قِرَاءَةُ الإِمَام ابن كَثِيرٍ المَكي
TARIHIN QARI'AI GOMA 10 DA RIWAYOYINSU 20
تاريخ القراء العشرة ورواتهم
RUBUTU NA: ![5️⃣](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/tf6/1/16/35_20e3.png)
![5️⃣](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/tf6/1/16/35_20e3.png)
Rubutawar
![✍](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/te2/1/16/270d.png)
Yau kuma Zamuyi bayani ne akan Qira'ar AL-IMAM IBN KATHIR insha Allah
ABUBUWAN DA KE KARKASHIN WANNAN RUBUTUN
![👇](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/t4f/1/16/1f447.png)
![👇](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/t4f/1/16/1f447.png)
![👇](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/t4f/1/16/1f447.png)
![👇](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/t4f/1/16/1f447.png)
![👇](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/t4f/1/16/1f447.png)
1- WANENE AL-IMAM IBN KATHIR
2- MALUMAN AL-IMAM IBN KATHIR
3- DALIBAN AL-IMAM IBN KATHIR
4- BAYANI AKAN QIRA'AR IBN KATHIR
1- WANENE AL-IMAM IBN KATHIR
SUNANSHI Abdullahi ibn Kathir ibn Amr ibn Abdullahi Ibn Zazan ibn Fairuzan ibn Hurmuz Almakky Addariyyu.
ALKUNYARSHI: Abu Ma'abad
An haifi Al-imam ibn kathir a garin Makkah a shekara ta 45 bayan Hijrah
Sai dai abunda ya Kamata Mu Sani a nan shine
Wannan ibn kathir din ba shine mai Tafsir ba wanda akafi sani mai تفسير ابن كثير
Shi wannan Abdullahi ibn Kathir ne sunanshi an haifeshi a shekara ta 45 bayan Hijrah ya rasu a shekara ta 120 bayan Hijrah
Shi kuma wancen Isma'il ibn kathir an haifeshi Garin Basra a shekara ta 701 bayan Hijrah ya rasu Dimashqa ta Sham a shekara ta 774 bayan Hijrah
Yanada Kyau mu kula
Al-imam ibn kathir ya Hadu da wasu daga Cikin Sahabbban Annabi صلى الله عليه وسلم
Daga cikin wadanda ya hadu dasu akwai
1- Abdullahi ibn Al-zubair رضي الله عنهما
2- Abu Ayyubal ansary رضي الله عنه
3- Anas ibn Malik رضي الله عنه
Haka kuma Ya Hadu da Tabi'ai Kamar
1- Mujahid ibn jabr
2- Dirbas Maula ibn Abbas رضي الله عنهما
3- Abdullahi ibn Assa'ib Al-makhzumy
Al-imam ibn kathir shine Shugaban Makaranta Qur'ani a garin Makkah a zamaninshi
Ibn kathir ya kasance Dogo ne mai Farin Gemu اللحية
Ya kasance mai Fasaha Masanin ilimin Balagah
2- MALAMAN AL-IMAM IBN KATHIR
Tabi'ai sune Malaman ibn kathir Duk da cewa yaga wasu daga cikin sahabbai Kasancewar an haifeshi a lokacin da Hijrah takeda shekaru 45
Daga cikin malaman shi akwai
1- Abdullahi bn Assa'ib shi kuma Abdullahi bn Assa'ib yayi karatu ga Sahabbai biyu
- Sayyidina Ubayyu bn Ka'ab رضي الله عنه
- Sayyidina Umar bn Alkhaddab رضي الله عنه
2- Mujahid ibn Jabr shi kuma mujahid yayi karatu ga Abdullahi ibn Al-sa'ib da kuma Abdullahi ibn Abbas رضي الله عنهما
3- yayi karatu ga Dirbas Maula ibn Abbas رضي الله عنهما Shi kuma Dirbas Yayi Karatu ga Maulanshi Abdullahi ibn Abbas رضي الله عنهما
Shi kuma Abdullahi ibn Abbas Yayi Karatu Ga Ubayyu ibn Ka'ab da Zaid ibn Sabit رضي الله عنهم
Su kuma
1- Umar bn Alkhaddab رضي الله عنه
2- Ubayyu bn Ka'ab رضي الله عنه
3- Zaid ibn Sabit رضي الله عنه
Sunyi Karatu Ga Annabi muhammad صلى الله عليه وسلم
3- DALIBAN AL-IMAM IBN KATHIR
Al-imam ibn kathir yanada Dalibai masu Tarin yawa kuma wadannan daliban jigajigai ne a wajen neman Ilimi da kuma yadashi Duniyar ilimi ta yadda da cewa malamai ne su
Rubutun mu bazai isa mu kawo sunayen su da yawa ba amma ga wasu daga cikin su
1- Isma'il ibn Abdullahi Alqusd
2- Isma'il ibn muslim
4- Hammad ibn Salamah ( masanin Hadisi)
5- Hammad ibn Zaid ( masanin Hadisi)
6- Sulaiman ibn Almugirah
7- Alkhalil ibn Ahmad ( Masanin ilimin Larabci)
8- Shibl ibn Abbad
9- Sadawatu ibn Abdullahi ibn Kathir (danshi)
10- Abdulmalik ibn juraij Almakky
11- Aliyu ibn Alhakam
12- Mudartif ibn Ma'aQil
13- Abu Amr ibn Al-ala' Albasry ( Daya Daga cikin Qurra'u saba'ah)
14- Ibn Abi Mulaikah
15- Sufyan ibn Uyainah (masanin Hadisi)
16- Harun ibn musa
Da dai Sauransu
AL-ASMA'I YACE : Nace da Abu Amr Albasry : Kayi karatu ga ibn kathir? Sai yace : Eh Nayi Khatama ( Sauka) ga ibn Kathir bayan Nayi Sauka Ga mujahid, Ibn kathir ya kasance mafi sanin ilimin larabci fiye da mujahid.
MUJAHID YACE : ibn kathir bai Gushe ba A matsayin imami Jagora a fannin karatun Qurani a garin makkah ba Har lokacin da ya Rasu a shekara ta 120 bayan Hijrah.
SUFYAN IBN UYAINAH YACE: na Halarci Janazar ibn kathir Addary A shekara ta 120 bayan Hijrah
Ibn kathir ya rasu a shekara ta 120 bayan Hijrah
Yanada Shekara 75 a rayuwar shi
رحمه الله رحمة واسعة
4- BAYANI AKAN QIRA'AR IBN KATHIR
Qira'ar ibn Kathir Qira'a ce aingantatta Mutawatirah Har Zuwa Ga Annabi صلى الله عليه وسلم kuma Dayace Daga cikin Qira'o'i 7
Qira'ar ibn kathir haka take Kamar Sauran Qira'o'i Tanada Riwayoyi biyu
- Riwayar Bazzy an ibn kathir
- Riwayar Qumbul an ibn kathir
KAFIN MU SHIGA BAYANI AKAN WANNAN QIRA'AR
GA WANI BAYANI MAI MUHIMMANCI DA YA KAMATA MU SANI
![👇](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/t4f/1/16/1f447.png)
![👇](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/t4f/1/16/1f447.png)
![👇](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/t4f/1/16/1f447.png)
![👇](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/t4f/1/16/1f447.png)
![👇](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/t4f/1/16/1f447.png)
![👇](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/t4f/1/16/1f447.png)
![👇](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/t4f/1/16/1f447.png)
![👇](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/t4f/1/16/1f447.png)
![👇](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/t4f/1/16/1f447.png)
![👇](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/t4f/1/16/1f447.png)
mu sani cewa Bazzy da Qumbul Basuyi Karatu Kaitsaye (Baki da baki) Ga ibn kathir ba
Akwai mutane a tsakaninsu da ibn kathir
Koda ibn Kathir ya rasu baa ma Haifesu ba
Saboda ibn kathir ya rasu a shekara ta 120
An haifi Bazzi a shekara ta 170
An haifi Qumbul a shekara ta 195
Nayi bayani a rubutu na na farko cewa
Wadanda ake Jinginawa riwayoyi (Masu Riwaya) Sun kasu gida uku
1- akwai wadanda sukayi karatu baki da baki ga QARI'AI da ake jinginawa riwayarsu zuwa garesu kamar
Qalun da warsh sunyi karatu baki da baki ga Nafi'u
2- Akwai wadanda A tsakaninsu da QARI'AN akwai wasidar Mutun Daya kamar
- Dury da susi Sunyi karatu ga Yahyal Yazidiyyi shi kuma yahya yayi karatu ga Abu amr
-Kamar Khalaf da khallad Sunyi karatu ga Sulaim shi kuma sulaim Yayi Karatu Ga Hamzah
3- Akwai wadanda akwai fiye da mutun daya a tsakaninsu da QARI'IN DA sukayi riwaya a gareshi kamar Bazzi da Qumbul basuyi karatu kai tsaye ga ibn kathir ba Akwai fiye da mutun daya a tsakanin su
Abun da yasa hakan ta faru shine
A lokacin da wannan ilimin na riwayoyi yayi yawa ya fadada riwayoyin sunyi yawa Kasancewar kowane Qari'i yanada dalibai masu dinbin yawa kuma kowane yana jingina riwayar shi zuwaga wannan Qariin
Sai akayi niyyar Takaita Riwayoyin Akace kowane QARI'I zaa fitar da mutun biyu daga cikin Rawiyanshi (Dalibanshi) Wadanda sukafi kwarewa da kuma tsoron Allah Da tsantseni domin a jingina riwayar shi zuwa garesu
Sai a bincika Idan an samu wanda ya cika sharudan daga cikin Daliban QARI'IN to الحمد لله idan kuma baa samu ba sai a duba cikin Daliban daliban QARI'IN haka kuwa akayi har Zabin Yazo Ga Bazzi da Qumbul Da ire irensu
Wannan shine Maanar Fadar Shadibiyy
تَخَيرَهم نُقَّادُهُم كلَّ بَارِعٍ
وَلَيسَ عَلى قُرءَانِه مُتَأَكِّلا
Wannan QIRA'AR Tanada Ayoyi 6220 Dubu shida da dari biyu da Ashirin
Wannan Adadin Na Ganshi ne a mushafin da nike dashi Na QIRA'AR IBN KATHIR 6220
Sai dai kuma Naga wani Adadin da ya sabawa wannan Adadin a wani littafi na QIRA'AR IBN KATHIR
Sunce Adadin Ayoyin Qira'ar ibn kathir sune 6210 dubu shida da dari biyu da goma
Wannan adadin shine Adadin da Abu Amr Addany ya riwaito Da sanadinshi Zuwa ga ibn kathir shi kuma ibn kathir ya Riwaito shi zuwa Ga mujahid ibn Jabr shi kuma mujahid Daga Abdullahi ibn Abbas رضي الله عنهما shi kuma Ibn Abbas Daga Ubayyu Ibn ka'ab رضي الله عنه
QIRA'AR IBN KATHIR
Zamuyi bayani ne kawai ga kalmomin Da ibn kathir ya kebanta dasu wadanda ya sabawa sauran QIRA'O'I wurin karanta su Sauran Bayani kuma Zamuyi shi a wurin bayani da zamuyi na musamman gameda wadannan riwayoyi nashi (Bazzy da Qumbul) A rubutun da zamuyi na Gaba insha Allah
Yadda Na Rubutasu haka ibn kathir ke karantawa sabanin sauran Qira'o'i
![👇](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/t4f/1/16/1f447.png)
![👇](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/t4f/1/16/1f447.png)
![👇](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/t4f/1/16/1f447.png)
![👇](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/t4f/1/16/1f447.png)
![👇](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/t4f/1/16/1f447.png)
![👇](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/t4f/1/16/1f447.png)
![👇](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/t4f/1/16/1f447.png)
1- وَاللَّذَآ نِّ يأتيانها منكم
Da yin madda wurin ذ da shadda ga ن
2- القُدْس
Da yin Skun ga harafin دْ a wannan kalmar duk inda tazo cikin Qurani
3- قل إن الله قادر على أن يُنزِلَ ءاية
A wannan ayar shi kadai ke karantawa haka يُنزِلَ da cire shadda
4- يجعل صدره ضَيْقًا da kuma ضَيْقًا مقرنين دعوا هنالك
Yana karantasu da cire shadda ga ي tareda daureta
5- فتلقى ءَادَمَ من ربه كَلِمَـٰتٍ
Kamar yadda na rubuta haka yake karantawa ءَادَمَ da kuma كَلِمَـٰتٍ
6- وما ربك بغـٰفل عما يَعْمَلُونَ () أفتطمعون
Yana sa ي wurin يَعْمَلُونَ Wacce daga ita sai أفتطمعون
7- جَبْرِيلَ
Duk ida tazo a Qur'ani kamar haka جَبْرِيلَ
8- إذا سلمتم ما أَتَيْتُم بالمعروف
Da cire madda wurin ءَاتَيْتُم sai ya dawo أَتَيْتُم
9- وما أَتَيْتُم من ربا ليربوا في أموال الناس
Da cire madda wurin ءَاتَيْتُم sai ya dawo أَتَيْتُم
10- أَأن يُؤْتَى أحد مثل ما أوتيتم
Da kara harafin أ a wannan kalmar ( kar mu manta da Tashilin da yakeyi idan an samu hamza biyu a cikin kalma daya kamar haka)
11- وَكَآئِن
A duk inda kalmar وَكَأَيِّن tazo to yana karantata وَكَآئِن da yin maddar ك da musanya ي zuwa ء
12- كأنما يَصْعَدُ في السماء
Da daure ص da cire shadda kamar yadda na rubuta
13- وأعد لهم جنـت تجرى مِن تَحْتِهَا الأنهـر خـلدين أبدا ( سورة التوبة)
Yana kara harafin مِن a wannan ayar yayiwa تِ kasra cikin ayar والسابقون الأولون dake taubah
14- لقد كان في يوسف وإخوته ءَايَتٌ للسائلين
Da cire madda wurin ءَايَــٰتٌ sai ya karanta ءَايَتٌ babu madda
15- وقالت هَيْتُ لك
Da yiwa ه fat'ha da yiwa ت damma
16- وكذلك مكنا ليوسف في الأرض يتبوأ منها حيث نَشَآء
Da sanya ن wurin ي kamar yadda na Rubuta نَشَآء
17- لقالون إنما سُكِرَتْ أبصارنا
Da cire shadda Ga harafin ك
18- قال أبشرتموني على أن مسني الكبر فبم تُبَشِّرُوٓنِّ
Da yin madda ga ر tareda yiwa ن shadda da kuma karsra تُبَشِّرُوٓنِّ
19- ولا تك في ضِيقٍ( سورة النحل ) da kuma ولا تكن في ضِيقٍ (سورة النمل )
Da yin kasra ga ض kamar yadda na rubuta ضِيقٍ
20- إن قتلهم كان خِطَآءً كبيرا
Da yiwa خ kasra da maddar ط kamar yadda na rubuta خِطَآءً
21- قال ما مَكَّنَنِي فيه ربي خير
Da kara harafin ن da kuma cire shadda مَكَّنَنِي
22- أي الفريقين خير مُّقَامًا وأحسن نديا
Yin dwamma ga harafin م kamar yadda na rubuta مُّقَامًا
23- قالوا إن هَذَآنِّ لسـحران
Da yin maddar ذ da kuma shadda ga ن kamar yadda na Rubuta هَذَآنِّ
24- فلا يَخَفْ ظلما
Da cire madda wurin خ kamar yadda na Rubuta يَخَفْ
25- أَلَمْ يرى الذين كفروا أن السموت والأرض كانتا رتقا
Da cire harafin و asalinshi أولم sai ya karanta أَلَمْ
26- هَذَآنِّ خصمان اختصموا في ربهم
Da yin maddar ذ da kuma shadda ga ن kamar yadda na Rubuta هَذَآنِّ
27- والذين هم لأَمَــٰــنَتِهِم وعهدهم راعون (سورة المؤمنون ) da kuma (سورة المعارج)
Da cire madda wurin harafin ن
28- ولا تأخذكم بهما رَأَفَةٌ في دين الله
Da yiwa أ fataha
29- ظُلُمَــٰتٍ بعضها فوق بعض
Da yin kasrataini wurin ت ظُلُمَــٰتٍ
30- وَنُنزِلُ المَلَئكَةَ تنزيلا
Cire wasali ga ن Da yin dwamma ga ل da fatahar ةَ kamar yadda na Rubuta
31- وهو الذى أرسل الرِّيحَ نشرا بين يدي رحمته
Da yin Tauhidi ga kalmar الرِّيحَ kamar yadda na rubuta ta
32- أو لَيَأْتِيَنَّنِي بسلطـن مبين
Da kara harafin ن wurin kalmar لَيَأْتِيَنَّنِي
33- فإنك لا تسمع الموتى ولا يَسْمَعُ الصُّمَ الدعاء
Yana karanta wadannan kalomomin haka kamar yadda na Rubuta su يَسْمَعُ الصُّمَ a cikin suratu Namli
34- قال إني أريد أن أنكحك إحدى ابنتي هَــٰــتَــيٰٓـــنِّ على أن تأجرني ثماني حجج
Da yin Madda wurin harafin ت da kuma yin shadda Ga ن kamar haka هَــٰــتَــيٰٓـــنِّ
35- قَالَ ربي أعلم بمن جاء بالهدى من عنده
Yana cire Harafin و dake farkon wannan ayar وَقَالَ sai ya karanta قَالَ kawai
36- يَــٰــبُــنَـيْ لا تشرك بالله da kuma يَــٰــبُــنَـيْ إنها إن تك مثقال حبة
Yana maranta يَــٰــبُــنَـي din da sukazo a cikin wadannan ayoyin Da daure harafin ي يَــٰــبُــنَـيْ wadannan ayoyin kawai 2 da na rubuta
37- واذكر عَبْدَنَا إبراهيم وإسحــق ويعقوب أرلى الأيدي والأبصـر
Yana karanta kalma عِبَــٰـدَنا da fataha ga ع tareda ciremishi madda da daure ب kamar haka عَبْدَنَا
38- كذلك يُوحَى إليك وإلى الذين من قبلك الله
Da yin fat'ha ga harafin ح kamar haka يُوحَى
39- فيها أنهـٰـر من ماء غير أَسِنٍ
Yana karantawa da cire madda ga harafin أ kamar haka أَسِنٍ
40- والله بصير بما يَعْمَلُونَ
Yana saka ي wurin harafin ت a karshen سورة الحجرات aya ta kashe
41- هذا ما يُوعَدُونَ لكل أواب حفيظ
Yana saka ي wurin harafin ت a wannan kalmar يُوعَدُونَ
42- وَمَنَــوٰٓءَةَ الثالثة الأخرى
Yana kara ء da kuma madda ga wannan kalmar kamar yadda na rubuta ta وَمَنَــوٰٓءَةَ
43- يوم يدع الداع إلى شيء نُّكْرٍ
Shi kadai ke daure Harafin كْ a wannan ayar نُّكْرٍ
44- يرسل عليكما شِوَاظٌ من نار
Shi kadai keyin kasra ga harafin ش a wannan ayar شِوَاظٌ
45- نحن قَدَرْنَا بينكم الموت
Yana cire shadda Ga harafin د a cikin wannan surar Waki'ah قَدَرْنَا
46- تبت يدا أبي لَهْبٍ وتب
Yana daure Harafin ه a wannan Kalmar لَهْبٍ
WADANNAN sune kalmomin da ibn kathir ya sa6awa kowa daga cikin Qurra'u a garesu kar mu manta kalominda nayiwa WASALI su nike nufi kuma yadda na rubutasu
إن شاء الله
Nan Zamu tsaya a wannan rubutun sai Ku Yi kokari ku samu sauran rubutun da mukayi a baya da kuma wadanda zamuyi nan gaba idan Allah ya Kaimu
JAN HANKALI
![👇](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/t4f/1/16/1f447.png)
![👇](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/t4f/1/16/1f447.png)
![👇](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/t4f/1/16/1f447.png)
![👇](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/t4f/1/16/1f447.png)
Duk wanda Zaiyi sharing ko Kwafi Na wannan Rubutun nawa To ya yi Sharing Dinshi A yadda Na Rubutashi Kar ya kara komai kuma Kar ya canja komai abar shi yadda nayishi
Duk wanda yakeda Ta'aliki ko gyara Ko shawara ko Mulahaza akan Wannan Rubutun to ya atuntubeni nizan gyara Da kaina Amma Kar A canja Min rubutu.
Ga lambar da zaa tuntubeni da ita +2348034468543
![✍️](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/te2/1/16/270d.png)
Habibu Muhammad Shugaba
+2348034468543
Monday
17-11-1442
28-06-2021
No comments:
Post a Comment