Monday, 14 March 2022

RUBUTU NA 2: TARIHIN QARI'AI GOMA 10 DA RIWAYOYINSU 20 | تاريخ القراء العشرة ورواتهم

 TARIHIN QARI'AI GOMA 10 DA RIWAYOYINSU 20

تاريخ القراء العشرة ورواتهم
RUBUTU NA: 2️⃣
الإِمَـــــامُ نَــــافِــــعٍ الــــمَـــــدَنِـــــي
✍Habibu Muhammad shugaba
ABUBUWAN DA KE KARKASHIN WANNAN RUBUTUN
👇👇👇👇👇
1- Wanene Al-imam Nafi'u
2-Suwaye Maluman Al-imam Nafi'u
3-Maganar Malamai Akan Al-imam Nafi'au
4- Suwaye Daliban Al-imam Nafi'u
4- Takaitaccen Bayani Akan Qira'ar Al-imam Nafi'u
1- WANENE AL-IMAM NAFI'U
SUNANSHI:- Nafi'u Dan Abdulrahman Dan Abu Nu'aim, Ana Yimishi Al-kunya Da ABU RUWAIM
Shidai Nafi'u Daya ne daga Cikin القراء العشرة Kuma daya ne Daga cikin manyan Maluman zamaninshi, shi Sika ne mai Gaskiya, Launin shi Bakar Fata ne, Yanada Kyakkyawar Mu'amalah Da halaye masu kyau, Masani ne Akan Qira'o'i Da kuma Larabci, Shine Shugaban QARI'AI Makaranta Qur'ani A garin Madinah Bayan Wucewar أبو جعفر المدني.
Al-imam Nafi'u ya kasance idan yana karatu ko yana magana Anajin Kamshin Turare Yana Fita Daga Bakinshi, Sai aka Tambayeshi aka ce mishi " Shin Kana Shafa Turare ne A duk Lokacin da zaka Fito Karatu? Sai yace: Aa Ni bana Sanya Turare, Sai dai ni wata rana Nayi Mafarkin Annabi صلى الله عليه وسلم yana Karatu A cikin Bakina Tun daga lokacin Bakina Yake Kamshin Turar"
Wannan shine Ma'nar Fadar الإمام الشاطبي da yake cewa :
فَأَمَّا الكَريمُ السرِّ في الطِّيبِ نَافعٌ
فَذاكَ الذي اخْتارَ المَدِينةَ مَنزِلا
An haifi Al-imam Nafi'u A shekara ta 70 bayan Hijrah
Ya Rasu A garin Madinah A shekara ta 169 Bayan Hijrah Yanada Shekara 99 A duniya (رحمه الله رحمة واسعة )
2-SUWAYE MALUMAN AL-IMAM NAFI'U
An Ruwaito Cewa Al-imam Nafi'u Yayi karatu Ga mutane 70 Daga cikin Tabi'ai
Daga cikin su Akwai
👇👇👇👇
1- Abu ja'afar Al-madany ( Qari'i na 8 Daga cikin القراء العشرة)
2- Abdulrahman ibn Hurmuz Al-A'araj
3- Shaibah ibn Nisah
4- muslim ibn Jundub Al-huzali
5- Yazidu Ibn Ruman
6- Salih ibn khuwat
7- Al-asbag ibn Abdulazeez Al-nahwi
8- Al-zuhri muhammad ibn muslim ibn Shihab
9- Abdulrahman ibn Qasim Ibn muhammad ibn Abubakar Assiddiq
wannan itace Silsilar Qira'ar Al-imam Nafi'u Har zuwa Ga Annabi صلى الله عليه وسلم
Al-imam Nafi'u yayi Karatun Qurani Ga Abu ja'afar Al-madany ( Qari'i na 8 Daga cikin القراء العشرة) da kuma Abdulrahman ibn Hurmuz Al-A'araj, da kuma Shaibah ibn Nisah, da kuma muslim ibn Jundub Al-huzali, Da kuma Yazidu Ibn Ruman,
Duka Wadannan Biyar da na Jero sunayensu a sama Sunyi karatu A wurin Sayyidina Abu Hurairah رضي الله عنه da kuma Abdullahi ibn Abbas رضي الله عنهما da kuma Abdullahi Ibn Ayyash, Daga ubayyu ibn Ka'ab رضي الله عنه . Shi kuma Ubayyu Yayi Karatu Ga Annabi صلى الله عليه وسلم
3-MAGANAR MALAMAI AKAN AL-IMAM NAFI'U
Malamai Daban Daban-daban magabata Sunyi Maganganu da dama gameda Al-imam Nafi'u
Ga kadan Daga Cikinsu
👇👇👇👇
IBN MUJAHID YACE : " Al-imam Nafi'u shine ya kasance Shugaban Masu Karatun Qurani A garin Madinah bayan Wucewar Tabi'ai" ya kara da cewa " Al-imam Nafi'u ya kasance masani a fannin Ilimin QIRA'AT, ya kasance mai biya akan Tafarkin magabata( Sahabbai Da Tabi'ai) na garin Madinah.
SA'ID IBN MANSUR YACE: Naji Malik dan Anas Yana Cewa Qira'ar mutanen madinah Sunnah ce, sai aka tambayeshi: Qira'ar Nafi'u yake nufi? Yace Eh.
ABDULLAHI IBN AHMAD IBN HAMBAL YACE: Na tambayi babana ( Ahmad bn Hambal) Wace Qira'a Tafi Soyuwa Agareka? Sai yace: Qira'ar mutanen Madinah, sai nace dashi, Bayan ita kuma fa? Sai yace: Qira'ar Asim.
QALOON YACE : Nafi'u ya kasance Daga cikin mafi tsarkin mutane Halaye na gari, Daga cikin Mafi Iya karatu daga cikin mutane, Haka kuma ya kasance mai Zuhudu kuma mai yawan kyauta, Ya yi Limanci A masallacin Annabi صلى الله عليه وسلم
Har tsawon Shekaru sittin 60
LAITH IBN SA'AD YACE : Nayi aikin hajji a shekara ta 113 bayan hijra Kuma Nafi'u shine Limamin masallacin Annabi صلى الله عليه وسلم a lokacin.
AL-IMAM MALIK YACE : a lokacin da aka tambayeshi gameda Basmalah sai yace: ku tambayi Nafi'u Domin kowane ilimi ana tambayarshi ga ma'abotanshi, Shi kuma Nafi'u shine Shugaban Mutanen Madinah a wurin Karatun Qurani.
AN HAKAITO CEWA: A lokacin da Ciwon ajali ya kama Nafi'u yayan shi sun nemi yayimusu wasiyyah sai yace dasu
اتقوا الله وأصلحوا ذات بينكم وأطيعوا الله ورسوله إن كنتم مؤمنين
Wato Kuji tsoron Allah Kuyi Sulhu a tsakaninku, kuyi da'a ga Allah da manzonshi idan ku kasance Muminai.
Al-imam Nafi'u ya Rasu a shekara ta 169 Bayan Hijrah Yanada Shekara 99 A duniya.
4- SUWAYE DALIBAN AL-IMAM NAFI'U?
An ruwato cewa Al-imam Nafi'u yayi shekara Sittin 60 Yana karantar da Qurani, wannan Yasa Dole zai tara Dalibai da yawa kusan ma zaace bazasu lissafu ba
Amma ga wasu daga cikin Daliban shi
1- Qalun
2- warsh
3- Isah ibn wardan ( Rawin Abu jaafar)
4- Sulaiman ibn jammaz( Rawin Abu jaafar)
5- malik bn Anas
6-khalid bn makhlad
7- Abdullahi bn wahab
8- Lais bn sa'ad
9- Ash'hab bn Abdulazeez
10- Musa bn DariQ
Da dai sauransu
5- TAKAITACCEN BAYANI AKAN QIRA'AR AL-IMAM NAFI'U
Qira'ar Nafi'u haka Take kamar sauran Qira'o'i Akwai wuraren da tayi muwafaqa da wasu Qira'o'in haka kuma akwai wuraren da suka sa6a
Haka kuma Akwai wuraren da QIRA'AR ta ke6anta ta karanta wasu kalmomi da wannan Sigar ma'ana Akwai kalmominda Nafi'u ya Sa6awa kowace Qira'a a wurin karanta su.
Qira'ar Nafi'u Tanada Riwayoyi biyu Kamar sauran Qira'o'i
👇👇👇👇👇
1- Qalun
2-Warsh
Kuma Su biyu Din dukansu sunyi karatu a gareshi Mushafahatan Baki da baki Har ma an riwaito cewa shine ya sakawa QALOON sunan QALOON Haka kuma shi ya sakawa Warsh sunan Warsh.
Ga Kadan daga Cikin Kalmomin da Qira'ar Nafi'u Ta Sa6awa kowace Qira'a a wurin Karantasu
👇👇👇👇
Kalmomin da Nayiwa Wasali su nake nufin ya sabawa sauran Qira'o'i kuma yadda nayi wasalin Haka yake karantawa
👇👇👇👇
1-حتى يَقُولُ الرسول والذين آمنوا معه
2- هل عَسِيتُمْ (سورة البقرة وسورة محمد صلى الله عليه وسلم )
3- قال الله هذا يَوْمَ ينفع الصـدقين صدقهم
4- فنظرة إلى مَيْسُرَةٍ
5- وإن تدعوهم إلى الهدى لا يَتْبَعُوكُمْ
6- ويقول أين شركاءي الذين كنتم تُشَآقُّونِ فيهم
7- والخـمسة أَنْ غَضِبَ اللهُ عليها
8- فأرسله معى رِدًا يصدقني
9- وما تَذْكُرُونَ إلا أن يشاء الله
10- في لوح مَّحْفُوظٌ
Wadannan sune wasu daga Cikin su
Kuma insha Allah zamu tsaya anan Ba don Abunda zaa fada Ya kare ba sai don takaitawa.
JAN HANKALI
👇👇👇👇
Duk wanda Zaiyi sharing ko Kwafi Na wannan Rubutun nawa To ya yi Sharing Dinshi A yadda Na Rubutashi Kar ya kara komai kuma Kar ya canja komai abar shi yadda nayishi
Duk wanda yakeda Taaliki ko gyara Ko shawara ko Mulahaza akan Wannan Rubutun to ya atuntubeni nizan gyara Da kaina Amma Kar A canja Min rubutu.
Ga lambar da zaa tuntubeni da ita +2348034468543
✍️WANDA YA RUBUTA
Habibu Muhammad Shugaba
+2348034468543
Friday
01-11-1442
11-06-2021

RUBUTU NA 1: TARIHIN QARI'AI GOMA 10 DA RIWAYOYINSU 20 | تاريخ القراء العشرة ورواتهم

 TARIHIN QARI'AI GOMA 10 DA RIWAYOYINSU 20

تاريخ القراء العشرة ورواتهم
RUBUTU NA: 1⃣
✍Habibu Muhammad shugaba
ABUBUWAN DA KE KARKASHIN WANNAN RUBUTUN
👇👇👇👇👇
1- Mecece QIRA'AH
2- QIRA'O'I NAWANE AKE KARATU DASU
3- TARIHIN ILIMIN QIRA'AT
4-WANENE QARI'I
5- WANENE RAWI
Duk Abunda muka rubuta mun rubutashi ne a takaice
1- MECECE QIRA'AH
Qira'ah a is'dilahin maluman Qira'at na nufin:- Karatunda aka jinginashi zauwa ga daya Daga cikin shuwagabannin Qira'o'i kamar, Qira'ar Nafi'u, Ibn kathir, Abu Amr, Ibn Amir, Asim, Hamzah, kisa'i, Abu Jaafar, Yakub, Khalaful-Ashir, Ds
Ana cemata Qira'a ne Idan Riwayoyi da Dariqoqin Wannan Qira'ar sunyi imja'i Akan kalmar da ake Magana Akanta.
Misali
وَأَن تَصَّدَّقُوا خَيرٌلَّكُمْ إِن كُنتُم تَعلَمونَ
Sai ace Qira'ar Asim A wannan Kalmar (تَصَّدَّقُوا) Itace A cire shadda ّ Ga harafin ص sai a karanta kamar haka
وَأَن تَصَدَّقُوا خَيرٌلَّكُمْ إِن كُنتُم تَعلَمونَ
Haka kuma
فَنَظِرَةٌ إِلَـى مَيْسَرَة
Sai ace Qira'ar Nafi'u A wannan Kalmar (مَيْسَرَة) Itace Ayi Dwamma ُ Ga Harafin س A karantashi haka
فَنَظِرَةٌ إِلَـى مَيْسُرَة
Da dai sauran Banbance-Banbancen Qira'o'in
Amma idan Riwayoyin Biyu na Qira'ar Sun Sa6a To zaace ne Misali, Riwayar Shu'ubah Daga Asim, ko Riwayar Washu daga Nafi'u da sauransu
2-QIRA'O'I NAWANE AKE KARATU DASU?
Qira'o'i ingantattu da ake Karatu dasu Sune Qira'o'i Goma Gasu a jere kamar haka
👇👇👇👇👇👇👇
1-قِرَاءَةُ نَافع المَدَني
2- قِرَاءَةُ ابن كَثِيرٍ المَكي
3- قِرَاءَةُ أَبِي عَـمْـرو البَصْرِي
4- قِرَاءَةُ ابن عَامِر الشامي
5- قِرَاءَةُ عَاصِمٍ الكُوفِي
6- قِرَاءَةُ حَـــمْـــزَة الكُوفِي
7- قِرَاءَةُ الكسائي الكُوفِي
8- قِرَاءَةُ أَبِي جَعفَر المَدنِـي
9- قِرَاءَةُ يَعْقوبَ الحضرمي البصري
10- قِرَاءَةُ خَـــلَـــف العَاشِر
A karkashin Kowace Qira'a daga cikin wadannan Qira'o'in Akwai Riwayoyi biyu
Gasu kamar haka
👇👇👇👇👇👇
1-قِرَاءَةُ نَافع المَدَني
= رِوايةُ قَالُونُ
= رِوايةُ وَرشٍ
2- قِرَاءَةُ ابن كَثِيرٍ المَكي
= رِوايةُ البَزِّي
= رِوايةُ قُنبُل
3- قِرَاءَةُ أَبِي عَـمْـرو البَصْرِي
= رِوايةُ الدُّورِي عَن أَبِي عَـمْـرو البَصْرِي
=رِوايةُ السُّوسي
4- قِرَاءَةُ ابن عَامِر الشامي
= رِوايةُ هِشَام
=رِوايةُ ابن ذَكوَان
5- قِرَاءَةُ عَاصِمٍ الكُوفِي
= رِوايةُ شُعْبَة
=رِوايةُ حَــفْـصٍ
6- قِرَاءَةُ حَـــمْـــزَة الكُوفِي
= رِوايةُ خَـــلَـــف
=رِوايةُ خَلَّاد
7- قِرَاءَةُ الكسائي الكُوفِي
= رِوايةُ أَبِي الحارث (الليث)
=رِوايةُ الدُّورِي عَن الكسائي
8- قِرَاءَةُ أَبِي جَعفَر المَدنِـي
= رِوايةُ ابن وَرْدان
=رِوايةُ ابن جَمَّاز
9- قِرَاءَةُ يَعْقوبَ الحضرمي البصري
= رِوايةُ رُوَيسٍ
=رِوايةُ رَوْح
10- قِرَاءَةُ خَـــلَـــف العَاشِر
= رِوايةُ إِسْـــحَــاق
=رِوايةُ إِدرِيس
Wadannan Sune Qira'o'i 10 tareda Riwayoyin su a jere
3- TARIHIN ILIMIN QIRA'AT
Wannan ilimin ya samo asali ne Tun daga Zamanin Annabi صلى الله عليه وسلم Domin Shine Ya Koyar da sahabbai yadda Ake Karatun Alqurani mai Girma su kuma suka Karantar Da Almajiransu (tabi' ai) a haka dai Har Karatun yazo Garemu
Kasancewar Larabawa sun Kasu Kashi-Kashi Kabila-kabila Kuma Yadda wasu suke Furta Wasu Haruffa ko wasu Kalmomi ya banbanta da yadda wasu suke furatasu Kuma Shi Qurani an Saukar dashi Ne Akan Haruffa bakwai Duk da cewa Malamai Sunyi Sabani akan menene Cikakkiyar maanar cewa an saukar da Qurani akan Haruffa Bakwai
Wannan ne Yasa Duk sahabin da yazo Koyon Qurani Wurin Manzon Allah صلى الله عليه وسلم Manzon Allah صلى الله عليه وسلم Yana Karantar dashi Qur'ani kamar yadda Kabilar shi suke Furta Kalmomin su
Misali
Wadanda keyin Ibdali ( الإِبدَال) yana koyar dasu Tareda yin Ibdalin
Da sauransu
Idan muka Duba Komu a yarenmu na Hausa Akwai irin Wadannan Banbance-Banbancen a maganar mu
Hausar Sokoto ba daya Take da ta Kano Ba, ta kano Ba daya take da ta Zamfara Ba Da dai sauransu
To haka dai abun Yata tafiya Har zamanin Sayyidina ABUBAKAR akazo wurin Rubuta Qur'ani aka Rubuta shi tareda Wadannan karatukan daban daban da Manzon Allah صلى الله عليه وسلم ya koyar da sahabbai duk da cewa an Rubuta QURANIN ne a hade Wuri daya Amma ya kunshi Duk wadannan Fuskokin.
Haka Sahabbai suka Cigaba da Koyar da Qurani kowa Yana karatu da karantar Da Qurani ne yadda Manzon Allah صلى الله عليه وسلم ya koyar dashi
Har Zamanin Sayyidina USMAN a wannan Lokacin Musulunci ya samu karbuwa a wurare Daban-daban Sai wata Qadiyya ta Faru A wurin wani yaki Da ake kira YAKIN ARIMINIYA Har takai Sashen musulmi suna Aibata sashe suna cewa Basu Iya Karatu ba Suna 6ata Qur'ani, Abun Dai Har Ya kusa yasa Suyi Fada t a tsakanin su.
Wannan Ne yasa Sayyidina HUZAIFAH (صَاحب السِّر) رضي الله عنه Ya ba Sayyidina USMAN رضي الله عنه Shawara cewa A rubuta Qur'ani Da Dukkan Fuskokinshi Yadda Kowa zai karanta Shi ta hanyar Da Manzon Allah صلى الله عليه وسلم ya koyar da Sahabai
Haka kuwa akayi Aka RUBUTA wadannan Qur'anan Dauke Da Dukkanin Fuskokin da har yanzu da su Muke Karatu
Wannan Rubutun da Akayi Shine Ake Kira da الرسم العثماني wato Rubutun Sayyidina Usman رضي الله عنه
Aka rarraba Kwafi Na Wadannan Qur'anan a kasashe Da suka Shahara Da karatun Qurani a wancen Lokacin
Ga kasashen
1-Madina kwafi 2 daya Na Sayyidina Usman Daya Na sauran Al-umar gari
2- makkah
3- kasar Sham
4- kasar Kufa
5- kasar Basra
Daga nan kuma baa sake samun Sabani ba
Har Allah ya kawo lokacin da zaa ke6ance Kowace Qira'ah Da Qari'in ta Da kuma Rawin ta
Kafin Wannan Lokacin Riwayoyin sun yawaita sosai Amma Cikin iyawar Allah masu Tacewa da Tantancewa Sukazo suka dubi kowace Riwaya Suka Fitar da Mutun daya Da ya iyata sosai Wanda kuma an shede shi da tsroron Allah da kuma Tsantseni da Gudun Duniya
Misali
NAFI'U Yanada Dalibai masu Yawa da azako tacewa sai aka Zabi Qalun da warshu
Asim yanada Dalibai da yawa shima Da akazo Fitarwa aka zabi Shu'ubah Da Hafsu
Wadansu Ma idan Anzo ba Daliban Qari'in Ake Zaba Ba sai dai a zabi Dabilan- Dalibanshi koma na kasa dasu
Kamar Abu Amr DURY DA SUSI basuyi karatu kai tsaye Ga Abu amr Ba
SHI Abu amr ya karantar da يَحيَى اليَزِيدِيّ NE su kuma suka karba gareshi
Amma da akazo tacewa da zabe sai aka zabesu
Shine الإمام الشاطبي yake cewa
أَفَاضَ على يَحيَى اليَزِيدِيّ سَيبَه
فَأَصبَحَ بالعَذبِ الفُرَاتِ مُعَللا
Kamar Hamza Khalaf Da Khallad basuyi Karatu Kai tsaye Gareshi ba Sunyi karatu ne Ga Dalibin Hamza Wanda ake Kira سُلَيْم
Amma da akazo tacewa da zabe sai aka zabesu
Shine الإمام الشاطبي yake cewa
رَوَى خَـــلَـــف عنه وخلاد الذي
رواه سُلَيْم مُتقَنًا وَمحصلا
Wannan shine Dan Takaitaccen Tarihin Ilimin QIRA'AT
4- WANENE QARI'I?
QARI'U :- A is'dilahin Maluman Qiraat Shine wanda ake Jingina Daya Daga Cikin Riwayoyin Qurani zuwa Gareshi
Misali
قِرَاءَةُ نَافع
Ana Jingina Riwayoyi biyu Zuwaga Nafi'u Sune QALOON DA WARSH Sai ace
رِوايةُ قَالُونُ عن نَافع
رِواية وَرشٍ عن نَافع
Bayanin wannan Ya Gabata
5- WANENE RAWI?
RAWI :- Shine wanda Ake yin Karatu Da riwayar da ya Riwaito daga Daya daga cikin QARI'AI, kuma shine Ake jinginawa zuwa ga Qari'i.
Misali
رِوايةُ شُعْبَة عَن عاصم
رِوايةُ البَزِّي عَن ابن كَثِيرٍ المَكي
رِواية خَـــلَـــف عن حمزة
رِواية هشام عن ابن عامر
Da dai sauransu
Anan Zan Tsaya Insha Allah
Rubutan mu na Gaba Zai Soma Ne Da TARIHIN wadannan Qira'o'in da Riwayoyin su daya bayan Daya insha Allah
JAN HANKALI
👇👇👇👇
Duk wanda Zaiyi sharing ko Kwafi Na wannan Rubutun nawa To ya yi Sharing Dinshi A yadda Na Rubutashi Kar ya kara komai kuma Kar ya canja komai abar shi yadda nayishi
Duk wanda yakeda Taaliki ko gyara Ko shawara ko Mulahaza akan Wannan Rubutun to ya atuntubeni nizan gyara Da kaina Amma Kar A canja Min rubutu.
Ga lambar da zaa tuntubeni da ita +2348034468543
✍️WANDA YA RUBUTA
Habibu Muhammad Shugaba
+2348034468543
Thursday
29-10-1442
10-06-2021