TARIHIN QARI'AI GOMA 10 DA RIWAYOYINSU 20
تاريخ القراء العشرة ورواتهم
وايةُ وَرشٍ
عَن الإِمَامِ نَافع المَدَني
RUBUTU NA:
![4️⃣](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/td7/1/16/34_20e3.png)
Rubutawar
![✍](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/te2/1/16/270d.png)
ABUBUWAN DA KE KARKASHIN WANNAN RUBUTUN
![👇](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/t4f/1/16/1f447.png)
![👇](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/t4f/1/16/1f447.png)
![👇](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/t4f/1/16/1f447.png)
![👇](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/t4f/1/16/1f447.png)
![👇](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/t4f/1/16/1f447.png)
1-Wanene warsh
2-Daliban warsh
3- Takaitaccen bayani Akan Usul Na Riwayar Warsh ( Abubuwan da Aka gina Riwayar akansu)
1- WANENE WARSH
SUNANSHI:- Usman ibn Sa'id, ibn Abdullahi, ibn Amr, ibn Sulaiman, ibn Ibrahim,
Wasu Kuma Sunce SUNANSHI:- Usman ibn Sa'id Adiyyi ibn Gazwan ibn Dawud ibn Sabiq
LAQABINSHI :- Warsh
ALKUNYARSHI :- Abu Sa'id ko kuma Abul-qasim
Warshu Mutumin Misra Ne
An haifeshi a shekara ta 110 bayan Hijrah a misra
Ya rasu a misra a shekara ta 197 yanada shekara 87 a duniya رحمه الله
Shine shugaban masu Karatun Qur'anida karantar dashi a kasar misra a zamanin shi
A shekara ta 155 bayan Hijrah Warsh ya zo Garin Madinah Domin yayi karatu a wurin Malaminshi Nafi'u
Kuma yayi Saukar Qur'ani a wurin Nafi'u Adadi masu yawa
Ance Al-imam Nafi'u ne ya Yiwa Warshu Lakabi da WARASHAN ( وَرَشَان) ana karantashi da yiwa harafin وَ da رَ da شَ fataha وَرَشَان
Nafi'u Ya kasance idan Zai kirashi yakan ce dashi " zo yakai WARASHAN"
Ko kuma idan Yanaso warshu ya Karanta Qurani sai yace dashi " karanta yakai WARASHAN"
Ko kuma idan Yana nemanshi yace " ina WARASHAN?"
Daga baya sai aka Mayar Dashi WARSH وَرْشُ
Daga baya sunan ya kasance dashi ne aka san Warshu ba asalin Sunanshi (Usman) ba
Sunan Warshu ya kasance suna mafi soyuwa a wurin Warshu Har ya kasance yana Cewa malamina ne yayimin wannan lakabi (Warsh)
Ance Warshu ya kasance yanada Fari (hasken fata) wannan ne yasa Nafi'u ya yimishi Laqabi da Warsh saboda kalmar WARSH Kalma ce da take nuni akan Wani abu da akeyi Da NONO اللبن Sai akayiwa warshu laqabi dashi Saboda Hasken fatar shi
Wasu kuma sunce Warsh ya kasance Kajere( Guntu) bayada tsayi saboda haka yake saka Tufafi Gajeru wadanda har kafafuwanshi (kwaurinsh) suna bayyana Wannan ne Yasa Akayimishi Lakabi Da Warsh
2- DALIBAN WARSH
Warsh yanada Daliban da yawa Zamu kawo wasu daga cikinshu
1- yunus ibn abdul-A'ala
2- Abu ya'akubal Azraq
3- Abu mas'ud Al-aswadullaun
4- Ahmad ibn Salih
5- Dawud ibn Abi Daybab
6- Aburrabi'i Sulaiman ibn Dawud Al-mahdi
7- muhammad ibn Abdullahi ibn yazid Almakky
8- abdussamad ibn Abdulrahman ibn Alqasim
9- Amr ibn Basshar
10- Amir ibn Sa'id Abul-ash'as
Da sauransu
3- TAKAITACCEN BAYANI AKAN RIWAYAR WARSH
Riwayar Warsh Daya ce daga cikin Riwayoyi 20 ingantattu daga cikin Riwayoyin Qurani mai Girma
Kuma Tana daya Daga cikin Riwayoyi 4 da sukafi sauran Riwayoyi karbuwa a duniyar mu ta yanzu
sune:-
1- Riwayar hafs
2- Riwayar Warsh
3-Riwayar Qalun
4- Riwayar Dury an abi Amr
Haka Kuma Riwayar Warsh Riwaya ce ingantatta wacce takeda INGANTACCEN sanadi tun daga Warsh Har zuwa Ga manzo Allah صلى الله عليه وسلم
Ga Isnadin Riwayar Warsh
Wanna RIWAYA ce da warsh ya Riwaito daga malaminshi Nafi'u ibn Abdulrahman ibn Abi nu'aim Almadany, shi kuma Nafi'u yayi karatu Ga Malumanshi :-
1- Abu ja'afar Almadany
2- Abu Dawud Abdulrahman ibn Hurmzu Al-a'araj
3- Shaibah ibn nisah Al-qady
4- Abu Abdullahi muslim ibn jundub Alhuzaly
5- Abu Rauh Yazid ibn Ruman
Su kuma wadannan maluman na Nafi'u su 5 sunyi karatu Ga Sayyidina Abu Hurairah رضي الله عنه da Abdullahi ibn Abbas رضي الله عنهما Da Abdullahi bn Ayyash ibn abi Rabi'ah رضي الله عنه
Su kuma wadannan Sahabbai masu Girma Sunyi Karatu Ga babban Sahabinnan masanin Qur'ani UBAYYU IBN KA'AB رضي الله عنه shi kuma ubayyu yayi karatu Ga Annabi Muhammad صلى الله عليه وسلم
Wanna shine Sanadin Riwayar Warsh
Wannan Riwaya ce da warsh ya Riwaito daga Malaminshi Nafi'u kamar Yadda Bayani ya gabata
Haka kuma Wannan Riwaya tanada Dariqoqi Guda biyu Sanannu mafi Shahara
1- Dariqar yusuf Al-Azraq
2- Dariqar Asbahany
Riwayar Warsh tanada Ayoyi 6214 aya Dubu shida da dari biyu da sha hudu
A lissafin Mushafin Madinah na biyu عدد المدني الأخير
Akwai wasu Abubuwa da warsh ya kebanta Dasu sabanin ga riwayarshi kamar
1- Tarqiqin harafin Ra'un ر idan ta cika wasu sharudda
Kamar
خَيرَ
غَيرَ
شَرَرٍ
Da sauransu
(Domin neman sanin wadannan sharudda to a nemi littafan da sukayi magana Akan riwayar Warsh a duba musamman Babi mai magana akan Ra'at wato hukuncin harafin Ra'un ر)
2- Taglizin harafin Lamun ل idan ya cika wasu sharudda
Kamar
مَطْلَع
ظَلَمُوا
صَلَوٰة
Da sauransu
(Domin neman sanin wadannan sharudda to a nemi littafan da sukayi magana Akan riwayar Warsh a duba musamman Babi mai magana akan Lamat wato hukuncin harafin lamun ل)
3 Da kuma Jan Maddar badal
Kamar
ءامنون
إيمان
أوتوا
Da sauransu
Shima wannan Yanada sharudda wadanda ya kamata ace mutun ya sansu
A duba littafan da sukayi magana akan Riwayar Warsh musamman Babin Da yayi magana Akan Maddodi
ABUBUWAN DA YA KAMATA MU SANI GAMEDA USUL NA RIWAYAR WARSH
1- Hukuncin bisimillah
2- Hukuncin mimul-jam'i
3- Hukuncin Maddodi
4- Hukuncin harafin Hamzah أ ء
5- Hukuncin izhari da idgami
6- Taq'lili Da Imalah
7- hukuncin harafin Ra'un ر
8- hukuncin harafin Lamun ل
9- Ya'atul Idafah
10- Ya'atuzzawa'id
1- HUKUNCIN BISIMILLAH
Warsh yanada Fuska 5 a bisimillah dake Zuwa Tsakanin surori
1- قطع الجميع
Shine Ka kare sura Ka tsaya Kayi bisimillah ka tsa sai ka shiga wata sura
Misali
ولم يكن له كفوا أحد، بسم الله الرحمن الرحيم، قل أعوذ برب الفلق
2- وَصلُ الجميع
Shine ka hade karshen sura da bisimillah da kuma farkon surar da take gaba
Misali
ولم يكن له كفوا أحدٌ بِسم الله الرحمن الرحيمِ قُل أعوذ برب الفلق
3- قطع الأول ووصل الثاني بالثالث
Shine Ka kai karshen sura ka tsaya Sai kuma ka hade Bisimillah da farkon surar da take gaba
Misali
ولم يكن له كفوا أحد، بسم الله الرحمن الرحيمِ قُل أعوذ برب الفلق
4- الوصل بلا بسملة
Shine ka sadar da karshen surar da ka gama da surar da take a gaban ta ba tareda kayi bisimillah ba
Misali
ولم يكن له كفوا أحدٌ قُل أعوذ برب الفلق
Sai kuwa Akwai wasu surori guda hudu da suka sabawa Wannan tsarin ana kiransu da suna أربَعُ الزُّهُهر
Sune :-
1- سورة القيامة
2- سورة المطففين
3- سورة البلد
4- سورة الهمزة
A nemi littafin Riwayar Warsh domin neman Karin Bayani
5- السكت بلا بسملة
Shine idan ka gama Sura sai ka dan tsaya kadan ba tareda kayi nunfashi ba sai ka shiga surar da take gaba ba tareda kayi bisimillah ba
Misali
ولم يكن له كفوا أحدْ (س) قُل أعوذ برب الفلق
Sai kuwa Akwai wasu surori guda hudu da suka sabawa Wannan tsarin ana kiransu da suna أربَعُ الزُّهُهر
Sune :-
1- سورة القيامة
2- سورة المطففين
3- سورة البلد
4- سورة الهمزة
A nemi littafin Riwayar Warsh domin neman Karin Bayani
2- HUKUNCIN MIMUL-JAM'I
Mimul-jam'i م mimun ce da take zuwa a Qurani domin nuni akan Jam'i (abunda ya wuce biyu)
Warshu yana karantawa da yin silar mimul-jam'i idan Aka samu Harafin Hamzah ء yazo a gaban ta
Misali
سواء عليهم ءأنذرتهم
وإذا قيل لهم ءامنون
Da sauransu
Amma idan Harafin Hamzah ء baizo ba to Warsh baya yin silar ta
Misali
صراط الذين أنعمت عليهم غير المغضوب عليهم ولا الضالين
Da sauransu
3 HUKUNCIN MADDODI
Warsh yana ja 6 ga maddul wajib da kuma ja'iz
Haka kuma yana fuska biyu A wurin maddul lin المد اللين wacce takeda harafin hamzah ء a cikinta
Misali
شَيء شَيئا هَيئة
Yana ja 4 ko 6 a wannan maddar
Sai dai akwai kalmomin da aka togaci (aka ware) wadanda baayimusu maddar
A nemi Littafin da yayi magana akan riwayar Warsh domin neman karin bayani
Haka ma yanada fuska uku a wurin Maddul badal
Kamar
ءامنون إيماناً. أوتوا
Da sauransu
Yana ja 2 ko 4 ko 6 ga maddul badal
Sai dai akwai kalmomin da aka togaci (aka ware) wadanda baayimusu maddar
A nemi Littafin da yayi magana akan riwayar Warsh domin neman karin bayani
4- HUKUNCIN HARAFIN HAMZAH ء
Akwai Hamzah kala uku da ya kamata ace munyi magana akansu a wannan babin
Sune
1- الهمزتين من كلمة
2- الهمزتين من كلمتين
3-الهمز المُفرد
1- الهمزتين من كلمة
Sune Hamza biyu dake Zuwa a tare a cikin kalma daya
Misali
ءأنذرتهم ءألد ءأمنتم
Da sauransu
2- الهمزتين من كلمتين
Shine a samu Hamza tazo A karshen kalma ta farko sai kalmar da take a gabanta ta fara da harafin Hamza ء
Misali
جَاءَ أُمة
نَشاء أصبناهم
من السماء أو ائتنا
Da sauransu
3- الهَمز المُفرد
Itace Hamzah da take zuwa guda daya a cikin Kalma
Misali
يؤمن يأت يؤتَونَ يأجوج ومأجوج
Da sauransu
Warsh Yana yin Tas'hili a dukkan wadannan nau'uka uku na wadannan Hamzojin
Ha kuma yanayin Ibdali A wasu daga cikinsu
A nemi littafin da yayi magana akan Riwayar Warsh Domin neman karin bayani
5- HUKUNCIN IZHARI DA IDGAMI
Warsh bai sabawa hafsu ba a wurin izharin nunussakina da tan'wini ko lam Al da sauran tajwidi da muka sani
Inda ya sabawa Hafs shine wuraren da zamu kawo
![👇](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/t4f/1/16/1f447.png)
![👇](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/t4f/1/16/1f447.png)
![👇](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/t4f/1/16/1f447.png)
![👇](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/t4f/1/16/1f447.png)
Duk inda aka samu قَد tazo sai harafin ض ko ظ sunzo a gabanta to warsh yana yin Idgamin harafin د a cikin daga daga cikin wadannan haruffa
Misali
قال لقَد ظَّلمك
فَقَد ضَّل سواء السبيل
Da sauransu
Haka kuma idan aka samu Ta'utta'anis (تاء التأنيث) sai aka samu harafin ظ yazo a gaba to nan ma warsh yana yin idgami
Misali
كانت ظَّالمَةً
Da sauransu
Haka kuma yana idgami ln wadannan kalmomin
أَخَذتَّ أَخَذتُّم اتَّخَذتَّ. اتَّخَذتُّم
Da makamantansu
6- TAQLILI DA IMALAH
Mafi yawan Mutane suna yiwa warshu Gurguwar fahimta a wannan babin
Sai kaji mutum yana karatu da Riwayar Warsh amma sai ya rika yin Imalah a wuraren da ya kamata yayi Taq'lili
Warshu bayada IMALAH in ba a wuri daya ba shine ga harafin ه wurin kalmar طــه a farkon suratu طــه
A nan ne kawai mutun zaiyi Imalah idan yana karatu da Riwayar Warsh
Sauran Duk Taq'lili ne ko shi kuwa yanada ka'idoji da sharuda da ya kamata mu nemi littafin da yayi magana akan Wannan Riwayar domin neman karin Bayani
Wasu kuma suna kiran Taq'lili da sunan IMALAH SUGRA wato Karamar Imalah
7- HUKUNCIN HARAFIN RA'UN ر
Warsh yanada wani hukunci da ya kebanta shikadai a wurin Harafin Ra'un
Shine yimata tarqiqi bayan Tarqiqi da sauran Riwayoyi suke yimata
Shine Tarqiqin harafin Ra'un ر idan ta cika wasu sharudda
Kamar
خَيرَ
غَيرَ
شَرَرٍ
Da sauransu
(Domin neman sanin wadannan sharudda to a nemi littafan da sukayi magana Akan riwayar Warsh a duba musamman Babi mai magana akan Ra'at wato hukuncin harafin Ra'un ر)
8- HUKUNCIN HARAFIN LAMUN ل
Warsh yanada wani hukunci da ya kebanta shikadai a wurin Harafin LAMUN ل
Shine yimishi Taglizi bayan Taglizi da sauran Riwayoyi suke yimata
Shine Taglizin harafin Lamun ل idan ya cika wasu sharudda
Kamar
مَطْلَع
ظَلَمُوا
صَلَوٰة
Da sauransu
(Domin neman sanin wadannan sharudda to a nemi littafan da sukayi magana Akan riwayar Warsh a duba musamman Babi mai magana akan Lamat wato hukuncin harafin lamun ل)
9- YA'ATUL IDAFAH (ياءات الإضافة)
YA'ATUL IDAFA
Ita wannan Ya'un Tanada Halaye biyu a wurin Qurra Akwai masu yimata Fat'ha
Kamar
إِنِّــيَ أَعلَم
إِنِّــيَ أُرِيد
دُعَآءِى إلا فرارا
haka kuma akwai masu Yimata Skun
Kamar
إِنِّــيٰٓ أَعلَم
إِنِّــيٰٓ أُرِيد
دُعَآءِىٰٓ إلا فرارا
Shima warsh Yabi Sahun Sauran Riwayoyi a wannan babin
Akwai wuraren da yake yimata fat'ha kuma Sune sukafi yawa
Akwai kuma wuraren da yake yimata skun Sune sukafi karanci
Domin neman Karin bayani a binciki littafan wannan Fannin
10- YA'ATUZ-ZAWA'ID ياءات الزوائد
Ita kuma wannan Itama ya'un ce da Asalinta baarubuce take ba a cikin Qur'ani, kuma Qurra'u sunyi sabani a gareta sunyi sabani kashi uku
1- Akwai masu karanta ta A kowane irin yanayi ( lokacin tsayawa WAQAFI a kanta, ko lokacin wucewa da karatu a kanta) kamar Ibn Kathir
2- Akwai Wadanda basu karantawa da ita A kowane irin yanayi Na karatu ( lokacin tsayawa WAQAFI a kanta, ko lokacin wucewa da karatu a kanta) Kamar Hafsu
3- Akwai wadanda ke Tabbatar da ita a lokacin wucewa da Karatu Kamar warsh, suna cireta wurin WAQAFI
Aduk wurin da warsh yake da YA'ATUZ-ZAWA'ID to yana karanta ta ne Kawai idan zai wuce da karatu a mma idan xai tsaya a kan kalmar da take dauke Da ita To kaitsaye yana cireta
Ya'atuz-zawa'id Tana zuwa ne a cikin wadannan kalmomin da ire-iren su
![👇](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/t4f/1/16/1f447.png)
![👇](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/t4f/1/16/1f447.png)
![👇](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/t4f/1/16/1f447.png)
![👇](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/t4f/1/16/1f447.png)
إلى الداع
واليل إذا يَسر
الجَوَار
الجَواب
يناد المناد
Da sauransu
Domin neman Karin Bayani a Bincika cikin littafan wannan Fannin
Anan zamu tsaya sai a taremu a rubutu na gaba inda zaa jimu da wata Qira'ar ta daban insha Allah
JAN HANKALI
![👇](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/t4f/1/16/1f447.png)
![👇](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/t4f/1/16/1f447.png)
![👇](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/t4f/1/16/1f447.png)
![👇](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/t4f/1/16/1f447.png)
Duk wanda Zaiyi sharing ko Kwafi Na wannan Rubutun nawa To ya yi Sharing Dinshi A yadda Na Rubutashi Kar ya kara komai kuma Kar ya canja komai abar shi yadda nayishi
Duk wanda yakeda Taaliki ko gyara Ko shawara ko Mulahaza akan Wannan Rubutun to ya atuntubeni nizan gyara Da kaina Amma Kar A canja Min rubutu.
Ga lambar da zaa tuntubeni da ita +2348034468543
![✍️](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/te2/1/16/270d.png)
Habibu Muhammad Shugaba
+2348034468543
Tuesday
11-11-1442
22-06-2021
No comments:
Post a Comment