Monday, 14 March 2022

RUBUTU NA 1: TARIHIN QARI'AI GOMA 10 DA RIWAYOYINSU 20 | تاريخ القراء العشرة ورواتهم

 TARIHIN QARI'AI GOMA 10 DA RIWAYOYINSU 20

تاريخ القراء العشرة ورواتهم
RUBUTU NA: 1⃣
✍Habibu Muhammad shugaba
ABUBUWAN DA KE KARKASHIN WANNAN RUBUTUN
👇👇👇👇👇
1- Mecece QIRA'AH
2- QIRA'O'I NAWANE AKE KARATU DASU
3- TARIHIN ILIMIN QIRA'AT
4-WANENE QARI'I
5- WANENE RAWI
Duk Abunda muka rubuta mun rubutashi ne a takaice
1- MECECE QIRA'AH
Qira'ah a is'dilahin maluman Qira'at na nufin:- Karatunda aka jinginashi zauwa ga daya Daga cikin shuwagabannin Qira'o'i kamar, Qira'ar Nafi'u, Ibn kathir, Abu Amr, Ibn Amir, Asim, Hamzah, kisa'i, Abu Jaafar, Yakub, Khalaful-Ashir, Ds
Ana cemata Qira'a ne Idan Riwayoyi da Dariqoqin Wannan Qira'ar sunyi imja'i Akan kalmar da ake Magana Akanta.
Misali
وَأَن تَصَّدَّقُوا خَيرٌلَّكُمْ إِن كُنتُم تَعلَمونَ
Sai ace Qira'ar Asim A wannan Kalmar (تَصَّدَّقُوا) Itace A cire shadda ّ Ga harafin ص sai a karanta kamar haka
وَأَن تَصَدَّقُوا خَيرٌلَّكُمْ إِن كُنتُم تَعلَمونَ
Haka kuma
فَنَظِرَةٌ إِلَـى مَيْسَرَة
Sai ace Qira'ar Nafi'u A wannan Kalmar (مَيْسَرَة) Itace Ayi Dwamma ُ Ga Harafin س A karantashi haka
فَنَظِرَةٌ إِلَـى مَيْسُرَة
Da dai sauran Banbance-Banbancen Qira'o'in
Amma idan Riwayoyin Biyu na Qira'ar Sun Sa6a To zaace ne Misali, Riwayar Shu'ubah Daga Asim, ko Riwayar Washu daga Nafi'u da sauransu
2-QIRA'O'I NAWANE AKE KARATU DASU?
Qira'o'i ingantattu da ake Karatu dasu Sune Qira'o'i Goma Gasu a jere kamar haka
👇👇👇👇👇👇👇
1-قِرَاءَةُ نَافع المَدَني
2- قِرَاءَةُ ابن كَثِيرٍ المَكي
3- قِرَاءَةُ أَبِي عَـمْـرو البَصْرِي
4- قِرَاءَةُ ابن عَامِر الشامي
5- قِرَاءَةُ عَاصِمٍ الكُوفِي
6- قِرَاءَةُ حَـــمْـــزَة الكُوفِي
7- قِرَاءَةُ الكسائي الكُوفِي
8- قِرَاءَةُ أَبِي جَعفَر المَدنِـي
9- قِرَاءَةُ يَعْقوبَ الحضرمي البصري
10- قِرَاءَةُ خَـــلَـــف العَاشِر
A karkashin Kowace Qira'a daga cikin wadannan Qira'o'in Akwai Riwayoyi biyu
Gasu kamar haka
👇👇👇👇👇👇
1-قِرَاءَةُ نَافع المَدَني
= رِوايةُ قَالُونُ
= رِوايةُ وَرشٍ
2- قِرَاءَةُ ابن كَثِيرٍ المَكي
= رِوايةُ البَزِّي
= رِوايةُ قُنبُل
3- قِرَاءَةُ أَبِي عَـمْـرو البَصْرِي
= رِوايةُ الدُّورِي عَن أَبِي عَـمْـرو البَصْرِي
=رِوايةُ السُّوسي
4- قِرَاءَةُ ابن عَامِر الشامي
= رِوايةُ هِشَام
=رِوايةُ ابن ذَكوَان
5- قِرَاءَةُ عَاصِمٍ الكُوفِي
= رِوايةُ شُعْبَة
=رِوايةُ حَــفْـصٍ
6- قِرَاءَةُ حَـــمْـــزَة الكُوفِي
= رِوايةُ خَـــلَـــف
=رِوايةُ خَلَّاد
7- قِرَاءَةُ الكسائي الكُوفِي
= رِوايةُ أَبِي الحارث (الليث)
=رِوايةُ الدُّورِي عَن الكسائي
8- قِرَاءَةُ أَبِي جَعفَر المَدنِـي
= رِوايةُ ابن وَرْدان
=رِوايةُ ابن جَمَّاز
9- قِرَاءَةُ يَعْقوبَ الحضرمي البصري
= رِوايةُ رُوَيسٍ
=رِوايةُ رَوْح
10- قِرَاءَةُ خَـــلَـــف العَاشِر
= رِوايةُ إِسْـــحَــاق
=رِوايةُ إِدرِيس
Wadannan Sune Qira'o'i 10 tareda Riwayoyin su a jere
3- TARIHIN ILIMIN QIRA'AT
Wannan ilimin ya samo asali ne Tun daga Zamanin Annabi صلى الله عليه وسلم Domin Shine Ya Koyar da sahabbai yadda Ake Karatun Alqurani mai Girma su kuma suka Karantar Da Almajiransu (tabi' ai) a haka dai Har Karatun yazo Garemu
Kasancewar Larabawa sun Kasu Kashi-Kashi Kabila-kabila Kuma Yadda wasu suke Furta Wasu Haruffa ko wasu Kalmomi ya banbanta da yadda wasu suke furatasu Kuma Shi Qurani an Saukar dashi Ne Akan Haruffa bakwai Duk da cewa Malamai Sunyi Sabani akan menene Cikakkiyar maanar cewa an saukar da Qurani akan Haruffa Bakwai
Wannan ne Yasa Duk sahabin da yazo Koyon Qurani Wurin Manzon Allah صلى الله عليه وسلم Manzon Allah صلى الله عليه وسلم Yana Karantar dashi Qur'ani kamar yadda Kabilar shi suke Furta Kalmomin su
Misali
Wadanda keyin Ibdali ( الإِبدَال) yana koyar dasu Tareda yin Ibdalin
Da sauransu
Idan muka Duba Komu a yarenmu na Hausa Akwai irin Wadannan Banbance-Banbancen a maganar mu
Hausar Sokoto ba daya Take da ta Kano Ba, ta kano Ba daya take da ta Zamfara Ba Da dai sauransu
To haka dai abun Yata tafiya Har zamanin Sayyidina ABUBAKAR akazo wurin Rubuta Qur'ani aka Rubuta shi tareda Wadannan karatukan daban daban da Manzon Allah صلى الله عليه وسلم ya koyar da sahabbai duk da cewa an Rubuta QURANIN ne a hade Wuri daya Amma ya kunshi Duk wadannan Fuskokin.
Haka Sahabbai suka Cigaba da Koyar da Qurani kowa Yana karatu da karantar Da Qurani ne yadda Manzon Allah صلى الله عليه وسلم ya koyar dashi
Har Zamanin Sayyidina USMAN a wannan Lokacin Musulunci ya samu karbuwa a wurare Daban-daban Sai wata Qadiyya ta Faru A wurin wani yaki Da ake kira YAKIN ARIMINIYA Har takai Sashen musulmi suna Aibata sashe suna cewa Basu Iya Karatu ba Suna 6ata Qur'ani, Abun Dai Har Ya kusa yasa Suyi Fada t a tsakanin su.
Wannan Ne yasa Sayyidina HUZAIFAH (صَاحب السِّر) رضي الله عنه Ya ba Sayyidina USMAN رضي الله عنه Shawara cewa A rubuta Qur'ani Da Dukkan Fuskokinshi Yadda Kowa zai karanta Shi ta hanyar Da Manzon Allah صلى الله عليه وسلم ya koyar da Sahabai
Haka kuwa akayi Aka RUBUTA wadannan Qur'anan Dauke Da Dukkanin Fuskokin da har yanzu da su Muke Karatu
Wannan Rubutun da Akayi Shine Ake Kira da الرسم العثماني wato Rubutun Sayyidina Usman رضي الله عنه
Aka rarraba Kwafi Na Wadannan Qur'anan a kasashe Da suka Shahara Da karatun Qurani a wancen Lokacin
Ga kasashen
1-Madina kwafi 2 daya Na Sayyidina Usman Daya Na sauran Al-umar gari
2- makkah
3- kasar Sham
4- kasar Kufa
5- kasar Basra
Daga nan kuma baa sake samun Sabani ba
Har Allah ya kawo lokacin da zaa ke6ance Kowace Qira'ah Da Qari'in ta Da kuma Rawin ta
Kafin Wannan Lokacin Riwayoyin sun yawaita sosai Amma Cikin iyawar Allah masu Tacewa da Tantancewa Sukazo suka dubi kowace Riwaya Suka Fitar da Mutun daya Da ya iyata sosai Wanda kuma an shede shi da tsroron Allah da kuma Tsantseni da Gudun Duniya
Misali
NAFI'U Yanada Dalibai masu Yawa da azako tacewa sai aka Zabi Qalun da warshu
Asim yanada Dalibai da yawa shima Da akazo Fitarwa aka zabi Shu'ubah Da Hafsu
Wadansu Ma idan Anzo ba Daliban Qari'in Ake Zaba Ba sai dai a zabi Dabilan- Dalibanshi koma na kasa dasu
Kamar Abu Amr DURY DA SUSI basuyi karatu kai tsaye Ga Abu amr Ba
SHI Abu amr ya karantar da يَحيَى اليَزِيدِيّ NE su kuma suka karba gareshi
Amma da akazo tacewa da zabe sai aka zabesu
Shine الإمام الشاطبي yake cewa
أَفَاضَ على يَحيَى اليَزِيدِيّ سَيبَه
فَأَصبَحَ بالعَذبِ الفُرَاتِ مُعَللا
Kamar Hamza Khalaf Da Khallad basuyi Karatu Kai tsaye Gareshi ba Sunyi karatu ne Ga Dalibin Hamza Wanda ake Kira سُلَيْم
Amma da akazo tacewa da zabe sai aka zabesu
Shine الإمام الشاطبي yake cewa
رَوَى خَـــلَـــف عنه وخلاد الذي
رواه سُلَيْم مُتقَنًا وَمحصلا
Wannan shine Dan Takaitaccen Tarihin Ilimin QIRA'AT
4- WANENE QARI'I?
QARI'U :- A is'dilahin Maluman Qiraat Shine wanda ake Jingina Daya Daga Cikin Riwayoyin Qurani zuwa Gareshi
Misali
قِرَاءَةُ نَافع
Ana Jingina Riwayoyi biyu Zuwaga Nafi'u Sune QALOON DA WARSH Sai ace
رِوايةُ قَالُونُ عن نَافع
رِواية وَرشٍ عن نَافع
Bayanin wannan Ya Gabata
5- WANENE RAWI?
RAWI :- Shine wanda Ake yin Karatu Da riwayar da ya Riwaito daga Daya daga cikin QARI'AI, kuma shine Ake jinginawa zuwa ga Qari'i.
Misali
رِوايةُ شُعْبَة عَن عاصم
رِوايةُ البَزِّي عَن ابن كَثِيرٍ المَكي
رِواية خَـــلَـــف عن حمزة
رِواية هشام عن ابن عامر
Da dai sauransu
Anan Zan Tsaya Insha Allah
Rubutan mu na Gaba Zai Soma Ne Da TARIHIN wadannan Qira'o'in da Riwayoyin su daya bayan Daya insha Allah
JAN HANKALI
👇👇👇👇
Duk wanda Zaiyi sharing ko Kwafi Na wannan Rubutun nawa To ya yi Sharing Dinshi A yadda Na Rubutashi Kar ya kara komai kuma Kar ya canja komai abar shi yadda nayishi
Duk wanda yakeda Taaliki ko gyara Ko shawara ko Mulahaza akan Wannan Rubutun to ya atuntubeni nizan gyara Da kaina Amma Kar A canja Min rubutu.
Ga lambar da zaa tuntubeni da ita +2348034468543
✍️WANDA YA RUBUTA
Habibu Muhammad Shugaba
+2348034468543
Thursday
29-10-1442
10-06-2021

Monday, 24 January 2022

2022 JIGAWA STATE MUSABAQAH RESULTS

30TH JIGAWA STATE QURANIC RECITATION COMPETITION
2022 JIGAWA STATE MUSABAQAH RESULTS















 30th Session - Jigawa State Qur'anic Recitation Competition

Organized by Islamic Education Bureau, Dutse, Jigawa State. Held at Jigawa State Polytechnic - Dutse - Jigawa State - Nigeria. 13th January, 2022 - 20th January, 2022 36th Nigerian National Quranic Recitation Competition organized by Musabaqah Foundation For Quranic Recitation In Nigeria Centre For Islamic Studies, Usmanu Danfodio University, Sokoto - Nigeria. #Quran #QuranRecitation #QuranMusabaqah #Musabaqah #NationalMusabaqah #NigerianNationalMusabaqah #QuranCompetition #quranrecitationcompetition #nationalquranicrecitationcompetition #nigeria #nigerianquranrecitation #quraninafrica #learnquran #listentoquran #thewordofGod #bookrevealedtoprophetmuhammad القرآن الكريم القرآن الكريم #القران الكريم في نيجيريا#نيجيريا# #jigawastate#jigawamusabaqah#jigawastatemusabaqah#jigawastatquranicrecitationcompetition #qurancompetition

2021 JIGAWA STATE MUSABAQAH RESULTS

 RESULTS FOR THE 29TH JIGAWA STATE QURANIC RECITATION COMPETITION

2021 JIGAWA STATE MUSABAQAH RESULTS

29th Session - Jigawa State Qur'anic Recitation Competition Organized by Islamic Education Bureau, Dutse, Jigawa State. Held at Jigawa State Polytechnic - Dutse - JIgawa State - Nigeria. 4th February, 2021 - 11th February, 2021 36th Nigerian National Quranic Recitation Competition organized by Musabaqah Foundation For Quranic Recitation In Nigeria Centre For Islamic Studies, Usmanu Danfodio University, Sokoto - Nigeria. #Quran #QuranRecitation #QuranMusabaqah #Musabaqah #NationalMusabaqah #NigerianNationalMusabaqah #QuranCompetition #quranrecitationcompetition #nationalquranicrecitationcompetition #nigeria #nigerianquranrecitation #quraninafrica #learnquran #listentoquran #thewordofGod #bookrevealedtoprophetmuhammad القرآن الكريم القرآن الكريم #القران الكريم في نيجيريا#نيجيريا# #jigawastate#jigawamusabaqah#jigawastatemusabaqah#jigawastatequranicrecitationcompetition#qurancompetition #karatunalkurani #karatunalkur'animaigirma #quran #qur'ani #alquran #alqur'an #alqur'ani #alkuran #Koran #alkur'ani














Tarihin Sheikh Dr. Rufa'i Uba Hamza Gabari

    Tarihin Sheikh Dr. Rufa'i Uba Hamza Gabari

Rubutawa: Aminu Aliyu Sakwaya

1988 60 Hizb & Tafsir Winner | Nigerian Musabaqah
An haifi Mallam a shekarar 1968. Ya haddace Alkur'ani mai girma a sati ashirin.
Ya fara karatu a wajen Mallam Alhaji Gabari. Sannan ya ci gaba a hannun Mallam Madi Gabari har ya kammala.
Ya yi satu guda a hannun Mallam Labaran Gadon Kaya.
Ya yi karatun ilimi wajen Mallam Ahmad babban Malami Gabari da magajinsa Mallam Umar Bawa da Mallam Ibrahim Ruwaan Dorawa da Mallam Danlami Darma.
1981 Mallam ya shiga makarantar Ulumuddin a Koki.
1983 Mallam ya shiga S.A.S Kano. Daga cikin malamansa na wannan makaranta akwai Sheikh Kabir Sani Ayagi da Dr. Abbas Yakubu Abbas da Sheikh Dr. Abdulhamid Shu'aib Akaga da Sheikh Habibullah Adam Ilori.
Ya yi karatun ilimin tajwidi wajen Mallam Shehu Sulaiman Adam da Sheikh Sulaiman Khan al-Bakistani da Sheikh Aliy Zahrani al-Su'udiy.
Ilimin tajwidin da Mallam ya samu ne ya karfafa masa gwiwar shiga musabakar Alkur'ani Mai Girma.
MUSABAQAH
1986 - 60 Hizb - Bai samu wuce karamar hukuma ba.
1987 - 60 Hizb - Ya je ta Jaha daga Gumel Zone.
1988 - 60 Hizb da Tafsir - 1st Position a Jaha daga Minjibir.
An yi musabakar kasa a Kano 1988 inda Mallam ya samu nasarar mataki na farko, sai dai wannan shekarar yan Jahar Borno ba su turo yan takararsu ba kwata-kwata, kila sakamakon abinda ya faru a musabakar bara da ta gabata a can Bornon 1987.
1988 KANO REPRESENTATIVES | NIGERIAN NATIONAL MUSABAQAH
Male Participants:
60 Tafsir: Rufa'i Uba Hamza Gabari
60 Hizb: Muhammad Nasiru Yahya Ramadan (ya gama Madina da Sudan mai tafsir a Dutse)
40 Hizb: Muhammad Sani Armaya'u ( Chief Judge National Musabaqah)
20 Hizb: Abdussamad Isma'ila
2 Hizb da Tangimi: Auwalu Gwani Mukhtar
Female Participants:
20 Hizb: A'isha Mahmud Barnoma
10 Hizb: A'isha Muhammad Rabi'u
2 Hizb: Nafisa Isma'il
Kuma alhamdu lillah sai duk suka samu nasarar mataki na farko idan ban da Nafisa Isma'il yar izu biyu inda Fatima Zubair daga Katsina ta lashe kujerar.
Mallam daga nan ya wakilci Najeriya a musabakar duniya ta Sarki Abdul'aziz da ke Saudiyya shekarar 1989 inda ya samu nasarar mataki na shida.
DUBAI INTERNATIONAL HOLY QURAN AWARD
Mallam ne kuma dan Najeriya na farko da yayi wakilci a Musabakar Duniya ta Dubai izu sittin shekarar 1998/1999 inda ya zo na bakwai a karo na biyu da fara musabakar.
A yanzu kuma, kungiyar da Mallam yake shugabanta, Jam'iyyatu Ahlil Quran Fi Najeriya ce ke kai yan takara daga Najeriya zuwa musabakar Dubai, ofishinta na nan a titin B.U.K Old Site.
BAYAN MUSABAKAR DUNIYA 1988
Mallam ya karanta Hidayatil Murid wajen Sheikh Tijjani Rabi'u sannan ya auri Gwarzuwar Shekarar da su ka yi musabaka tare bangaren mata Mallama A'isha Mahmud Barnoma a 1990.
KARATUN ZAMANI
Gwamnatin Kano ta dauki nauyin Mallam inda yayi digiri na farko a Jami'ar Azhar da ke Misra, ya kammala 1995. A nan Jami'ar Mallam ya yi karatun Qira'atil ashr a wajen Sheikh Aliyu Ridha Salim, tare da Gwani Kabir Ya'aqub a saukar farko.
Ya kuma yi karatu wajen Sheikh Abdullah Atiyyah al-Bayyumiy, limami Ratibi a Jam'iar Azhar.
Ya yi babar Diploma a Masar shekarar 2008.
Ya yi digiri na biyu 2013 a Jam'iar Amerika dake Qahirah akan tafsirin Sheikh Muhammad Mutawallah Sha'arawi cikin Suratil Hajj da kuma digiri na uku a Jami'ar Musulunci da ke Malaysia 2018.
Risalarsa ta Ph.D aka mayar littafi (Tatawwur Ilmul Qira'at wal Shu'unil Quraniyya Fi Najeriya.
Littafin na nan ana samunsa a kasuwar Kurmi da kuma wajen Mallam din.
Haka nan Mallam ya yi karatun Diploma a F.C.E Kano da Kano State Polytechnic a matakai daban-daban har zuwa H.N.D.
Yanzu haka Malami ne Sa'adatu Rimi College of Education.
MAJLISIN KARATU
Mallam na karatu bayan Sallar Asuba ranar Jumu'a da Asabar da dalibai Mahaddata Alkur'ani akan ilimin tajwidi da Qira'at da kuma gyaran ada'i.
Wannan majilisi ba shakka ya fitar da zakarun Alkur'ani mai girma gida da wajen Najeriya.
Kamar yadda muka rubuta a tarihin Goni Kabir Ya'aqub, haka ya ke ga Sheikh Dr. Rufa'i Uba Hamza.
Za ka iya cewa daliban musabakar da suka samu nasara to hakika sun samu horo daga wajen Mallam ko kuma daga daliban Mallam.
Haka nan duk yan takarar da suka wakilci Najeriya zuwa musabakar Dubai to sun samu horo wajen Mallam.
Allah Ya saka masa da alheri.
Ga kadan daga cikin mutanen da wannan majisin ya yaye:
Mallam Abdulkadir Datti
Mallam Muhammad Sani Muhammad al-Minshawiy
Dr. Ahmad Tijjani Ramadan
Mallam Aliyu Abdulkadir
Mallam Abdullahi Sulaiman Kabara
Goni Idris Sa'id Alhassan
Goni Abdussamad Salisu Sani Adam
Mallam Ibrahim Muhammad Zakariyya
Mallam Shu'aib Habib Shu'aib
Mallam Munir Sani Inuwa, da mutane da yawa.
Allah Ya karbi aiyukan Mallam, Ya yafe masa laifukansa, Ya kiyayeshi duniya da lahira, Ya kyautata zurriyarsa, Ya kuma azurtashi da kyakkyawar cikawa.
Amin amin.

Video Credit: Ahlul Quran Tv
Rubutu: Tatawwur - Littafin da Malam ya rubuta da sauran takardu

TARIHIN GONI MUHAMMAD KABIR YA'AQUB KANO

TARIHIN GONI MUHAMMAD KABIR YA'AQUB KANO

Rubutawa: Aminu Aliyu Sakwaya

FARKON RAYUWA
An haifeshi a 1966 a unguwar Yan awaki da ke birnin Kano.
Mahaifinsa ya kasance malami, mahaddacin Alkur'ani mai girma.
Ya yi karatu a wajen mahaifinsa da kuma kawunsa Mallam Garba, daga nan ya ci gaba a wajen Mallam Shu'aib dan Ringim bayan rasuwar mahaifinsa.
A 1979 mahaifinsa ya kai shi Maiduguri tsangayar Goni Adam dan Dakaso inda a nan ya kammala haddar Alkur'ani mai girma cikin kananan shekaru.
Daga nan ya shiga makarantun ilimi a nan Maiduri ya ci gaba da neman ilimin addinin musulunci.
Ya koyi ilimin tajwidi a wajen Goni Habu a Maiduguri, inda ya karanta littafin Hidayatul Murid da wasu littafan a wajensa.
MUSABAQA
1987 Borno - Ya yi musabakar izu sittin a ckin kwaryar birnin Maiduguri inda ya yi na uku, da aka hada da sauran kauyuka (kila ta zone) sai ya yi na biyar.
(Bai samu wakilci zuwa Jaha ba).
1987 Kano - Ya dawo gida hutu bayan kammala musabakar Borno, a Kano kuma lokacin ba a gama musabaka ba. Ya yi musabakar izu sittin a kwaryar birnin Kano inda ya yi na biyu a matakin karamar hukuma Kano Municpal.
1st: Gwani Nasir Abdullahi
2nd: Goni Kabir Ya'aqub
3rd: Gwani Lawi Gwani Dan Zarga
A MATAKIN JAHA KUMA:
1st: Gwani Nasiru Abdullahi
2nd: Sheikh Ja'afar Mahmud Adam
3rd:Gwani Lawi Gwani Dan Zarga
4th: Goni Kabir Ya'aqub
1988 - Kano - Ya sake na hudu a matakin Jaha
1989 Kano - Ya yi na daya a matakin Jaha
WADANDA SUKA WAKILCI KANO A WANNAN SHEKARAR A MUSABAKAR KASA A BAUCHI SU NE:
60 da Tafsiri: Sheikh Alkali Jibril Muhammad Mustapha Birnin Kudu
60 Hizb: Goni Kabir Ya'qub
40 Hizb: Goni Muhammad Khamis Umar
20 Hizb: Goni Abdul'aziz Hussain Akarami
10 Hizb: Mallam Auwal Abdulmumin
2 Hizb : Mallam Muhammad Tijjani Lawan
BANGAREN MATA:
Gwana Karimatu Sahalu - 30 Hizb
Maryam Ibrahim Kafin Hausa - Allah Ya mata rahama
Rumasa'u Shehu Ibrahim.
MUSABAKAR KASA A BAUCHI 1990
A matakin kasa, sai Mallam Jibril Muhammad Mustapha da Goni Kabir Ya'aqub suka samu nasarar mataki na daya, izu sittin da tafsir (Gwarzon Shekara) da izu sittin kenan. Sai dai ba su samu wakiltar Najeriya a musabakar duniya da ke Saudiyya ba sakamakon fara yakin tekun Fasha (Gulf War).
1ST POSITIONS WINNERS - 1990 BAUCHI NATIONAL MUSABAQAH
60 Hizb & Tafseer: Jibril Muhammad Mustapha Kano State
60 Hizb: Muhammad Kabir Ya'aqub Kano State
40 Hizb: Alghali Bishara Borno State
20 Hizb: Khamis Balarabe Plateau State - Allah Ya masa rahama
10 Hizb: Nasir Abdurrahman Funtua Katsina State
ALKALANCIN MUSABAQA
1998 - An nada shi alkalin musabakar a Jahar Kano a matakin kananan hukumomi
2003-2007: Ya yi alkalanci a musabakar kasa ta Najeriya bangaren maza
2007 - An zabeshi daga Najeriya inda ya yi alkalanci a musabakar duniya ta Sarki Abdul'aziz da ake gabatarwa a Saudiyya duk shekara.
NADIN GONI
2007 - Goni Abdullahi Borno ya nada shi Goni daga shawarin malaminsa Goni Adam dan Dakaso.
KARATUN QIRA'AT
Alhaji Ado Dan Dawaki ya dauki nauyinsa inda ya tafi Misra ya yi karatun Qira'at a wajen Sheikh Ridha Salim shekara daya.
Ya samu International Scholarship karkashin Gwamnar Jahar Kano na mulkin soja Kanar Idris Garba inda ya koma Misra ya shekara uku a Ma'ahad Qira'at bangaren Aliyat-Qira'at, ya kuma samu ijaza a Qira'o'i goma wajen Sheikh Saleem Ridha.
KARATUN ZAMANI
2010 - Ya kammala N.C.E a Sa'adatu Rimi College of Education, Kano
2013 - 2017: B.Ed Islamic Education - Northwest University, Kano
2019 2021: Master's Degree - Islamic Studies - Bayero University, Kano
2021 - Date - Ya fara Ph.D a Bayero University, Kano
MAJALISIN KARANTARWA
Babban majlisin da ake koyon karatun Alkur'ani da Ada'i da Qira'at da tadribin yan musabaqah dake unguwar Dorayi cikin birnin Kano.
Duk Asabar da Lahadi bayan sallar Asuba Goni Kabir na karantarwa a wannan majalisi - Allah Ya saka masa da alheri.
WASU DAGA CIKIN TSOFFIN MAHALARTA WANNAN MAJALISI
Zai yi wuya ka samu mutum daya da ya kasance zakara a musabaqar Jahar Kano da kuma kewayenta face Goni Kabir ya karantar da shi, ko kuma daliban Goni Kabir sun karantar da shi.
Lalle mafiya kyawun karatun Alkur'ani a Kano da kuma kewayanta za ka samu sun fa'idanta da kwarewa da baiwa da gogewa da iya karatu da rerawa da kuma kyan ada'i da Qira'at da Allah Yai wa Goni Kabir Ya'aqub.
Ana daukarsa Jaha-Jaha domin ya yi wa dalibai da yan musabaqah tadribi na yadda ake karatun Alkur'ani mai girma.
Ga wasu daga cikin zakaru a musabakar Alkurani mai girma da wannan majalisi ya yaye;
Mazidu Adam Shu'aib - Gwarzon Shekara 2003 Nasarawa
Zubair Hamza Dahir - Gwarzon Shekara 2005 Kano
Kabir Abubakar Musa - Gwarzon Shekara da Duniya 2013 Zamfara
Jamilu Lawan - 2004 Kebbi 40 Hizb 1st
Aminu Hassan - 2009 Edo 60 Hizb 1st
Mukhtar Barnoma - Gwarzon Shekara 2009 Edo
Idris Abdulkadir - 2006 Bauchi 60 Hizb 1st
Shamsu Lawan - 2007 -40H-2nd | 2010 -60H-5th | 2014-Tafsir-4th | Kuwait
Abdullahi Aliyu - 2013 Zamfara 60 Hizb - 1st
Mulkhtar Umar
Faruq Goni Kabir Ya'aqub - Ya sha wakiltar Kano a musabakar kasa
Da sauran dubunnan mutane.
Allah Ya sakawa Mallam da alheri Ya karbi aiyukansa na alkhairi Ya kyautata bayansa.

Littafin da aka duba: Littafin Tatawwur na Dr. Rufa'i Uba Hamza Gabari da sauran takardun bincike