](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/t4f/1/16/1f447.png)
ياجوج وماجوج مُوصَدَة
Amma idan ba a wadannan Kalmomin ba to suna tareda Hafs
Sai dai kuma a wadannan Kalmomin Qumbul yana saka harafin Hamzah a wurin da Hafs baya sakawa
Duk inda kalmar ضِيَآءً
ضِئَآءً yana saka Hamza
بالسُّوق yana sa Hamza بالسُّئُوقِ والأَعنَاق
فاستوى على سُوقِهِ yana sa Hamza على سُئُوقِهِ
وكشفت عن ساقيها yana sa Hamza سَأْقيها
وَمَنَاةَ الثالثة yana saka Hamza وَمَنَآءَةَ الثالثة
تلك إَذًا قسمة ضِيزى yana sa Hamza تلك إَذًا قسمة ضِئزى
والله أعلم
A nemi littafin da yayi magana akan wannan Riwayar Domin neman karin bayani
6- Hukunce-hukuncen tsayawa akan Ha'utta'anith wacce aka rubuta ta a harafin ت (budaddar ت)
Idan muna Bibiyar Qurani zamuga wasu wurare ana rubuta ت budadda a wurin da ya kamata ace an Rubuta ة rufafa Misali
قرت عين لي ولك
وَجَنَّتُ نَعيم
فطرتَ الله
إلا سُنَّتَ الأولين
لسنتِ الله
ومعصيت الرسول
بَقِيَّت الله
كَلِمَتُ رَبك
أولئك يَرجُونَ رَحمَتَ الله
To wannan Babin Shi zai yimuna bayanin Matsayin Qumbul akan yin Waqafi akan wannan ت
A duk wurin da aka ga irin wannan تTo mu sani Cewa Qumbul yana yin waqafi tare da Daure Ha'un هْ ne Misali
قرت عين لي ولك.
قُرَّهْ. ( idan zaa tsaya )
![👈](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/td0/1/16/1f448.png)
وَجَنَّتُ نَعيم.
وَجَنَّهْ ( idan zaa tsaya )
![👈](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/td0/1/16/1f448.png)
فطرتَ الله.
فطرهْ ( idan zaa tsaya )
![👈](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/td0/1/16/1f448.png)
إلا سُنَّتَ الأولين. .
سُنَّهْ ( idan zaa tsaya )
![👈](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/td0/1/16/1f448.png)
ومعصيت الرسول
معصيَهْ. ( idan zaa tsaya )
![👈](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/td0/1/16/1f448.png)
بَقِيَّت الله.
بَقِيَّهْ. ( idan zaa tsaya )
![👈](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/td0/1/16/1f448.png)
كَلِمَتُ رَبك
كَلِمَهْ ( idan zaa tsaya )
![👈](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/td0/1/16/1f448.png)
أولئك يَرجُونَ رَحمَتَ الله.
رَحمَهْ ( idan zaa tsaya )
![👈](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/td0/1/16/1f448.png)
Da dai sauransu
Sai dai a wadannan kalmomi da zan Kawo yana Tsayawa akan تْ ne ba akan هْ ba
![👇](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/t4f/1/16/1f447.png)
![👇](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/t4f/1/16/1f447.png)
أفرأيتم اللَّتَ وَالعُزى
اللَّتْ( idan zaa tsaya )
![👈](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/td0/1/16/1f448.png)
مَرضاتِ الله.
مَرضاتْ( idan zaa tsaya )
![👈](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/td0/1/16/1f448.png)
ذَاتَ بَهْجَةٍ
ذَاتْ( idan zaa tsaya )
![👈](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/td0/1/16/1f448.png)
ولاتَ حِينَ مَنَاص.
ولاتْ( idan zaa tsaya )
![👈](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/td0/1/16/1f448.png)
Ya na daure تْ ne a wurin tsayawa akan wadannan kalmomin 4
والله أعلم
Haka kuma Al-imamu Qumbul yana tsayawa akan Harafin هْ daurarra a duk inda Kalmar يَــٰــأَبَتِ tazo
Idan zai tsaya a kan wannan kalmar yana Daure هْ ne a duk inda tazo a Qur'ani
Misali
يَــٰــأَبَتِ إني رَأيت أحد عشر كَوكَبًا
يَــٰــأَبَتِ.
. يَــٰــأَبَهْ. ( idan zaa tsaya)
![👈](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/td0/1/16/1f448.png)
7- matsayin Qumbul akan Sak'tah (السكت) da hafs keyi akan wadansu Kalmomi hudu a Alqurani mai Girma
Sak'tah itace Mutun yana Karatu sai ya dan tsaya kadan akan wani Harafi Ba tareda yayi numfashi ba sai ya wuce
Qumbul baya yin Sak'tah ko daya a Qur'ani
A wurare Hudu ma Da hafs yakeyin Sak'tar Qumbul Bayayi Ga wuraren kamar Haka
1- ولم يجعَل له عِوَجا(١) قيما لينذر بأسا شديدا
2- من بَعَثَنَا من مرقَدِنا هذا ما وَعَدَ الرحمن
3- وقِيلَ مَن رَاق
4- كلا بل ران على قلوبهم
Baya yin Sak'tar wadannan wuraren
8- Izhari Da Idgami الإظهار والإدغام
Qumbul yana tare da Hafs A wannan Babin wuraren da hafs yake IZ'HARI to Bazzy shima Yanayi inda Hafs keyin idgami Qumbul ma idgami yakeyi
Hakama a wurin izhari ko idgamin wadannan Haruffan dama wasun su
![👇](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/t4f/1/16/1f447.png)
![👇](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/t4f/1/16/1f447.png)
![👇](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/t4f/1/16/1f447.png)
إذْ، قَد، تاء التأنيث، هَلْ، بَل.
Sai dai a wadannan kalmomin
- يَلهَثْ ذَلك مثل القوم
والله أعلم
9-Ya'atul Idafah الياءات الإضافة
Ya'ul Idafah itace ya'un Ce Da mai magana zaiyi amfani da ita domin jingina wani abu zuwa Gareshi
Wannan Ya'un Ta kasu Kashi-kshi
Kamar haka:-
= Akwai wace harafin Hamzah ِأُأَإ mai fataha ko kasra ko Dwamma yake zuwa a gabanta
إِنِّــيٰٓ أَعلَم
إِنِّــيٰٓ أُرِيد
دُعَآءِىٰٓ إلا فرارا
= Akwai kuma wacce lamu-Al ( لام ال. التعريف ) ke zuwa a gabanta kamar haka
- لا ينال عَهدِى الظلمين
- عبادى الصلحون
- إنما حرم ربـى الفواحش
Da dai sauransu
= Akwai kuma wacce Hamzatu-waslin (الهَمزَةُ الوَصل) ke zuwa Gabanta kamar
- إنـى اْصطفَيتُك على الناس
- إن قومى اتخذوا
- يأتـى من بعدى اْسمه أحمد
= Akwai kuma wacce Haruffa ke zuwa a gabanta ba Hamzah أ ko Lamu-Al ba Misali
- أين شركآءِى قالوا
- من وراءِى وكانت امرأتي عاقرا
- لكم دينكم ولى دين
- إن أرضِى واسعة
Da sauransu
= A duk Wadannan Sassa Na Ya'atul Idafah akwai wuraren da Qumbul keyimata Fat'ha Akwai kuma Wuraren da yakeyin Skun (Dauri) Wannan Rubutun Bazai Isa mu Bayyana komai Da komai Ba
Domin neman Bayani A nemi Littafan Da sukayi Bayani Akan Wannan Riwayar Domin neman Karin Bayani
GA WANI MUHIMMIN RUBUTU DA YA SHAFI YA'ATUL IDAFA
![👇](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/t4f/1/16/1f447.png)
![👇](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/t4f/1/16/1f447.png)
![👇](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/t4f/1/16/1f447.png)
![👇](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/t4f/1/16/1f447.png)
Akwai Ya'atul Idafah 212 Dari biyu da sha biyu A cikin Qurani mai Girma.
= Wadanda harafin Hamzah أَ mai fat'ha yazo a gabanta 99 ne
= Wadanda harafin Hamzah إِ mai kasra 52 ne
= Wadanda harafin Hamzah أُ mai Dwamma 10 ne
= Wadanda Lam-Al لام التعريف tazo a gabanta 14 ne
= Wadanda Hamzatul-wasli tazo gabansu 7 ne
= Wadanda wasu haruffa na daban sukazo gabansu 30 ne
Wannan shine Takaitaccen jawabi gameda Wannan babin
10- Ya'atuzzawa'id الياءات الزوائد
Ita kuma wannan Itama ya'un ce da Asalinta ba arubuce take ba a cikin Qur'ani, Anyi Ilhakinta ne a cikin Mushafi
Qurra'u sunyi sabani a wurin karanta ta, sun kasu kashi uku
1- Akwai masu karanta ta A kowane irin yanayi ( lokacin tsayawa (WAQAFI) a kanta, ko lokacin wucewa da karatu a kanta) kamar Ibn Kathir
2- Akwai Wadanda basu karantawa da ita A kowane irin yanayi Na karatu ( lokacin tsayawa (WAQAFI) a kanta, ko lokacin wucewa da karatu a kanta) Kamar Hafsu
3- Akwai wadanda ke Tabbatar da ita a lokacin wucewa da Karatu, suna cireta wurin WAQAFI Kamar warsh
Qumbul yana Tabbatar da wannan Ya'un din a hali biyu na Karatunshi ( lokacin Wucewa da karatu ko lokacin tsayawa) A Duk inda yake da ita
Ya'atuz-zawa'id Tana zuwa ne a cikin wadannan kalmomin da ire-iren su
![👇](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/t4f/1/16/1f447.png)
![👇](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/t4f/1/16/1f447.png)
![👇](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/t4f/1/16/1f447.png)
![👇](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/t4f/1/16/1f447.png)
إلى الداع
إذا دَعَان
واليل إذا يَسر
الجَوَار
الجَواب
يناد المناد
Da sauransu
Sai dai Yana tabbatar da Ya'atu zawa'id da sukazo a cikin wadannan kalmomin A lokacin da zai tsaya da karatu kawai
Ga kalmomin kamar haka
![👇](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/t4f/1/16/1f447.png)
![👇](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/t4f/1/16/1f447.png)
من وَالٍ.
وَالِ>
![👈](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/td0/1/16/1f448.png)
فما له من هادٍ.
هادِ>
![👈](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/td0/1/16/1f448.png)
مِن واقٍ.
واقِ>
![👈](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/td0/1/16/1f448.png)
ومَا عندَ الله بَاقٍ.
بَاقِ>
![👈](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/td0/1/16/1f448.png)
Domin neman Karin Bayani a Bincika cikin littafan da sukayi magana akan Wannan Riwayar.
Anan zamu tsaya sai a taremu a rubutu na gaba inda zaa jimu da wata Qira'ar ta daban insha Allah
JAN HANKALI
![👇](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/t4f/1/16/1f447.png)
![👇](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/t4f/1/16/1f447.png)
![👇](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/t4f/1/16/1f447.png)
![👇](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/t4f/1/16/1f447.png)
Duk wanda Zaiyi sharing ko Kwafi Na wannan Rubutun nawa To ya yi Sharing Dinshi A yadda Na Rubutashi Kar ya kara komai kuma Kar ya canja komai abar shi yadda nayishi
Duk wanda yakeda Taaliki ko gyara Ko shawara ko Mulahaza akan Wannan Rubutun to ya atuntubeni nizan gyara Da kaina Amma Kar A canja Min rubutu.
Ga lambar da zaa tuntubeni da ita +2348034468543
![✍️](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/te2/1/16/270d.png)
Habibu Muhammad Shugaba
+2348034468543
Thursday
19-12-1442
29-07-2021
No comments:
Post a Comment