Monday, 14 March 2022

RUBUTU NA 15: TARIHIN QARI'AI GOMA 10 DA RIWAYOYINSU 20 | تاريخ القراء العشرة ورواتهم

 رِوايــةُ شُعْبَة

عَن عَـاصِم
TARIHIN QARI'AI GOMA 10 DA RIWAYOYINSU 20
تاريخ القراء العشرة ورواتهم
RUBUTU NA: 1️⃣5️⃣
Rubutawar
✍Habibu Muhammad shugaba
ABUBUWAN DA KE KARKASHIN WANNAN RUBUTUN
👇👇👇👇👇
1- WANENE SHU'UBAH
2- MALAMAN SHU'UBAH
3- MAGANAR MALAMAI GAMEDA SHU'UBAH
4- DALIBAN SHU'UBAH
5- BAYANI AKAN USUL NA RIWAYAR SHU'UBAH
6- RUFEWA
1- WANENE SHU'UBAH?
Sunanshi:- Shu'ubah ibn Ayyash ibn Salim Al-asadi Al-kufi
Shu'ubah ya kasance Masani Na Hakika A fannin Karatun Qurani Haka kuma Mai yawan Ilimi ne da kuma Aiki da ilimin da Yakeda shi
Shu'ubah Daya ne daga cikin Rawiyan Asim Guda biyu, Kuma shi ake Gabatarwa kan Hafs A wurin Jerin Sunayen Riwayoyi da kuma Wurin جَمْعُ القِراءَات
HAIHUWARSHI
Harun ibn Hatim Yace:- Naji Shu'ubah yana cewa "An Haifeni a shekara ta 95" Bayan Hijrah
RASUWARSHI
Yahya Al-himani yace:- A lokacin da ciwon Ajali ya Kama Shu'ubah yar uwarshi ta kama Kuka Sai Shu'ubah ya tambayeta yace da ita " Me kike yiwa Kuka? Dubi wancen Wurin (ya Nuna mata wani wuri da ya kebe domin sallah da kuma Karaun Qur'ani) yace da ita Nayi Saukar Al-Qur'ani mai girma Har Dubu Goma sha Takwas (18,000) a cikinta".
Ya fadamata wannan ne domin ya kwantar mata da hankali, Kuma wannan Zai nuna muna Yadda yake yawan Karatun Qur'ani mai Girma
SHU'UBAH ya rasu a watan Jimadal-Ula shekara ta 193 yanada Shekaru 98 a duniya
رحمه الله رحمة واسعة
2- MALAMAN SHU'UBAH
1- Asim Abin-najud Al-kufi ( القارئ)
2- Ada'u ibn As-sa'ib
3- Aslam Al-munqari
4- Isma'il Al-asadi
5- Sulaiman ibn Mihran ( Al-a'amash)
6- Hussain ibn Abdulrahman
3- MAGANAR MALAMAI GAMEDA SHU'UBAH
Akwai Riwayoyi da dama da aka Riwaito kalamai na yabo da akayowa Shu'ubah daga maluma Daban-daban wasu maganganun ma An Riwaito shi Shu'ubah din ya fadesu da kanshi
Ga wasu daga cikinsu
Abdullahi Al-nakha'i da Yahaya ibn Ma'in Sunce " Tsawon Shekaru 50 Ba'a Taba yiwa Shu'ubah Shimfida domin ya yi bacci ba"
Sun fadi wannan ne domin Su nuna yadda yake yawan Ibada a cikin dare, Ba wai suna Nuni ne akan Baya bacci ba
Haka kuma yana nuna Zuhudun Shu'ubah Domin Rashin Yin Bacci akan shimfidar da zata iya shagaltar dashi akan Ibadah
= Yahya ibn Adam yace :- Shu'ubah yace dani " Na Yi karatun Qur'ani a wurin Asim Kamar Yadda Yaro ke koyon Karatu a wurin Malaminshi"
= Hafs Yacewa Asim " Shu'ubah yana Sabamin A wirin Karatu a wurare da yawa" Sai Asim yace da Hafs " Na koyama Karatu ne Irin karatun da na koya daga Wurin Abdulrahman As-sulami Shi kuma ya koyo wannan jaratu ne daga Aliyu Ibn Abi Dalib رضي الله عنه. Shi kuma (Shu'ubah) Na koya mishi Karatu ne wanda na koya daga Zirru ibn Hubaish Shi kuma Zirru ya koya daga Abdullahi ibn Mas'ud رضي الله عنه "
= Mujahid Yace" Akwai Ban-bancin فرش الحروف tsakanin Hafs da Shu'ubah"
4- DALIBAN SHU'UBAH
1- Abu Yusuf ibn Khalifah Al-a'asha
2- Abdulrahman ibn Abi Hammad
3- Urwah ibn muhammad Al-asadi
4- Yahya ibn Muhammad Al-alimi
5- Sahl ibn Shu'aib
Al-imam Abu Amr Al-dani Yace:- Ba'asan Wasu da sukayi Karatu Baki-da-baki ga Shu'ubah ba Sabanin wadannan mutanen Biyar
GA WANI BAYANI MAI MUHIMMANCI DA YA KAMATA MU SANI
👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇
Shu'ubah da Hafs Sunyi karatu Kaitsaye Ga Asim
Dama Wadanda ake Jinginawa riwayoyi (Masu Riwaya) Sun kasu gida uku
1- akwai wadanda sukayi karatu baki da baki ga QARI'AI da ake jinginawa riwayarsu zuwa garesu kamar
- Shu'ubah da Hafsu Sunyi karatu Kai tsaye Ga Asim
2- Akwai wadanda A tsakaninsu da QARI'AN akwai wasidar Mutun Daya kamar
- Dury da susi Sunyi karatu ga Yahyal-Yazidiyyi shi kuma yahya yayi karatu ga Abu Amr Al-basry
-Kamar Khalaf da khallad Sunyi karatu ga Sulaim shi kuma sulaim Yayi Karatu Ga Hamzah
3- Akwai wadanda akwai fiye da mutun daya a tsakaninsu da QARI'IN DA sukayi riwaya a gareshi kamar
- Hisham da ibn Zakwan basuyi karatu kai tsaye ga ibn Amir ba Akwai fiye da mutun daya a tsakanin su
Abun da yasa hakan ta faru shine
A lokacin da wannan ilimin na riwayoyi yayi yawa ya fadada riwayoyin sunyi yawa Kasancewar kowane Qari'i yanada dalibai masu dinbin yawa kuma kowane daga cikin su yana jingina riwayar shi zuwaga wannan Qari'in
Sai akayi niyyar Takaita Riwayoyin Akace kowane QARI'I zaa fitar da mutun biyu daga cikin Rawiyanshi (Dalibanshi) Wadanda sukafi kwarewa da kuma tsoron Allah Da tsantseni domin a jingina riwayar shi zuwa garesu
Sai a bincika Idan an samu wanda ya cika sharudan daga cikin Daliban QARI'IN, haka kuwa akayi Zabin Ya fada Ga Duriy da Susi sai aka aka cigaba da jingina Qira'ar Abu Amr Al-basry zuwa garesu, Riwayar su kuma ake jinginata kai tsaye zuwa gareshi (Abu Amr Al-basry) Sabanin asalin Malaminsu ( yahyal-yazidiyyi)
Wannan shine Ma'anar Fadar Shadibiyy
تَخَيرَهم نُقَّادُهُم كلَّ بَارِعٍ
وَلَيسَ عَلى قُرءَانِه مُتَأَكِّلا
Adadin Ayoyin Qur'ani na wannan QIRA'AR 6236
عَدُّ الكُوفِـيـينَ
Wato Qirgar Ayoyin Mutanen Kufa Wanda aka Riwaito daga Abu Abdilrahman Abdullahi ibn Habib As-sulami, shi kuma ya Riwaito daga Sahabi Aliyu ibn Abi Dalib رضي الله عنه
والله أعلم
Al-imam As-shadibiyy ya sanya Ramzin نَـــصَــــعْ ya zamo alamar da za'a Gane Qira'ar Asim da ita da kuma Riwayoyin shi Biyu Shu'ubah Da Hafsu
Ko ince Daya daga cikin Alamomin da zaa ganesu da ita
Ga abunda yake nufi
نَـــصَــــعْ
1- idan mukaga Ramzin ن a cikin Shadibiyya To Ramzi ne dake Nuni Ga Qira'ar Asim
2- idan mukaga Ramzin ص a cikin Shadibiyya To Ramzi ne dake Nuni Ga Riwayar Shu'ubah
3- haka kuma idan mukaga Ramzin ع a cikin Shadibiyya To Ramzi ne dake Nuni Ga Riwayar Hafs
والله أعلم
Za a Iya cewa QIRA'AR ASIM itace Qira'ar da tafi Kowace Qira'a Fice a duniya A wannan Zamani namu
Musamman ma Riwayar Hafs itace Riwaya Mafi Shahara a duniya a wannan Zamanin
SILSILAH DA ISNADIN RIWAYAR SHU'UBAH
Riwayar Shu'ubah An Asim
رِواية أبي بكر شعبة بن عَيَّاش ابن سَالِمٍ الأَسَدِي الكُوفِي لقراءة عاصم بن أبي النَّجُود الكُوفِي التَّابعِـي عن زِرِّ بن حُبَيْشٍ عن عبد الله بن مسعود وعثمان بن عفان وعَلِـي بن أبي طالب رضي الله عنهم عن النبى صلى الله عليه وسلم.
5- BAYANI AKAN USUL NA RIWAYAR SHU'UBAH
Malaman Qira'at Suna Kasa Kowace Riwaya zuwa Sashe Biyu Gasu kamar
1- Sashen Usul
2- Sashen Farsh فَرْش
Abunda ake cewa Usul shine Abubuwan da Riwaya ke Ginuwa akansu musamman Abunda da kaji anyishi kaitsaye zaka iya Fahimtar Riwayar da ake karantawa Misali
👇
= Idgamulkabir Ga Riwayar Susi
= Kamar Sak'tah السَّكْتَة ga riwayar khalaf
= Taglizin Lamun da Tarqiqin Ra'un Ga riwayar Warshu
= Silar HA'UL-KINAYAH Ga Qira'ar ibn kathir
Da dai sauransu
Farsh Kuma Shine Bayanin Kalmomin Qur'ani wadanda Qira'o'i sukayi Sabani a wurin karantasu
A cikin Farsh ne Zaayi bayani akan Kalma. Ace Wadannan suna karanta ta kamar haka, wadannan kuma ga yadda suke karantawa
A wannan Babin kuma Zamuyi bayani ne akan wadannan Abubuwan da zamu jero insha Allah
👇👇
1- BISIMILLAH DAKE ZUWA TSAKANIN SURORI BIYU ما جاء بين السورتين
2- HA'UL KINAYAH ko (هَاء الضمير)
3- MADDODI المُدُود
4- HUKUNCE-HUKUNCEN HAMZA
5- NAQLU DA SAKT النقل والسكت
6- IZ'HARI DA IDGAMI الإظهار والإدغام
7- FAT'HA DA IMALAH الفَتحُ والإمالة
8- YA'ATUL IDAFAH الياءات الإضافة
9- YA'ATUL-ZAWA'ID الياءات الزوائد
Akwai Babukan da zamu Tsallake basai munyi bayani akansu ba saboda Shu'ubah da Hafs sunyi muwafaqa a cikinsu sai a nemi littafan Qira'at domin neman Qarin bayani
1- BISIMILLAH DAKE ZUWA TSAKANIN SURORI BIYU ما جاء بين السورتين
Kamar yadda muka sani cewa a tsakanin Surorin Qur'ani Akwai Bisimillah dake zuwa idan mutun ya gama wata surah zai shiga wata
Tsakanin Anfal da Taubah ne kawai babu basmalah
Shu'ubah bai sabawa Hafs ba a wannan Babin Kamar yadda Hafs yakeda Fuskoki Uku to shima Shu'ubah Uku yakeda su Gasu kamar Haka
1- قطع الجميع
Shine Ka kare sura Ka tsaya Kayi bisimillah ka tsaya sai ka shiga wata sura
Misali
ولم يكن له كفوا أحد، بسم الله الرحمن الرحيم، قل أعوذ برب الفلق
2- وَصلُ الجميع
Shine ka hade karshen sura da bisimillah da kuma farkon surar da take gaba Ba tareda ka tsaya ba
Misali
ولم يكن له كفوا أحدٌ بِسم الله الرحمن الرحيمِ قُل أعوذ برب الفلق
3- قطع الأول ووصل الثاني بالثالث
Shine Ka kai karshen sura ka tsaya Sai kuma ka hade Bisimillah da farkon surar da take gaba
Misali
ولم يكن له كفوا أحد، بسم الله الرحمن الرحيمِ قُل أعوذ برب الفلق
Haka kuma A tsakanin Anfal da Taubah Yanada Fuska Uku kamar sauran Riwayoyi a duk wadannan Fuskokin yana yinsu ba tareda Bisimillah ba
1- الوصل بلا بسملة
2- السكت بلا بسملة
3- القَطع بلا بسملة
Haka kuma Wajibi ne a wurin karatun kowace Riwaya Ayi bisimillah idan An gama سورة الناس kuma anaso a sake dauko karatu daga Fatiha
2- HA'UL KINAYAH ko (هَاء الضمير)
Ha'ul-kinayah Ha'un ce Da ke nuni akan wani abu Guda daya namiji (المُذَكَّر) Wanda bayanan الغَائِب Kamar عليه da فيه da sauran su
Akwai sabanin riwayoyi a wurare da dama a wurin wannan Ha'un din kamar haka
1- wasu suna Daure ta a wasu wuraren kamar. يُؤَدِّهْ إِلَيك
2- wasu kuma Wasu suna Yimata Wasali ba tare da anja mata Madda Ba (Sila) kamar. يُؤَدِّهِ إِلَيك
3- wasu kuma Suna Yimata Wasali tareda Silar ta wato jan Madda Gareta kamar يُؤَدِّهِ> إِلَيك
A nemi littafan Riwayoyi domin sanin matsayin kowace riwaya a wannan Babin
Shu'ubah Yana Karanta wadannan kalmomin Tareda Daure Ha'un
Ga kalmomin kamar haka
يُؤَدِّهْ إِلَيك
نُؤْتِهْ منها
نُوَلِّهْ ما تولى.
نُصْلِهْ جهنم.
وَيَتَّقِهْ فأولئك هم الفائزون
Yana Cire madda A wurin
فيهِ مُهَانًا
Sabanin yadda hafs da ibn kathir ke karantawa
Yana mayar da Dwammar Ha'un Ta dawo Kas'ra a wurin wadannan kalmomin
وَمَــــا أَنسَـــٰـــنِيهِ إلا الشيطـن
عَلَيهِ اللهَ
Sabanin yadda Hafs ke karantawa
3- MADDODI المُدُود
Maddah Itace Jan Sauti Saboda zuwan Daya daga Cikin Haruffan Madda Guda Uku sune. ا da و da ي
Alif Daurarra Idan Harafin da ke gabaninta kamar قَالَ
Wawun Daurarra idan Harafin da ke Gabaninta yanada Dwwmma ُ kamar نُوح
Ya'un Daurarra idan Harafin da ke Gabaninta yazo da Kas'ra ِ kamar قِيلَ
Shu'ubah Bai Sabawa Hafs ba a wannan babin na Madda
Kamar yadda Muka Sani Cewa Hafsu yana Ja 4 Ga maddul-munfasil da kuma Muttasil To shima Shu'ubah haka yake jan Wadannan Maddodin
Kar mu manta Da cewa Dariqar Shadibiyyah Hafsu Bayada Ja 2 ga Maddul-munfasil الجائز المنفصل
والله أعلم
4- HUKUNCE-HUKUNCEN HAMZA
Hamzah ء dayace Daga Cikin haruffan Hija'iyyah أب ت ث ج ح خ د zuwa karshe.
Riwayoyi sunyi sabani a wurin karanta ta a cikin wasu kalmomi Saboda yadda takeda Wahalar fada ga wani sashe na Larabawa
Wasu sunayin TAS'HILI a wurin wasu kalmomi
Wasu kuma sukanyi TAH'QIQI
Wasu kuma Ibdali ko Hazafi sukeyi a wurin wasu kalmomin
Shu'ubah Bai Sabawa Hafsu Ba A wurin Hukunce-Hukuncen Hamza ba Sai a wurare yan kadan
Sunyi sabani ne a wurin
1- الهمزتين من كلمة
2-الهَمز المُفرد
A wadannan Babukan ma Sunyi Muwafaqa A wurare Mafi yawa
Zamu kawo yan kalmomin da suka yi Sabani ne kawai A wurin Karantasu
Sabanin da sukayi anan Shine Akwai wasu kalmomi da Hafsu ke karantasu da harafin Hamzah ء Guda daya Shi kuma Shu'ubah yana karantasu da Hamzah biyu ءء
Haka kuma Akwai kalmomin da Hafsu ke Karantasu da Hamzah ء Shi kuma Shu'ubah sai ya karantasu ba tareda Hamzah ba ko kuma Shu'ubah ya Karantasu da Hamzah ء Shi kuma Hafsu ya karantasu ba tareda Hamza ba
1- الهمزتين من كلمة
Sune Hamza biyu أأ dake Zuwa tare a cikin kalma daya
Misali
ءأنذرتهم ءألد ءأمنتم
Da sauransu
Ga Kalmomin da Shu'ubah ke Kara harafin Hamza A wurin Karantasu shi kuma Hafs yana karantasu da Hamzah Daya
👇
أَئنَّ لَنَا لأَجرا Cikin Suratul A'arof
ءَأ ٰمَنتُم لَه قبل أن
ءَأ ٰمَنتُم به قبل أن
أَأَن كَانَ ذَا مَالِِ
ءأَعْجَـمِـــيٌّ وَعَرَبي
أَإِنَّا لَمغرَمُون
Idan muka Duba wadannan Kalmomin zamuga cewa Dukansu Hafs Yana karantasu ne da Hamzah Daya
2-الهَمز المُفرد
Itace Hamzah da take zuwa guda daya a cikin Kalma daya
Misali
يؤمن جِئت هِئتَ. شِئتَ يأت يؤتَونَ يأجوج ومأجوج
Da sauransu
Akwai sabanin Riwayoyi a wannan Babin Saidai mu Zamu Takaitu ne akan Kalmomin da Shu'ubah Ya sabawa Hafsu a ciki
Wadannan Kalmomin da zamu kawo Shu'ubah yana karantasu Ba tare da harafin Hamzah ء ba shi kuma Hafsu yana Karantawa Da Hamzah
👇👇👇👇👇
عليهم نار مُوصَدَةٌ
إنها عليهم مُوصَدَةٌ
اللَُّولُؤ
لُولُؤا
Kamar
يخرجُ منهُمَا اللَُّولُؤُ
من أسَاوِرَ من ذَهَب ولُولُؤًا
Hamzar Farko yake cirewa
Wadannan Kalmomin kuma Yana Sanya harafin Hamzah ء a garesu shi kuma Hafsu yana cire Hamzah
👇👇👇👇
وءاخَرُون مُرْجَئُونَ لِأمر الله
تُرْجِئُ مَن تَشَآء منهن
هُزُؤًا a duk inda tazo
كُفُؤًا أَحَد
Idan muka Duba Dakyau zamuga Karara Sun Saba A wadannan Kalmomin da muka kawo
والله أعلم
5- NAQLU DA SAKT النقل والسكت
Abunda ake cewa NAQLU shine Cirato wani abu Daga wani wuri Zuwa wani wuri, Anfi amfani da wannan isdilahin Ga Hamza a wurin maluman Qira'o'i kamar ace
نقل حركة الهمزة إلى الساكن قبلها
Wato cirato Wasalin Hamza a dorashi kan Harafin da ke Gabaninshi kamar ace
قَدَ افْلَحَ
مَنُ اوتِـيَ
Da sauransu
Warshu shine mai wannan Babin
SAKTAH:- Tana nufin Tsayawa dan lokaci kadan a yayin Karatu ba tareda Shedawa (nufashi) ba sannan a wuce kamar كَلَّا بَل رَان sananne a Riwayar Hafs
Shu'ubah bayada Naqlu ko Saktah a cikin Qurani don Haka duk wuraren nan Da hafs keyin Saktah wuri 4 shi bayayi, Ga wuraren kamar Haka
1- ولم يجعَل له عِوَجا(١) قيما لينذر بأسا شديدا
2- من بَعَثَنَا من مرقَدِنا هذا ما وَعَدَ الرحمن
3- وقِيلَ مَن رَاق
4- كلا بل ران على قلوبهم
Baya yin Sak'tar wadannan wuraren
6- IZ'HARI DA IDGAMI الإظهار والإدغام
IZ'HARI shine Fitar da Harafi daga mafitarshi ba tareda anyimishi Gunnah ba
IDGAMI Shine Shigar da Wani Abu a cikin wani abu
Akwai wasu Haruffa da ke Shiga cikin wasu kuma Riwayoyi sunyi sabani a garesu wato wasu suna Izhari wasu kuma Suna Idgami
Akwai
(إِذْ) ت ز ص د س ج harafi 6
(قَدْ) harafi 8 س ذ ض ظ ز ج ص ش
(تَاء التأنيث) harafi 6 س ث ص ز ظ ج
(هَل) ( بَل) harafi 8 ت ث ظ ز س ن ط ض
Shu'ubah da Hafsu Basuda Banbanci a wadannan Babukan na
إذ
قَد
تاء التأنيث
هَل
بَل
Shu'ubah da Hafsu sunayin Izharin duk wadannan
Saidai akwai Wuraren da Dukkan Qurra'u sukayi Ittifaqi wurin yin Idgamin wasu kalmomi, to wannan wurin suna yin Idgami kamar kowa
A nemi littafan Riwayoyi domin neman karin Bayani
والله أعلم
Shu'ubah Yana Idgamin wadannan Kalmomin da zan jero
أَخَذتَّ أَخَذتُّم
اتَّخَذتَّ اتَّخَذتُّم
يسٓ والقرءان
Idan ya Sadar da يسٓ da والقرءان
نٓ والقَلَم
Idan ya Sadar da نٓ da والقَلَم maana idan bai tsaya ba
والله أعلم
7- FAT'HA DA IMALAH الفَتحُ والإمالة
Riwayoyi sun kasu Gida Uku gameda abunda ya shafi IMALAH ko Rashin Yinta
1- Akwai wadanda Basuda Imala Ko Taq'lili ko daya Kamar Qira'ar Ibn Kathir da Abu Ja'afar
2- Akwai wadanda Imalah Daya Kawai Garesu Kamar, QALOON, warshu, Hafs,
Saidai kuma Warsh Yanada Taq'lili da yawa
3- Akwai masu Imaloli da Yawa kamar, Hamza da Kisa'i, Abu Amr da sauransu
Shu'ubah yana daga Cikin Riwayoyin da suke da imaloli Fiye da daya
Sai dai duk da haka basuda Yawa sosai kamar sauran Riwayoyin da ke yin imalah da yawa
Ga Kalmomin da yake yiwa Imala a duk inda Sukazo a cikin Qur'ani
Yana yin imalah ga Harafin ر a duk inda wadannan kalmomin Sukazo
أدرىٰك
أدرىٰكم
بَل رّانَ
Haka kuma yana yin imalah ga Harafin ر da kuma ء da ke zuwa a cikin Kalmomin
رَءَا رَءَاكَ رَءَاهُ رَءَاهَا
Da sharadin a Samu Harafi mai Wasali yazo a gaban hamzah Na kalmar رَءَا Misali
رَءَا كَوكَبًا
Da sauransu
Amma idan Aka samu Harafi mai Dauri (skun) yazo Gaban رَءَا to Yana yin imalah ne Ga harafin ر kawai a lokacin da zai Sadar da karatu misali
رَءَا القَمَرَ
رَءَا الشَّمْسَ
Da sauransu
Amma idan
Amma a Duk lokacin da zaiyi waqafi (tsayawa) akan kalmar رَءَا to zaiyi imalar harufan Guda biyu koda kuwa akwai harafi mai dauri a gaba
والله أعلم
Haka ma yana IMALAH ga harafin م a wadannan Kalmomin
رَمَى
وما رميت إذ رميت ولكن الله رَمَى
Da kuma أعمى Guda biyu na suratul Isra'i
أعمى
ومن كان في هذه أعْمَى فهو في الآخرة أعْمَى
Haka kuma yana yin Imalah ga Harafin ء Na cikin kalmaar نَــئَــا da tazo a سورة الإسراء
وإذا أنعمنا على الإنســن أعرض ونَــئَــا بجانبه
Duk da cewa ba haka yake Rubuce a cikin Qur'ani ba
Wannan kawai Yake yiwa imalah Baya yin imalar na Suratu Fussilat
Wadannan Sune Wuraren Da Shu'ubah yakeyin Imalah
Shu'ubah baya yin Imalah Ga Kalamr مَجرىها wacce Hafs yake yiwa imalah
والله أعلم
8-YA'ATUL IDAFAH الياءات الإضافة
Ya'ul Idafah itace ya'un Da mai magana keyin anfani da ita domin Jingina wani abu zuwa gareshi
Wannan Ya'un Ta kasu Kashi-kashi
Kamar haka:-
= Akwai wace harafin Hamzah أإ mai fataha ko kasra ko Dwamma yake zuwa a gabanta
إِنِّــيٰٓ أَعلَم
إِنِّــيٰٓ أُرِيد
دُعَآءِىٰٓ إلا فرارا
= Akwai kuma wacce lamu-Al ( لام ال. التعريف ) ke zuwa a gabanta kamar haka
- لا ينال عَهدِى الظلمين
- عبادى الصلحون
- إنما حرم ربـى الفواحش
Da dai sauransu
= Akwai kuma wacce Hamzatu-waslin (الهَمزَةُ الوَصل) ke zuwa Gabanta kamar
- إنـى اْصطفَيتُك على الناس
- إن قومى اتخذوا
- يأتـى من بعدى اْسمه أحمد
= Akwai kuma wacce Haruffa ke zuwa a gabanta ba Hamzah أ ko Lamu-Al ba Misali
- أين شركآءِى قالوا
- من وراءِى وكانت امرأتي عاقرا
- لكم دينكم ولى دين
- إن أرضِى واسعة
Da sauransu
Mazhabar Shu'ubah a wannan babin Itace Iskan Wato Daure Ya'un ي
Shu'ubah Bai Sabawa Hafsu ba Sai a wurare kadan
Akwai Kalmomin da Hafsu Ke yiwa Fat'ha Shi kuma Shu'ubah yana Dauresu
👇👇👇
مَعِي
Duk inda Tazo kamar
مَعِي أبدًا ولن تقاتلوا مَعِي عَدُوا
Da sauransu
إن أجرِىٰٓ إلا
A duk inda tazo idan ya Daure ya'un zata koma Maddul-munfasil sai ya yi Ja 4
بَيْتِي
Guda uku da suka zo
بَيْتِي للطائفين والعاكفين
بَيْتِي للطائفين والقائمين
وَلِمَن دخَلَ بَيْتِي
Yana daure ya'un dinsu
وَجْهِي
Guda biyu
فقل أسلمت وَجْهِي لله
إني وجهت وَجْهِي
Haka kuma
وَلِـي فيها مآرب أخرى
وَلِـي نَعْجَة
لكم دينكم وَلِـي دين
وما كان لِـي عليكم من سلطن
ما كان لِـي من علم
وَأُمِّـيٰٓ إلــٰــهَين
ما أنا بباسط يَدِىٰٓ إليك
Wadannan sune wuraren da Hafs Ke Yin Fat'ha Ga yي shi kuma Shu'ubah ya Daure ta
Ga Wuraren da Hafs Ke Daure ي Shi kuma Shu'ubah Ya yi mata Fat'ha يَ
👇👇👇👇
لا ينالُ عَهدِيَ الظالمين
يأتي من بعدِيَ اْسْمُهُ أحمد
Wannan kuma Shu'ubah yana Kara Harafin ي kuma ya yi mata Fat'ha a يَــٰــعِبَاد cikin Suratul-Zukhruf
يَــٰــعِبَادِيَ لا خَوفٌ عليكم اليوم
Wadannan sune wuraren da Hafs ya sabawa Shu'ubah
Sauran wuraren da bamu kawo ba kuma Shu'ubah yana tare da Hafs A wurin Karantasu
والله أعلم
9- Ya'atuzzawa'id الياءات الزوائد
Ita kuma wannan Itama ya'un ce da Asalinta ba arubuce take ba a cikin Qur'ani, Anyi Ilhakinta ne a cikin Mushafi
Qurra'u sunyi sabani a wurin karanta ta Da kuma Waqafi akanta, sun kasu kashi uku
1- Akwai masu karanta ta A kowane irin yanayi ( lokacin tsayawa (WAQAFI) a kanta, ko lokacin wucewa da karatu a kanta) kamar Ibn Kathir
2- Akwai Wadanda basu karantawa da ita A kowane irin yanayi Na karatu ( lokacin tsayawa (WAQAFI) a kanta, ko lokacin wucewa da karatu a kanta) Kamar Shu'ubah
3- Akwai wadanda ke Tabbatar da ita a lokacin wucewa da Karatu, suna cireta wurin WAQAFI Kamar warsh Da Al-imam Al-dury
Wuri Daya ne Shu'ubah ya Sabawa Hafs a wannan Babin
Shine fadar Allah ( S W T)
فما ءاتَــــٰــنِ الله خير
Shu'ubah yana cire Wannan Ya'un din
Idan ya Cireta
Zaiyi تغليظ لام الإسم الجلاله a lokacin da zai wuce da karatu.
Zai Daure Harafin نْ idan zaiyi Waqafi akan kalmar ءاتَــــٰــن
Mun san cewa Hafs Fuska biyu yakeda ita a lokacin da zai tsaya a wannan kalmar
والله أعلم
Ya'atuz-zawa'id Tana zuwa ne a cikin wadannan kalmomin da ire-iren su
👇👇👇👇
إلى الداع
إذا دَعَان
واليل إذا يَسر
=الجَوَار
الجَواب
يناد المناد
Da sauransu
Domin neman Karin Bayani a Bincika cikin littafan da sukayi magana akan Wannan Riwayar.
5- RUFEWA
فَــأَمَّا أَبُــوبَـكْرٍ وَعَــاصِــمُ اسْــمُــهُ
فَـــشُــعْـبَــةُ رَاوِيهِ الــمُــبَـرِّزُ أَفْـضَـلَا
وَذَاكَ ابنُ عَــيَّـــاشٍ أَبُـــوبَــكْرٍ الــرِّضَـا
وَحَــفْــصٌ وَبِـالإِتــقَـــانِ كَانَ مُفَضَّلَا
Anan zamu tsaya sai a taremu a rubutu na gaba inda zamuyi Rubutu akan RIWAYAR HAFS An Asim
Insha Allah
Abunda Muka Fada Daidai Allah ya bamu ikon yin Aiki dashi Kuskure kuma Allah ya yafe muna ya Gogeshi cikin Zukatan mu.
JAN HANKALI
👇👇👇👇
Duk wanda Zaiyi sharing ko Kwafi Na wannan Rubutun nawa To ya yi Sharing Dinshi A yadda Na Rubutashi Kar ya kara komai kuma Kar ya canja komai abar shi yadda nayishi
Duk wanda yakeda Ta'aliki ko gyara Ko shawara ko Mulahaza akan Wannan Rubutun to ya atuntubeni nizan gyara Da kaina Amma Kar A canja Min rubutu.
Ga lambar da zaa tuntubeni da ita +2348034468543
✍️WANDA YA RUBUTA
Habibu Muhammad Shugaba
+2348034468543
Monday
24-04-1443
29-11-2021

RUBUTU NA 14: TARIHIN QARI'AI GOMA 10 DA RIWAYOYINSU 20 | تاريخ القراء العشرة ورواتهم

 قِرَاءَةُ الإِمَام عَاصِمٍ

ابن أبِـي النَّجُود الكُوفِـي
TARIHIN QARI'AI GOMA 10 DA RIWAYOYINSU 20
تاريخ القراء العشرة ورواتهم
RUBUTU NA: 1️⃣4️⃣
Rubutawar
✍Habibu Muhammad shugaba
ABUBUWAN DA WANNAN RUBUTUN YA KUNSA
👇👇👇👇👇
1- WANENE AL-IMAM ASIM
2- MALAMAN AL-IMAM ASIM
3- YABO DA KUMA MAGANAR MALAMAI GAMEDA AL-IMAM ASIM
4- DALIBAN AL-IMAM ASIM
5- KALMOMINDA QIRA'AR ASIM TA SABAWA DUKKAN QIRA'O'I WURIN KARANTASU (انفرادت قراءة الإمام عَاصِم)
6- RUFEWA
1- WANENE AL-IMAM ASIM?
SUNANSHI:- Asim Ibn Bahdalah, ibn Abin-najud, Al-kufi, Al-Asadiyy
ALKUNYARSHI:- Abu Bakr wasu kuma Sukace Abu Amr
Ance Abun-najud Shine Sunan Mahaifinshi na Hakika wasu Sunce sunan Abun-najud din Abdullahi
BAHDALAH:- Sunan Mahaifiyarshi ne
Asim Daya Ne daga Cikin QARI'AI 7 Na Qur'ani
Asim Masanin Qur'ani da Hadisi ne
Bayan Rasuwar Abu Abdil-raman As-sulami Asim ne ya zamo Shugaba kuma Jagora a Fannin karatun Qur'ani a garin Kufa
Haka kuma Asim mutum ne mai fasaha, mai dadin sauti, masanin Tajwidin Qur'ani, Masanin Hadisi.
An Haifi Asim A garin Kufa ya rayu a garin kufa haka ma Ya rasu a garin kufa
A dana binciken da Nayi Mafi yawan Littafan da na Duba Maluma Basu Hakaito Ayyanannar Rana ko shekarar da aka Haifi Asim Ba
Sai dai naga Wadanda Sukace An haifeshi a shekara ta 700 miladiyyah
Asim Ya rasu a shekara ta 127 bayan Hijrah dai dai da 745 Miladiyyah
رحمه الله رحمة واسعة
2- MALAMAN AL-IMAM ASIM
1- Zirru Dan Hubaish
Shi kuma Zirru ya yi Karatu ne ga Sahabi Abdullahi Dan Mas'ud رضي الله عنه
2- Abu Abdil-rahman Al-sulami
Shi kuma Abu Abdil-rahman ya yi karatu ne Ga Sahabi Aliyu Bn Abi Dalib رضي الله عنه
3- Abu Amr Sa'ad Ibn Iyas
An Hakaito cewa shi wannan Sa'ad Ibn Iyasdin Ya Riski Zamani Annabi صلى الله عليه وسلم Sai dai Bai Hadu Da Annabi صلى الله عليه وسلم ba ya yi Karatu Ga Sahabi Abdullahi Dan Mas'ud رضي الله عنه
Tsakanin Asim Da Annabi صلى الله عليه وسلم Mutum biyu ne kawai
Saboda haka Zamu iya Cewa Qira'arshi Itace Mafi Gajartar Isnadi Daga Cikin Qira'o'i Goma Idan Aka Cire Qira'ar Ibn Kathir da ta Ibn Amir Domin su sunyi Karatu har ga wasu Daga cikin Sahabbai
GA Silsila ko ince Isnadin Riwayoyi Biyu na Qira'ar Asim
1-Riwayar Shu'ubah An Asim
2- Riwayar Hafs An Asim
1-Riwayar Shu'ubah An Asim
رِواية أبي بكر شعبة بن عَيَّاش ابن سَالِمٍ الأَسَدِي الكُوفِي لقراءة عاصم بن أبي النَّجُود الكُوفِي التَّابعِـي عن زِرِّ بن حُبَيْشٍ عن عبد الله بن مسعود وعثمان بن عفان وعَلِـي بن أبي طالب رضي الله عنهم عن النبى صلى الله عليه وسلم.
2- Riwayar Hafs An Asim
رِواية حَفْص بن سليمان الأَسَدِي الكُوفِي لقراءة عَاصِم بن أبي النَّجُود الكُوفِي التَّابعِـي عن أبي عبد الرحمن السَُلَمِـي عَن عثمان بن عفان وعَلِـي بن أبي طالب وزيد بن ثَابِت وأُبَـيُّ بن كَعْب رضي الله عنهم أجمعين عن النبى صلى الله عليه وسلم.
3- YABO DA KUMA MAGANAR MALAMAI GAMEDA AL-IMAM ASIM
= Shu'ubah Ibn Ayyash Yace:- Asim Ya cemin " Nayi Rashin Lafiya Har Tsawon Shekara Biyu Wata Rana na Karance Qur'ani Ba tareda nayi Kuskuren Koda Harafi Daya ba"
Wannan Shi zai Nuna Muna Karfin Haddar Shi Domin ya yi Rashin Lafiya Bayan Yaji sauki yayi wannan karatun
=Ibn Ayyash Yace:- Sau da yawa nikejin Abu Ishaq Assabi'i yana Cewa " Ban Taba Ganin Wanda yafi Asim ibn Abin-Najud Iya karatu ba"
= Yahya Ibn Adam Ya Riwaito daga Hassan Ibn Salih Yana Cewa " Ban taba ganin sanda Yafi Asim Fasaha ba"
=Abdullahi ibn Ahmad Ibn Hanbal yace :- Na Tambayi Babana (Ahmad Dan Hanbali Daya daga Cikin Malaman Mazhabobi hudu) Na tambayeshi Gameda Asim Yace " Mutumin Kirki ne Siqah Salihi"
4- DALIBAN AL-IMAM ASIM
Asim Yanada Dalibai Da yawa Ga wasu daga Cikinsu
1- Aban Ibn Taglib
2- Aban Ibn Yazid Al-Addar
3- Hassan Ibn Salih
4- Hafs Ibn Sulaiman (mai Riwayah)
5- Al-hakam Ibn Zuhair
6- Hammad ibn Salamah
7- Hammad ibn Abi Ziyad
8- Hammad ibn Amr
9- Sulaiman ibn Mahran Al-A'amash Al-kufi
10- Sallam ibn Sulaiman
11- Abubakar ibn Ayyash Shu'ubah (Mai Riwayah)
12- Abu Amr Al-basry (mai Qira'ah)
13- Khalil ibn Ahmad Alfarahidi( Masanin Nahawu)
14- Hamzah ibn Habib Al-zayyat ( Mai Qira'ah)
15- Al-mugirah Al-dwabbi)
Da dai sauransu
Riwayar Shu'ubah Itace Ake Gabatarwa Akan Riwayar Hafs a wurin Jeranta Riwayoyi Ko Kuma جَمْعُ القِراءَات
Da Sauransu
Shu'ubah Da Hafs Sunyi Karatu Ga Asim Ne kai tsaye Baki-da-Baki
Sabanin wasu riwayoyin wanda Ana iya Samun Tsakanin msu da Qari'in da ake Jingina Riwayar su gareshi Akwai Wasidar Mutun Daya ko biyu wasu ma Sama da haka
GA WANI BAYANI MAI MUHIMMANCI DA YA KAMATA MU SANI
👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇
Wadanda ake Jinginawa riwayoyi (Masu Riwaya) Sun kasu gida uku
1- akwai wadanda sukayi karatu baki da baki ga QARI'AI da ake jinginawa riwayarsu zuwa garesu kamar
- Shu'ubah da Hafsu Sunyi karatu Kai tsaye Ga Asim
2- Akwai wadanda A tsakaninsu da QARI'AN akwai wasidar Mutun Daya kamar
- Dury da susi Sunyi karatu ga Yahyal-Yazidiyyi shi kuma yahya yayi karatu ga Abu Amr Al-basry
-Kamar Khalaf da khallad Sunyi karatu ga Sulaim shi kuma sulaim Yayi Karatu Ga Hamzah
3- Akwai wadanda akwai fiye da mutun daya a tsakaninsu da QARI'IN DA sukayi riwaya a gareshi kamar
- Hisham da ibn Zakwan basuyi karatu kai tsaye ga ibn Amir ba Akwai fiye da mutun daya a tsakanin su
Abun da yasa hakan ta faru shine
A lokacin da wannan ilimin na riwayoyi yayi yawa ya fadada riwayoyin sunyi yawa Kasancewar kowane Qari'i yanada dalibai masu dinbin yawa kuma kowane daga cikin su yana jingina riwayar shi zuwaga wannan Qari'in
Sai akayi niyyar Takaita Riwayoyin Akace kowane QARI'I zaa fitar da mutun biyu daga cikin Rawiyanshi (Dalibanshi) Wadanda sukafi kwarewa da kuma tsoron Allah Da tsantseni domin a jingina riwayar shi zuwa garesu
Sai a bincika Idan an samu wanda ya cika sharudan daga cikin Daliban QARI'IN, haka kuwa akayi Zabin Ya fada Ga Duriy da Susi sai aka aka cigaba da jingina Qira'ar Abu Amr Al-basry zuwa garesu, Riwayar su kuma ake jinginata kai tsaye zuwa gareshi (Abu Amr Al-basry) Sabanin asalin Malaminsu ( yahyal-yazidiyyi)
Wannan shine Ma'anar Fadar Shadibiyy
تَخَيرَهم نُقَّادُهُم كلَّ بَارِعٍ
وَلَيسَ عَلى قُرءَانِه مُتَأَكِّلا
Adadin Ayoyin Qur'ani na wannan QIRA'AR 6236
عَدُّ الكُوفِـيـينَ
Wato Qirgar Ayoyin Mutanen Kufa Wanda aka Riwaito daga Abu Abdilrahman Abdullahi ibn Habib As-sulami, shi kuma ya Riwaito daga Sahabi Aliyu ibn Abi Dalib رضي الله عنه
والله أعلم
Al-imam As-shadibiyy ya sanya Ramzin نَـــصَــــعْ ya zamo alamar da za'a Gane Qira'ar Asim da ita da kuma Riwayoyin shi Biyu Shu'ubah Da Hafsu
Ko ince Daya daga cikin Alamomin da zaa ganesu da ita
Ga abunda yake nufi
نَـــصَــــعْ
1- idan mukaga Ramzin ن a cikin Shadibiyya To Ramzi ne dake Nuni Ga Qira'ar Asim
2- idan mukaga Ramzin ص a cikin Shadibiyya To Ramzi ne dake Nuni Ga Riwayar Shu'ubah
3- haka kuma idan mukaga Ramzin ع a cikin Shadibiyya To Ramzi ne dake Nuni Ga Riwayar Hafs
والله أعلم
Za a Iya cewa QIRA'AR ASIM itace Qira'ar da tafi Kowace Qira'a Fice a duniya A wannan Zamani namu
Musamman ma Riwayar Hafs itace Riwaya Mafi Shahara a duniya a wannan Zamanin
5- KALMOMINDA QIRA'AR ASIM TA SABAWA DUKKAN QIRA'O'I WURIN KARANTASU (انفرادت قراءة عاصم)
Kowace Qira'a Tanada Wasu kalmomi da ta Sabawa Sauran Qira'o'i a wurin Karantasu.
Sabanin Zai iya Kasancewa Ta Fuskar Wasali ko canja Harafi da wani Harafi koma cire Harafin Gaba daya
Ga Kalmomin da Qira'ar Asim ta sabawa Sauran Qira'o'i
Zan kawo Kalmominda Riwayoyinshi biyu sukayi ittifaqi
Bazan kawo wadda daya ke karantawa banda daya ba
Saidai Abun Lura anan Shine Kalmar da nayiwa wasali ita nike nufin an saba gareta Kuma yadda nayi wasalin hakanan yake karantawa duk da cewa Zaa iya samun kalma mai banbancin Qira'at fiye da biyu To yadda nayi wasali haka nike nufin Asim ya sabawa sauran
ASIM Bayada انفرادت Da yawa Kamar Sauran Qira'o'i
Ga kalmomin
👇
1- من ذا الذي يقرض الله قرضا حسنا فَيُضَــٰـــعِـفَهُ له
Surar Baqarah da Hadid
2- وأن تَصَدَّقُوا خير لكم
Yana Cire Shadda Ga harafin ص sabanin Sauran Qira'o'i suna Karantawa ne تَصَّدَّقُوا
3- إلا أن تكون تِجَــٰــرَةً حَاضِرَةً
Saura Suna Karantawa ne
تِجَــٰــرَةٌ حَاضِرَةٌ
4- إن نَّعفُ عن طائفة منكم نُعَذِّبْ طائفةً
Sauran Qira'o'i suna Karantawa ne
إن يُعفَ عن طائفة منكم تُعَذَّبْ طائفةٌ
5- بُشْرًا بين يدي....
Surar A'atof da Furqan da Namli
Yana Karantawa da Harafin ب sabanin Sauran Riwayoyi da suke karantawa da ن duk da cewa Sun Saba Wurin Wasulla
6- يَأْجُوجَ ومَأْجُوجَ
Yana Karantawa da Harafin ءْ daurarre
Sauran Kuma Suna Karantawa ne Da yin Ibdalin Hamzar Zuwa Harafin Madda kamar haka يَاجُوجَ ومَاجُوجَ
7- أو جَذْوَةِِ من النار
Yana Yiwa جَ fat'ha
Dama a wurin Wasalin ج ne riwayoyi suka yi sabani a wannan kalmar Har Gida Uku
جَذْوَةِِ
جِذْوَةِِ
جُذْوَةِِ
8- تُظَــٰـهِرُون منهن أمهتكم
9- أُسْوَةٌ حسنة
Yana Yiwa أُ dwamma A duk Wurare Uku da wannan Kalmar tazo a cikin Qurani
Ahzab da Mumtahanah
Sauran kuma Suna yimata Kas'rah إِسْوَةٌ حسنة
10- وَخَاتَمَ النبيين
Da yiwa تَ fat'ha Sauran kuma suna Yimata Kas'ra ne وَخَاتِمَ
11- الذين يُظَــٰـهِرُون منكم من نسائهم
12- والذين يُظَــٰـهِرُون من نسائهم
13- إذا قيل لكم تفسحوا في المَجَــٰــلِسِ
Da yin fat'haDa kuma Maddar ج
Sauran kuma suna Cire Maddar Kuma Su daure جْ
إذا قيل لكم تفسحوا في المَـجْـلِسِ
14- أو يذكر فَتَنفَعَهُ الذكرى
Yana yiwa harafin عَ fat'ha
Sauran Kuma Suna yimishi Dwamma فَتَنفَعُهُ الذكرى
15- وامرأته حَمَّالَةَ الحطب
Da yiwa ةَ fat'ha
Sauran kuma Suna Yimata Dwamma حَمَّالَةُ الحطب
Wadannan Sune Kalmomin da Qira'ar Asim Da Sabawa Dukan Qira'o'i wurin Karantasu
A nemi Littafan Qira'at Domin neman Karin Bayani Zai iya Yiyuwa akwai Abunda ya kamata Mu saka Bamu sa ba ko kuma Wanda muka rubuta bai kamata mu Rubuta ba
والله أعلم
8- RUFEWA
Anan zamu tsaya sai a taremu a rubutu na gaba inda zamuyi Rubutu akan Riwayar Shu'ubah Daya daga cikin Riwayoyin Asim
Insha Allah
JAN HANKALI
👇👇👇👇
Duk wanda Zaiyi sharing ko Kwafi Na wannan Rubutun nawa To ya yi Sharing Dinshi A yadda Na Rubutashi Kar ya kara komai kuma Kar ya canja komai abar shi yadda nayishi
Duk wanda yakeda Taaliki ko gyara Ko shawara ko Mulahaza akan Wannan Rubutun to ya atuntubeni nizan gyara Da kaina Amma Kar A canja Min rubutu.
Ga lambar da zaa tuntubeni da ita +2348034468543
✍️WANDA YA RUBUTA
Habibu Muhammad Shugaba
+2348034468543
Saturday
15-04-1443
20-11-2021