TARIHIN QARI'AI GOMA 10 DA RIWAYOYINSU 20
تاريخ القراء العشرة ورواتهم
RUBUTU NA : 3
رِوايةُ قَالُونُ
عَن الإِمَامِ نَافع المَدَني

ABUBUWAN DA KE KARKASHIN WANNAN RUBUTUN





1-Wanene Qalun
2- Malaman Qalun
3- Abubuwan da malamai Suka fada Gameda shi
4-Daliban Qalun
5- Takaitaccen bayani Akan Usul Na Riwayar Qalun( Abubuwan da Aka gina Riwayar akansu)
1- WANENE QALUN
SUNANSHI: Isah ibn Mina ibn Wardan ibn Isah Ibn Abdussamad.
ALKUNYARSHI: Abu musa
LAQABINSHI : Qalun
Al-imam Nafi'u shine Ya Sakawa Qalun Lakabin Qalun Saboda iya karatunshi da kyawon Karatunshi
Kalmar QALUN a Harshen Rumanci tana nufin KYAU (mai kyau)
Kakan Kakan Qalun Mai Suna Abdullahi Yana Daya daga cikin Kamammun Yaki (Bayi) Wadanda aka kamo a yakin da akayi Da RUMAWA a zamanin Khilafar Sayyidina Umar رضي الله عنه , Da akazo Dasu Madina Aka ya siyar Dashi Ga wasu daga Cikin mutanen Madina (Al-ansar)
Haka kuma Ana cewa Qalun Dan matar Nafi'u ne (agola)
An Haifeshi A shekara ta 120 Bayan Hijrah, A lokacin Mulkin Hisham ibn Abdulmalik
Ya fara Karatu a wurin Malaminshi Al-imam Nafi'u a shekara ta 150, a zamanin mulkin Abu ja'afar Al-mansur
Qalun daya ne Daga cikin Daliban Al-imam Nafi'u Kuma yayi Karatu gareshi Baki da baki, kuma Qalun daya ne Daga Cikin Rawiyai 20 na Qur'ani mai Girma Shine ma Na daya a jerin Riwayoyin Qurani mai Girma.
2- MALAMAN QALUN
QALUN YACE :- Na karanta Qira'ar Nafi'u a wurin Nafi'u sau adadi Mai yawa.
Al-imam Nafi'u Shine Babban Malamin Qalun Kuma a wurin Shi ne ya karanci Qira'ar ta Nafi'u Da kuma Qira'ar Abu Ja'afar
Haka kuma Qalun Yayi Karatu A wurin Ibn Wardan Rawin Abu Ja'afar
3- ABUBUWAN DA MALAMAI SUKA FADA GAMEDA SHI (QALUN)
AL-IMAMUL AHWAZY YACE: An haifi Qalun A shekara ta 120 bayan Hijrah,Ya Fara karatu A wurin Malaminshi Nafi'u a shekara ta 150 Bayan Hijrah.
AL-IMAM AN-NAQQASH YACE : An tambayi Qalun Aka ce Dashi: Sau nawa ka karanta Qurani A wurin Nafi'u? Sai Qalun yace Bazai Iya Kirgesu ba Saboda Yawan su, Saidai ni nayi Dalibta a wurin Nafi'u Har Tsawon Shekaru 20.
USMAN IBN KHARZAZ YACE : Qalun Yace Dasu Al-imam Nafi'u shine ya Umarceshi da ya zauna Domin shima a Turomishi Dalibai yana Karantar Dasu Qur'ani (Saboda Yadda yayi Karatu Da yawa a wurin Nafi'u din).
ABU MUHAMMAD AL-BAGDADI YACE: Qalun Ya kasance Bebe (Kurma) Bayajin Magana Amma Idan Ana karanta mishi Qur'ani yana ji Haka kuma Yana Gyarawa dalibanshi Karatu idan Sunyi Kuskure Ta Hanyar Dubin Bakinsu.
AL-IMAM AD-DANI YACE: Qalun Ya rasu A shekara ta 220 bayan Hijrah.
An Haifeshi 120 ya Rasu 220 Kenan yanada Shekara 100 daidai a duniya ya rasu (رحمه الله رحمة واسعة )
4-DALIBAN QALUN
Qalun Yanada Dalibai da yawa da sukayi karatu a wurinshi Zamu Kawo Wasu Daga cikinsu




1- Ibrahim ibn Isah ibn Mina (Danshi kenan)
2-Ahmad ibn Isah ibn Mina (Danshi kenan)
3- usman ibn kharzaz
4-musa ibn ishaq Al-kadi
5- Abdullahi ibn Fulaih
6- Salim ibn Harun
7- Ahmad ibn yazid Al-hulwani
8- Ibrahim ibn muhammad Al-madani
9- mus'ab ibn Ibrahim
10- Abdullahi ibn Isah Al-madani
Da dai Sauransu
5- TAKAITACCEN BAYANI AKAN USUL NA RIWAYAR QALUN ( ABUBUWAN DA AKA GINA RIWAYAR AKANSU )
Riwayar Qalun haka Take kamar Sauran Riwayoyin Qur'ani
Kamar yadda Muka sani Maluman QIRA'AT suna Raba Riwaya zuwa Gida Biyu
1- USUL (Tubalin da Riwaya ke ginuwa akanshi) Kamar Sakt (السكت) a wurin khalaf Da kuma Taglizin Lam (تغليظ اللام)a wurin warsh
Da sauransu
2- FARSH : wannan kuma Zaa iya Samun hadaka( tarayya) Da wasu Riwayoyi a cikinshi, kamar kalmar (مَــٰــلِكِ يوم الدين ) wasu riwayoyi sun karanta Da yiwa mimun Madda مَــٰــلِكِ kamar Hafsu, wasu kuma sun karanta da cire maddarمَلِكِ kamar Qalun.
Da dai sauransu
Kamar dai Sauran Riwayoyi Itama Riwayar Qalun Tanada Sanadi Ingantacce Tun daga Shi Qalun din Har Zuwa ga manzon Allah صلى الله عليه وسلم
Ga Sanadinta Kamar Haka



Qalun Yayi Karatu Ga Nafi'u, Nafi'u yayi karatu ga Abu Ja'afar Al-madani, Abu Ja'afar Al-madani Yayi karatu ga Wadannan Mutaten (tabi'ai)



1- Abdulrahman ibn hurmuz Al-a'araj
2- Shaibatu ibn Nisah Al-Kadi
3- Abu Abdillah Muslim ibn Jundub Alhuzali
4- Abu Rauh Yazid ibn Ruman
Su kuma Wadannan da na Lissafa Sunyi Karatu A wurin
1- Sayyidina Abu Hurairah رضي الله عنه
2- Abdullahi ibn Abbas رضي الله عنهما
3- Abdullahi ibn Ayyash ibn Abi Rabi'ah رضي الله عنه
Su kuma Sunyi Karatu a wurin Ubayyu Ibn Ka'ab رضي الله عنه
Shi kuma Ubayyu yayi Karatu a wurin Manzon Allah صلى الله عليه وسلم
Wannan shine isnadin Riwayar Qalun
Zamuyi bayani akan wasu daga cikin USUL na wannan Riwayar A takaice
GA ABUBUWAN DA ZAMUYI BAYANI AKANSU



1- HUKUNCIN BISIMILLAH DA KE ZUWA A TSAKANIN SURORIN
2- MADDODI
4- HA'UL KINAYAH
5- AL-HAMZA
6- IMALAH
7- IZ'HARI DA IDGAMI
8- YA'ATUL IDAFA
9 YA'ATUZ-ZAWA'ID
1- HUKUNCIN BISIMILLAH DA KE ZUWA A TSAKANIN SURORIN
Fuskokinsu daya da Riwayar Hafs
2- MADDODI
1- WAJIB :Yana Ja 4 a wurin Maddul wajib
2- JA'IZ : Yanada Fuska biyu A wurin Maddul ja'iz
ja 2 ko ja 4

3- MIMUL-JAM'I
Yanada Fuska Biyu a wurin Mimul-jam'i



1- Iskan ( Daure Mimul-jam'i)
2- sila ( Sadar Da Mimul-jam'i)
4- HA'UL KINAYAH
Yana karanta Wadannan Kalmomin Da Yiwa هـ kasra Ba tareda Yin Sila Ba



1- يؤدِّهِ إليك
2- فَأَلقِهِ إليهم
3- نُوَلِّهِ ما تولى
4- وَنُصلِهِ جهنم
5-نُؤتِهِ مِنهَا
6- أَرجِهِ وأخاه
7- وَيَتَّقِهِ فأولئك
8- فِيهِ مُهَانًا
9- ومن يَأتِهِ مؤمنًا yanada Fuska biyu ga wannan kalmar (sila ko rashin yinta)
Wadannan Kalmomin da na kawo guda 8 duka Qalun Yana Karantasu Ba tare da Yin Sila Ga harafin هـ ba na 9 kuma ومن يَأتِهِ مؤمنًا yanada Fuska biyu a gareta Sila ko rashin yinta
Haka kuma Qalun yana Karanta wadannan Kalmomin da yiwa هـ ha'un Kasra

وَمَا أَنسَــٰــنِيهِ إلا الشيطـن
عَليهِ الله
Sauran wurare kuma yana tareda Hafsu
5- AL-HAMZA
1- HAMZUL-MUFRAD أ
2- HAMZATANI MIN KALIMAH أأ
3-HAMZATANI MIN KALIMATAINI أ ء
> IBDALI : a wasu wurare yana karantawa da yin Ibdali مُوصَدَة
> TAS'HILI : a wasu wurare yana karantawa da yin Tas'hili ءاْشفقتم
> TAHQIQI : a wasu wurare yana karantawa da yin Tahqiqi مؤجلا
A koma Cikin littafai Domin neman karin bayani
1- HAMZUL-MUFRAD أ
Itace Hamza daya أ dake zuwa a tsakiyar kalma
Kamar
مُؤصَدَة مؤجلا لئلا
2- HAMZATANI MIN KALIMAH
Sune Hamza biyu أأ dake zuwa a farkon kalma
Kamar
ءأنتم. ءأشفقتم. أألد
3-HAMZATANI MIN KALIMATAINI
Sune a samu hamza أ tazo karshen kalma ta farko, sai kalma ta biyu ta fara da harafin hamza أ
Kamar
(جاء أمة) (من السماء ءاية) (إذا جاء أجلها)
Idan muka duba Kalmar farko جآء ta kare da harafin ء, Kalma ta biyu أمة ta fara da أ
A koma Cikin littafai Domin neman karin bayani
6- IMALAH
A duk Qur'ani Qalun bayada Imala Idan ba a kalma daya ba itace kalmar هَارٍ
على شَفَا جُرُفٍ هَارٍ
Yanada Fuska biyu A wurin kalmar تَوْرَىة ko التَوْرَىة
Yanayin fat'ha a wannan kalmar kamar yadda Hafs ke karantawa, ko yayi Taqlili kamar yadda Warshu ke karantawa
7- IZ'HARI DA IDGAMI
Qalun yayiwa Hafsu muwafaqa a wannan babin na izhari da idgami in ba a wadannan Kalmomin da zamu kawo ba



1- أَخَذتَّ أَخَذتُّم اتَّخَذتَّ. اتَّخَذتُّم
2- اركَبْ مَعَنَا ko kum اركَب مَّعَنَا
( yanada Fuska biyu a gareta IZ'HARI ko IDGAMI )
3- يَلهَث ذَّلك ko kuma يَلهَثْ ذَلك
( yanada Fuska biyu a gareta IZ'HARI ko IDGAMI )
8- YA'ATUL IDAFA
Ita wannan Ya'un Tanada Halaye biyu a wurin Qurra'u Akwai masu yimata Fat'ha
Kamar
إِنِّــيَ أَعلَم
إِنِّــيَ أُرِيد
دُعَآءِىَ إلا فرارا
haka kuma akwai masu Yimata Skun
Kamar
إِنِّــيٰٓ أَعلَم
إِنِّــيٰٓ أُرِيد
دُعَآءىٰٓ إلا فرارا
Shima Qalun Yabi Sahun Sauran Riwayoyi a wannan babin
> Akwai wuraren da yake yimata fat'ha kuma Sune sukafi yawa
> Akwai kuma wuraren da yake yimata skun Sune sukafi karanci
Domin neman Karin bayani a binciki littafan wannan Fannin
9 YA'ATUZ-ZAWA'ID
Ita kuma wannan Itama ya'un ce da Asalinta baarubuce take ba a cikin Qur'ani, kuma Qurra'u sunyi sabani a gareta sunyi sabani kashi uku
1- Akwai masu karanta ta A kowane irin yanayi ( lokacin tsayawa WAQAFI a kanta, ko lokacin wucewa da karatu a kanta) kamar Ibn Kathir
2- Akwai Wadanda basu karantawa da ita A kowane irin yanayi Na karatu ( lokacin tsayawa WAQAFI a kanta, ko lokacin wucewa da karatu a kanta) Kamar Hafsu
3- Akwai wadanda ke Tabbatar da ita a lokacin wucewa da Karatu Kamar Qalun, suna cireta wurin WAQAFI
Aduk wurin da Qalun yake da YA'ATUZ-ZAWA'ID to yana karanta ta ne Kawai idan zai wuce da karatu a mma idan xai tsaya a kan kalmar da take dauke Da ita To kaitsaye yana cireta
Ya'atuz-zawa'id Tana zuwa ne a cikin wadannan kalmomin da ire-iren su




إلى الداع
واليل إذا يَسر
الجَوَار
الجَواب
يناد المناد
Da sauransu
Domin neman Karin Bayani a Bincika cikin littafan wannan Fannin
Anan zan tsaya kasancewar anayin wannan Rubutun ne a takaice duk da cewa yanada matuqar yawa.
JAN HANKALI




Duk wanda Zaiyi sharing ko Kwafi Na wannan Rubutun nawa To ya yi Sharing Dinshi A yadda Na Rubutashi Kar ya kara komai kuma Kar ya canja komai abar shi yadda nayishi
Duk wanda yakeda Taaliki ko gyara Ko shawara ko Mulahaza akan Wannan Rubutun to ya atuntubeni nizan gyara Da kaina Amma Kar A canja Min rubutu.
Ga lambar da zaa tuntubeni da ita +2348034468543

Habibu Muhammad Shugaba
+2348034468543
Tuesday
04-11-1442
15-06-2021
No comments:
Post a Comment