رِوايةُ ابن ذَكْوَانَ
عَن ابن عَامِر الشََّامِي
TARIHIN QARI'AI GOMA 10 DA RIWAYOYINSU 20
تاريخ القراء العشرة ورواتهم
RUBUTU NA:
![1️⃣](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/t7a/1/16/31_20e3.png)
![3️⃣](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/tb8/1/16/33_20e3.png)
Rubutawar
![✍](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/te2/1/16/270d.png)
Habibu Muhammad shugaba
ABUBUWAN DA KE KARKASHIN WANNAN RUBUTUN
1- WANENE IBN ZAKWAN?
2- MALAMAN IBN ZAKWAN
3- MAGANAR MALAMAI GAMEDA IBN ZAKWAN
4- DALIBAN IBN ZAKWAN
5- BAYANI AKAN USUL NA RIWAYAR IBN ZAKWAN
6- RUFEWA
SUNANSHI: Abdullahi ibn Ahmad ibn Bashir ibn Zakwan
ALKUNYARSHI:- Abu Amr da kuma Abu Muhammad
An haifeshi A ranar Ashura wato 10 ga watan Al-muharram Shekara ta 173 Bayan Hijrah
Ibn Zakwan Babban malamine daga cikin maluman Dimashq a zamaninshi kuma Limamin Masallacin Jumu'ah ne na garin Dimashq, Hujjah ne a fannin Karatun Qurani, SiQah ne a fannin Riwayar Hadisi.
Ibn Zakwan Shine Rawi na biyu daga cikin Ruwat da ibn Amir, Ana Gabatar da Hisham akanshi a wurin Jeranta Riwayoyi
Ya Rasu a shekara ta 242 Bayan Hijrah yanada shekara 69 a duniya
رحمه الله رحمة واسعة
Wadannan sune Wasu daga cikin malaman ibn Zakwan
1- Ayyub bn Tamin
2- Irak ibn khalid
3- Bakiyyah ibn Al-walid
3- MAGANAR MALAMAI GAMEDA IBN ZAKWAN
Abu Hatim Yace:- Ibn Zakwan Sadukun (صَدُوق) ne ( wannan yaren Maluma Jarhi da Ta'adili ne a fannin Ilimin hadisi)
Al-imam Al-zahabi Yace:- Ibn Zakwan Yafi Hisham Ilim Sanin Qur'ani Sosai, Shi kuma Hisham yafi ibn Zakwan Yalwa da fadin Ilimi sosai.
Abu Amr Al-hafiz Yace:- Ibn Zakwan ya yi karatu Ga Kisa'i a lokacin da Kisa'i yazo A garin Sham
Al-naqqash yace:- Ibn Zakwan yace: Na zauna tareda Kisa'i har tsawon Watanni Bakwai, Kuma nayi karatun Qur'ani a gareshi sau da yawa.
Abu Zur'ah yace:- A wurina Babu wanda yafi ibn Zakwan Sanin Qur'ani a kasar Iraqi, Hijaz, Sham, Misra, Khurasan. A zamaninshi.
Ibn Al-jazari yace:- ibn ZAKWAN ya wallafa Littafi mai suna
أقسام القرآن وجوابها، وما يجب على قارئ القرآن عند حركة لسانه.
Daga cikin Daliban Ibn Zakwan Akwai:
1- Ahmad ibn Abdillahi ( Dan Ibn Zakwan ne)
2- Ahmad ibn Anas
3- Abu Zur'ah Abdulrahman bn Amr
4- Muhammad bn Isma'il Al-tirmizi
5- Harun Ibn Musa Al-akhfash
6- Ahmad ibn Yusuf Al-Taglabi
7- Abdullahi bn isah Al-asfahani
8- muhammad bn musa Assuri
9- Sahl ibn Abdillahi Ibn Al-farkhan
10- Ahmad ibn Nasr
Da sauransu
kafin mu shiga bayani akan Usul na Riwayar ibn Zakwan
![👇](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/t4f/1/16/1f447.png)
GA WANI BAYANI MAI MUHIMMANCI DA YA KAMATA MU SANI
Ka Sani Yakai dan uwa mai Karatu
![👉](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/t51/1/16/1f449.png)
Hisham da Ibn Zakwan Basuyi Karatu Kaitsaye (Baki da baki) Ga ibn Amir ba.
Su Daliban-Daliban-Daliban ibn Amir ne Wato Tsakaninsu da ibn Amir Akwai wasidar Mutun biyu
Idan ma Muka Dubi tarihin haihuwarsu zamuga cewa Koda ibn Amir ya rasu Ba'a haifesu ba
Domin kuwa ibn Amir ya Rasu ne a shekara ta 118 Bayan Hijrah
Hisham kuma an haifeshi ne a shekara ta 153 baywn Hijrah
Ibn Zakwan kuma an haifeshi a shekara ta 173 bayan Hijrah
Ga yadda abun yake
YAHAYA AL-ZIMARI:- Shine ya yi karatu ga ibn Amir
Sai wadannan daliban sukayi karatu gareshi (Yahaya)
1- Ayyub ibn Tamim
2- Irak ibn khalid
3- Sadaqatu ibn khalid
4- Suwaid ibn Abdul-aziz
Shi kuma Hisham yayi karatu ga
1- Ayyub ibn Tamim
2- Irak ibn khalid
3- Sadaqatu ibn khalid
4- Suwaid ibn Abdul-aziz
IBN ZAKWAN kuma Ya yi Karatu ga
1- Ayyub ibn Tamim
2- Irak ibn khalid
Wannan Shine Ma'nar Fadar Al-imam As-shadibiyy
هِـشَـامٌ وَعَـبـدُ اللهِ وَهْوَ انتِسَابُه
لِــذَكْـــوَانَ بِـالإِسْــنَــادِ عَـنْـه تَــنَــقَّــلَا
Fassara:-
Rawiyan Ibn Amir sune Hisham Da kuma Abdullahi (wannan Abdullahin) Shine Ake nasabtawa zuwa ga Zakwan (Zakwan daya ne daga cikin Kakannin ibn Zakwan), Hisham da ibn Zakwan sunyi Riwayar Qira'ar ibn Amir ne Da isnadi.
Wadanda ake Jinginawa riwayoyi (Masu Riwaya) Sun kasu gida uku
1- akwai wadanda sukayi karatu baki da baki ga QARI'AI da ake jinginawa riwayarsu zuwa garesu kamar
- Qalun da warsh sunyi karatu baki da baki ga Nafi'u
2- Akwai wadanda A tsakaninsu da QARI'AN akwai wasidar Mutun Daya kamar
- Dury da susi Sunyi karatu ga Yahyal-Yazidiyyi shi kuma yahya yayi karatu ga Abu Amr Al-basry
-Kamar Khalaf da khallad Sunyi karatu ga Sulaim shi kuma sulaim Yayi Karatu Ga Hamzah
3- Akwai wadanda akwai fiye da mutun daya a tsakaninsu da QARI'IN DA sukayi riwaya a gareshi kamar
- Hisham da ibn Zakwan basuyi karatu kai tsaye ga ibn Amir ba Akwai fiye da mutun daya a tsakanin su
Abun da yasa hakan ta faru shine
A lokacin da wannan ilimin na riwayoyi yayi yawa ya fadada riwayoyin sunyi yawa Kasancewar kowane Qari'i yanada dalibai masu dinbin yawa kuma kowane daga cikin su yana jingina riwayar shi zuwaga wannan Qari'in
Sai akayi niyyar Takaita Riwayoyin Akace kowane QARI'I zaa fitar da mutun biyu daga cikin Rawiyanshi (Dalibanshi) Wadanda sukafi kwarewa da kuma tsoron Allah Da tsantseni domin a jingina riwayar shi zuwa garesu
Sai a bincika Idan an samu wanda ya cika sharudan daga cikin Daliban QARI'IN, haka kuwa akayi Zabin Ya fada Ga Hisham da ibn Zakwan sai aka aka cigaba da jingina Qira'ar ibn Amir zuwa garesu, Riwayar su kuma ake jinginata kai tsaye zuwa gareshi (Ibn Amir) Sabanin asalin Malamansu
Wannan shine Ma'anar Fadar Shadibiyy
تَخَيرَهم نُقَّادُهُم كلَّ بَارِعٍ
وَلَيسَ عَلى قُرءَانِه مُتَأَكِّلا
Adadin Ayoyin Qur'ani na wannan QIRA'AR 6226
عَدُّ الشََّامِي
Wato Qirgar Ayoyi bisa Qirgar Sham Shine Akayi Aiki dashi wurin kayyade adadin Ayoyin Qur'anin Qira'ar ibn Amir
Al-imam As-shadibiyy ya sanya Ramzin كَـــلَِـــمْ ya zamo alamar da za'a Gane ibn Amir da ita da kuma Riwayoyin shi biyu Hisham da ibn Zakwan
Ko ince Daya daga cikin Alamomin da zaa ganesu da ita
Ga abunda yake nufi
كَـــلَِـــمْ
1- idan mukaga Ramzin ك a cikin Shadibiyya To Ramzi ne dake Nuni Ga Qira'ar Ibn Amir
2- idan mukaga Ramzin ل a cikin Shadibiyya To Ramzi ne dake Nuni Ga Riwayar Hisham
3- haka kuma idan mukaga Ramzin م a cikin Shadibiyya To Ramzi ne dake Nuni Ga Riwayar ibn Zakwan
Duk da cewa Wani lokacin yana ambatar su da sunayensu ko lakubansu gwargwadon yadda Lalurar waka ta bayar
والله أعلم
5- BAYANI AKAN USUL NA RIWAYAR AL-IMAM IBN ZAKWAN
Malaman Qira'at Suna Kasa Kowace Riwaya zuwa Sashe Biyu Gasu kamar
1- Sashen Usul
2- Sashen Farsh فَرْش
Abunda ake cewa Usul shine Abubuwan da Riwaya ke Ginuwa akansu musamman Abunda da kaji anyishi kaitsaye zaka iya Fahimtar Riwayar da ake karantawa Misali
= Idgamulkabir Ga Riwayar Susi
= Kamar Sak'tah السَّكْتَة ga riwayar khalaf
= Taglizin Lamun da Tarqiqin Ra'un Ga riwayar Warshu
= Silar HA'UL-KINAYAH Ga Qira'ar ibn kathir
Da dai sauransu
Farsh Kuma Shine Bayanin Kalmomin Qur'ani wadanda Qira'o'i sukayi Sabani a wurin karantasu
A cikin Farsh ne Zaayi bayani akan Kalma. Ace Wadannan suna karanta ta kamar haka, wadannan kuma ga yadda suke karantawa
A wannan Babin kuma Zamuyi bayani ne akan wadannan Abubuwan da zamu jero insha Allah
1- BISIMILLAH DAKE ZUWA TSAKANIN SURORI BIYU ما جاء بين السورتين
2- HA'UL KINAYAH ko (هَاء الضمير)
3- MADDODI المُدُود
4- HUKUNCE-HUKUNCEN HAMZA
5- NAQLU DA SAKT النقل والسكت
6- IZ'HARI DA IDGAMI الإظهار والإدغام
7- FAT'HA DA IMALAH الفَتحُ والإمالة
8- YA'ATUL IDAFAH الياءات الإضافة
9- YA'ATUL-ZAWA'ID الياءات الزوائد
Hisham da ibn Zakwan Basu Yi sabani ba sosai a wannan Gabobi da zamuyi Bayani akansu
Saboda haka Mafi yawan bayanan da mukayi a wurin bayanin Riwayar Hisham shi zamuyi
Akwai Babukan da zamu Tsallake basai munyi bayani akansu ba saboda Hisham da Hafs sunyi muwafaqa a cikinsu ko kuma Hisham bayada banbanci sosai da hafs a cikinsu sai a nemi littafan Qira'at domin neman Qarin bayani
1- BISIMILLAH DAKE ZUWA TSAKANIN SURORI BIYU ما جاء بين السورتين
Kamar yadda muka sani cewa a tsakanin Surorin Qur'ani Akwai Bisimillah dake zuwa idan mutun ya gama wata surah zai shiga wata
Tsakanin Anfal da Taubah ne kawai babu basmalah
IBN ZAKWAN yanada Fuska 5 a wurin bisimillah dake Zuwa Tsakanin surori
1- قطع الجميع
Shine Ka kare sura Ka tsaya Kayi bisimillah ka tsaya sai ka shiga wata sura
Misali
ولم يكن له كفوا أحد، بسم الله الرحمن الرحيم، قل أعوذ برب الفلق
2- وَصلُ الجميع
Shine ka hade karshen sura da bisimillah da kuma farkon surar da take gaba Ba tareda ka tsaya ba
Misali
ولم يكن له كفوا أحدٌ بِسم الله الرحمن الرحيمِ قُل أعوذ برب الفلق
3- قطع الأول ووصل الثاني بالثالث
Shine Ka kai karshen sura ka tsaya Sai kuma ka hade Bisimillah da farkon surar da take gaba
Misali
ولم يكن له كفوا أحد، بسم الله الرحمن الرحيمِ قُل أعوذ برب الفلق
4- الوصل بلا بسملة
Shine ka sadar da karshen surar da ka gama da surar da take a gaban ta ba tareda kayi bisimillah ba
Misali
ولم يكن له كفوا أحدٌ قُل أعوذ برب الفلق
Sai kuwa Akwai wasu surori guda hudu da suka sabawa Wannan tsarin ana kiransu da suna أربَعُ الزُّهُهر
Sune :-
1- سورة القيامة
2- سورة المطففين
3- سورة البلد
4- سورة الهمزة
5- السكت بلا بسملة
Shine idan ka gama Sura sai ka dan tsaya kadan ba tareda kayi nunfashi ba sai ka shiga surar da take gaba ba tareda kayi bisimillah ba
Misali
ولم يكن له كفوا أحدْ (س) قُل أعوذ برب الفلق
Sai kuwa Akwai wasu surori guda hudu da suka sabawa Wannan tsarin ana kiransu da suna أربَعُ الزُّهُهر
Sune :-
1- سورة القيامة
2- سورة المطففين
3- سورة البلد
4- سورة الهمزة
Haka kuma A tsakanin Anfal da Taubah Yanada Fuska Uku kamar sauran Riwayoyi a duk wadannan Fuskokin yana yinsu ba tareda Bisimillah ba
1- الوصل بلا بسملة
2- السكت بلا بسملة
3- القَطع بلا بسملة
Haka kuma Wajibi ne a wurin karatun kowace Riwaya Ayi bisimillah idan An gama سورة الناس kuma anaso a sake dauko karatu daga Fatiha
A nemi littafan Riwayoyi domin neman Karin Bayani
2- HA'UL KINAYAH ko (هَاء الضمير)
Ha'ul-kinayah Ha'un ce Da ke nuni akan wani abu Guda daya namiji (المُذَكَّر) Wanda bayanan الغَائِب Kamar عليه da فيه da sauran su
Akwai sabanin riwayoyi a wurare da dama a wurin wannan Ha'un din kamar haka
1- wasu suna Daure ta a wasu wuraren kamar. يُؤَدِّهْ إِلَيك
2- wasu kuma Wasu suna Yimata Wasali ba tare da anja mata Madda Ba (Sila) kamar. يُؤَدِّهِ إِلَيك
3- wasu kuma Suna Yimata Wasali tareda Silar ta wato jan Madda Gareta kamar يُؤَدِّهِ> إِلَيك
A nemi littafan Riwayoyi domin sanin matsayin kowace riwaya a wannan Babin
Ibn Zakwan Yana Karanta wadannan kalmomin Tareda yin Silar Ha'un Kamar yadda Hafs ko warsh ke karanta mafi yawa daga cikinsu
Ga kalmomin kamar haka
يُؤَدِّهِ> إِلَيك
نُؤْتِهِ>منها
نُوَلِّهِ> ما تولى.
نُصْلِهِ> جهنم.
وَيَتَّقِهِ> فأولئك هم الفائزون
فَأَلْقِهِ> إلَيهم
وَمَن يَأْتِهِ> مُؤمِنًا
يَرْضَهُ, لكم
Haka ma yana kara Harafin Hamzah ء Tareda yin Kasrar Ha'un هِ ba tareda yin sila ba
أَرْجِئْهِ وَأَخَاهُ
Yana Cire madda A wurin
فيهِ مُهَانًا
Sabanin yadda hafs da ibn kathir ke karantawa
Yana mayar da Dwammar Ha'un Ta dawo Kas'ra a wurin wadannan kalmomin
وَمَــــا أَنسَـــٰـــنِيهِ إلا الشيطـن
عَلَيهِ اللهَ
Sabanin yadda Hafs ke karantawa
Maddah Itace Jan Sauti Saboda zuwan Daya daga Cikin Haruffan Madda Guda Uku sune. ا da و da ي
Alif Daurarra Idan Harafin da ke gabaninta kamar قَالَ
Wawun Daurarra idan Harafin da ke Gabaninta yanada Dwwmma ُ kamar نُوح
Ya'un Daurarra idan Harafin da ke Gabaninta yazo da Kas'ra ِ kamar قِيلَ
Ibn Zakwan yana yin Ja 4 ne kawai A wurin maddul-munfasil da kuma Muttasil.
4- HUKUNCE-HUKUNCEN HAMZA
Hamzah ء dayace Daga Cikin haruffan Hija'iyyah أب ت ث ج ح خ د zuwa karshe.
Riwayoyi sunyi sabani a wurin karanta ta a cikin wasu kalmomi Saboda yadda takeda Wahalar fada ga wani sashe na Larabawa
Wasu sunayin TAS'HILI a wurin wasu kalmomi
Wasu kuma sukanyi TAH'QIQI
Wasu kuma Ibdali ko Hazafi sukeyi a wurin wasu kalmomin
Wannan babin Kuma munada babi Hudu da zamuyi bayanin Hamzah dake a cikin wadannan babukan
1- الهمزتين من كلمة
2- الإِستِفهَامُ المُكَرَّر
3- الهمزتين من كلمتين
4-الهمز المُفرد
1- الهمزتين من كلمة
Sune Hamza biyu أأ dake Zuwa tare a cikin kalma daya
Misali
ءأنذرتهم ءألد ءأمنتم
Da sauransu
Ibn Zakwan Yana yin Tahqiqin Hamza ne kamar yadda Hafs keyi a wannan Babin
Sai dai kuma Akwai wasu Kalmomi da ibn Zakwan yake Kara Harafin Hamza sabanin Yadda Hafs ke karantawa
yana Kara harafin Hamza A wadannan Kalmomin
أَئنَّ لَنَا لأَجرا Cikin Suratul A'arof
أءنَّكم لتأتون الرجال A'arof kissar Annabi Lud
ءَأ ٰمَنتُم لَه قبل أن
ءَأ ٰمَنتُم به قبل أن
أَأَذْهَبتُم طيباتكم
Wadannan kuma yana yin Tas'hilin Hamza ne
أَاْن كَانَ ذَا مَالِِ
ءاْعْجَـمِـــيٌّ وَعَرَبي
ءاْ ٰلِهَتُنَا خير أم هو
2- الإِستِفهَامُ المُكَرَّر
Akwai wasu kalmomi da sukazo a cikin Ayoyin Qur'ani ana Kiransu الإِستِفهَامُ المُكَرَّر wato tambayar da ta maimai tu
Misalinsu
أَءِذَا كُنا تُرَابًا أءِنا لفي خلق جديد
أَءِذَا كُنا تُرَابًا وَءَابَآؤنا أءِنا لَمُخرَجون
Da sauransu
Idan muka duba zamuga akwai sigar tambaya biyu a cikin wadannan Ayoyin to wannan ne ake cewa الإِستِفهَامُ المُكَرَّر
Ana samun irin wannan الإِستِفهَامُ المُكَرَّر din a wadannan Surorin
سورة الرعد
سورة الإسراء
سورة النمل
سورة العنكبوت
سورة الصافات
سورة الواقعة
سورة النازعات
A duk inda sukazo ibn Zakwan yana karantasu da Sigar Bada labari a Hamzozi biyu na farko (wato yana cire Hamzah daya) sai yace إِذَا ga ta farko بِالإِخْبَار, ya karanta ta biyu da sigar Tambaya بالإِستِفهَام, kamar أَءِنَّا
Misali
إِذَا كُنا تُرَابًا أءِنا لفي خلق جديد
Sai dai a wuri uku ga yadda yake karantawa
سورة النَّمل
Yana karantawa da sigar tambaya a farko ya karanta ta biyu da sigar Bada labari tareda Kara Harafin ن
أَءِذَا كُنا تُرَابًا وَءَابَآؤنا إِنَّنَا لَمُخرَجون
سورة الواقعة
Yana karantawa da sigar Tambaya a dukkanin kalmomin biyu kamar yadda hafs ke karantawa
وكانوا يقولون أَئذَا متنا وكنا تُرَابًا وعظــٰما أءنا لَمَبعوثونَ
سورة النازعات
Yana karantawa da sigar Tambaya a farko ya karanta na biyu da sigar Dada labari
يقولون أءِنا لَمَردودون في الحَافرة() إِذَا كُنا عظــٰما نخرة
Sune a samu Hamza tazo A karshen kalma ta farko جآء sai kalmar dake biye da ita ta fara d a harafin Hamzah
![👉](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/t51/1/16/1f449.png)
أمة
(جَاءَ أُمة)
Misali
جَاءَ أُمة
نَشاء أصبناهم
من السماء أو ائتنا
Da sauransu
Ibn Zakwan Bai sabawa Hafs ba a wannan Babin (yana yin TAHQIQI ne)
4- الهَمز المُفرد
Itace Hamzah da take zuwa guda daya a cikin Kalma daya
Misali
يؤمن جِئت هِئتَ. شِئتَ يأت يؤتَونَ يأجوج ومأجوج
Da sauransu
Mafi yawan wadannan Kalmomin da Hamzah daya ke zuwa a cikinsu ibn Zakwan bai sabawa Hafs a wurin karantasu ba
Sai dai akwai wasu kalmomi da Hafs ke karantasu da Hamzah shi kuma Ibn Zakwan yana Cire Hamzar kamar
يُضَـــٰـــهُونَ قَول الذين كفروا
مُوصَدَةٌ
يَاجُوج وَمَــــاجُوج
Da sauransu
2- Akwai wurin da hafs Ke Cire Hamza Shi kuma ibn Zakwan ya Saka Hamzar kamar
وءاخَرُون مُرْجَئُونَ لِأمر الله
Idan muka Duba Dakyau zamuga Karara Sun Saba A wadannan Kalmomin da muka kawo
والله أعلم
5- NAQLU DA SAKT النقل والسكت
Abunda ake cewa NAQLU shine Cirato wani abu Daga wani wuri Zuwa wani wuri, Anfi amfani da wannan isdilahin Ga Hamza a wurin maluman Qira'o'i kamar ace
نقل حركة الهمزة إلى الساكن قبلها
Wato cirato Wasalin Hamza a dorashi kan Harafin da ke Gabaninshi kamar ace
قَدَ افْلَحَ
مَنُ اوتِـيَ
Da sauransu
Warshu shine mai wannan Babin
SAKTAH:- Tana nufin Tsayawa dan lokaci kadan a yayin Karatu ba tareda Shedawa (nufashi) ba sannan a wuce kamar كَلَّا بَل رَان sananne a Riwayar Hafs
To ibn Zakwan bayada Saktah Ko daya a cikin Qurani don Haka duk wuraren nan Da hafs keyinta wuri 4 shi bayayi, Ga wuraren kamar Haka
1- ولم يجعَل له عِوَجا(١) قيما لينذر بأسا شديدا
2- من بَعَثَنَا من مرقَدِنا هذا ما وَعَدَ الرحمن
3- وقِيلَ مَن رَاق
4- كلا بل ران على قلوبهم
Baya yin Sak'tar wadannan wuraren
6- IZ'HARI DA IDGAMI الإظهار والإدغام
IZ'HARI shine Fitar da Harafi daga mafitarshi ba tareda anyimishi Gunnah ba
IDGAMI Shine Shigar da Wani Abu a cikin wani abu
Akwai wasu Haruffa da ke Shiga cikin wasu kuma Riwayoyi sunyi sabani a garesu wato wasu suna Izhari wasu kuma Suna Idgami
Akwai
(إِذْ) ت ز ص د س ج harafi 6
(قَدْ) harafi 8 س ذ ض ظ ز ج ص ش
(تَاء التأنيث) harafi 6 س ث ص ز ظ ج
(هَل) ( بَل) harafi 8 ت ث ظ ز س ن ط ض
Akwai haruffan Da ke shiga cikin wadannan Haruffan musali
إِذْ
Haruffa 6 ke shiga cikin إِذْ sune
ت ز ص د س ج
Kamar
إِذ تَّمشِي أُختُكَ
إِذ سَّمِعْتُمُوهُ
Da sauransu
Ibn Zakwan yana yin Idgamin إذ a cikin harafi daya shine د
Kamar
إِذ دَّخَلُوا عليه
Sai yayi izhari a wurin sauran haruffa 5
Haka kuma yana yin Idgamin قد a wurin Haruffa hudu ( ض ذ ز ظ ) kamar
فقَد ضَّلَّ
وَلَقَد ذَّرَأنا
لَقَد ظَّلَمَكَ
وَلَقَد زَّينا السماء fuska biyu yakeda wurin wannan kalmar 1- idgami 2- Izhari
Yana yin Idgamin تَاء التأنيث a cikin Harafin ث da ط
kamar
كذَّبَت ثَّمود
كَانَت ظَّالمة
Haka kuma yana Idgamin
لَهُدمَت صَّوَامع
Yanada Fuska Biyu A wannan kalmar وَجَبَتْ جُنوبها yin IZ'HARINTA shine Yafi inganci
Ibn Zakwan yana Yin IZ'HARIN Duk Haruffan da ke shiga cikin هَل da بَل
Kenan zamu iya cewa bayada Komai a wurin هَل da بَل sai IZ'HARI
Haka kuma Yana Idgamin wadannan Kalmomin da zan jero
أَخَذتَّ أَخَذتُّم
اتَّخَذتَّ. اتَّخَذتُّم
لَبِثتَّ. لَبِثتُّم
كهيعصٓ ذِّكرُ idan zaa wuce
مَن يُرِدثَّوَابَ
يَلْهَث ذَّلك
Haka kuma yana yin IZ'HARIN wadannan Kalmar
اركَبْ مَعَنا
7- FAT'HA DA IMALAH الفَتحُ والإمالة
Riwayoyi sun kasu Gida Uku gameda abunda ya shafi IMALAH ko Rashin Yinta
1- Akwai wadanda Basuda Imala Ko Taq'lili ko daya Kamar Qira'ar Ibn Kathir da Abu Ja'afar
2- Akwai wadanda Imalah Daya Kawai Garesu Kamar, QALOON, warshu, Hafs,
Saidai kuma Warsh Yanada Taq'lili da yawa
3- Akwai masu Imaloli da Yawa kamar, Hamza da Kisa'i, Abu Amr da sauransu
Ibn Zakwan Bayada wani ma'auni ko Ka'ida tsayayya da yakebi wurin yin imalah Sabanin Hamzah da Kisa'i sunada ka'idoji
Sai dai Duk da haka Ibn Zakwan yana yin imalar wadannan Kalmomin da zan Jero
Yana imalar Harafin ج na kalmar
جَآء
Duk inda tazo a cikin Qur'ani
Yana imalar Harafin ش na kalmar
شَآء
Duk inda tazo a cikin Qur'ani
Yana imalar Harafin ر na kalmar
تَورَاةَ
Duk inda tazo a cikin Qur'ani mai Alif Da lamun Ko wacce batada
المِحرَابِ wacce harafin ب dinta yanada jarrah ko ince kas'ra
Amma idan Kalar haka yake المِحرَابَ to fuska boyu yakeda ita
Baya yin Imalah a kalmar
بسم الله مُجْرَاهَا
Yana imalar Harafin ز na kalmar زَادَ ta farko a alqurani itace
فَزَادَهُم الله مَرَضًأ
Banda wannan to yanada fuska biyu a sauran Wu Raren da kalmar زَادَ tazo
Haka ma yanada fuska biyu a wurin yin imala ko rashin yinta
حِمَارِكَ
الحِمَارِ
عِمْرَان
هَارٍ
إكرَاهِهُنَّ
Yanada fuska biyu ga wadannan kalmomin da na Ambata
8-YA'ATUL IDAFAH الياءات الإضافة
Ya'ul Idafah itace ya'un Da mai magana keyin anfani da ita domin Jingina wani abu zuwa gareshi
Wannan Ya'un Ta kasu Kashi-kashi
Kamar haka:-
= Akwai wace harafin Hamzah أإ mai fataha ko kasra ko Dwamma yake zuwa a gabanta
إِنِّــيٰٓ أَعلَم
إِنِّــيٰٓ أُرِيد
دُعَآءِىٰٓ إلا فرارا
= Akwai kuma wacce lamu-Al ( لام ال. التعريف ) ke zuwa a gabanta kamar haka
- لا ينال عَهدِى الظلمين
- عبادى الصلحون
- إنما حرم ربـى الفواحش
Da dai sauransu
= Akwai kuma wacce Hamzatu-waslin (الهَمزَةُ الوَصل) ke zuwa Gabanta kamar
- إنـى اْصطفَيتُك على الناس
- إن قومى اتخذوا
- يأتـى من بعدى اْسمه أحمد
= Akwai kuma wacce Haruffa ke zuwa a gabanta ba Hamzah أ ko Lamu-Al ba Misali
- أين شركآءِى قالوا
- من وراءِى وكانت امرأتي عاقرا
- لكم دينكم ولى دين
- إن أرضِى واسعة
Da sauransu
Mazhabar ibn Zakwan a wannan babin Itace Iskan Wato Daure Ya'un ي
Akwai wasu kalmomi da Hafs yake dauresu shi kuma Hisham yana yimusu Fat'ha
Gasu kamar haka
وما توفيقِيَ إلا بالله
إنما أشكوا بثى وحزنِـىَ إلى الله
كتب الله لأغلبن أنا ورسلىَ إن الله
دُعاءِيَ إلا فرَارا
لعليَ أرجع إلى الناس
لعليَ ءاتيكم منها طه والقصص
لعليَ أعمل صلحا
لعليَ أطلع إلى إله موسى
لعليَ أبلغ الأسبب
أَرَهْطِىَ أَعز عليكم من الله
عَهديَ الظلمين
إن أرضِيَ واسعة
صرطِيَ مُستقيمًا فاتبعوه
Wadannan sune Yaat da Hisham yake yiwa fat'ha
Akwai wasu kalmomi da Hafs yake yimusu Fat'ha shi kuma ibn Zakwan yana Daure su
Gasu kamar haka
سأصرف عن ءايــٰــتي الذين يتكبرون في الأرض
مَعِي. A duk wuraren da hafs ke yimata fataha
بباسط يدي إليك
قل لعبادي الذين آمنوا يقيموا الصلوة
ما كان لـي من علم
ولـي فيها مآرب
ولـي نعجة
يعبادي لا خوف ya kara Ya'un
وجهي لله.
وجهي للذي
ولمن دخل بيتي
بيتي للطائفين
9- Ya'atuzzawa'id الياءات الزوائد
Ita kuma wannan Itama ya'un ce da Asalinta ba arubuce take ba a cikin Qur'ani, Anyi Ilhakinta ne a cikin Mushafi
Qurra'u sunyi sabani a wurin karanta ta Da kuma Waqafi akanta, sun kasu kashi uku
1- Akwai masu karanta ta A kowane irin yanayi ( lokacin tsayawa (WAQAFI) a kanta, ko lokacin wucewa da karatu a kanta) kamar Ibn Kathir
2- Akwai Wadanda basu karantawa da ita A kowane irin yanayi Na karatu ( lokacin tsayawa (WAQAFI) a kanta, ko lokacin wucewa da karatu a kanta) Kamar Hafsu
3- Akwai wadanda ke Tabbatar da ita a lokacin wucewa da Karatu, suna cireta wurin WAQAFI Kamar warsh Da Al-imam Al-dury
Al-imam Al-susi yana Tabbatar da wannan Ya'un ne kawai A lokacin sadar da karatu
Akwai wuraren da yake saka Ya'un din haka kuma Akwai inda baya sakawa
Sai a nemi littafai domin akarin bayani
Ya'atuz-zawa'id Tana zuwa ne a cikin wadannan kalmomin da ire-iren su
إلى الداع
إذا دَعَان
واليل إذا يَسر
=الجَوَار
الجَواب
يناد المناد
Da sauransu
Ibn Zakwan Bayada Wannan Ya'un din da yawa
Ibn Zakwan yanada Fuska biyu ga kalmar
فلا تسئلني عن شيء
Yana saka ya'un, kuma yana cireta
Domin neman Karin Bayani a Bincika cikin littafan da sukayi magana akan Wannan Riwayar.
وَحُــــجَّــــتِــــي قِـــــــرَاءَةُ ابـنِ عَـــــامِــــر
فَـــــكَـــم لَــهَـــا مِـن عَــاضـــدِ وَنَـــــاصِـــــرِ
Anan zamu tsaya sai a taremu a rubutu na gaba inda zamuyi Rubutu akan Wata Qira'a ta gaba wato Qira'ar Asim
Insha Allah
Abunda Muka Fada Daidai Allah ya bamu ikon yin Aiki dashi Kuskure kuma Allah ya yafe muna ya Gogeshi cikin Zukatan mu.
JAN HANKALI
Duk wanda Zaiyi sharing ko Kwafi Na wannan Rubutun nawa To ya yi Sharing Dinshi A yadda Na Rubutashi Kar ya kara komai kuma Kar ya canja komai abar shi yadda nayishi
Duk wanda yakeda Ta'aliki ko gyara Ko shawara ko Mulahaza akan Wannan Rubutun to ya atuntubeni nizan gyara Da kaina Amma Kar A canja Min rubutu.
Ga lambar da zaa tuntubeni da ita +2348034468543
![✍️](https://static.xx.fbcdn.net/images/emoji.php/v9/te2/1/16/270d.png)
WANDA YA RUBUTA
Habibu Muhammad Shugaba
+2348034468543
Tuesday
04-04-14438
08-11-2021