Tarihin Sheikh Dr. Rufa'i Uba Hamza Gabari
Rubutawa: Aminu Aliyu Sakwaya
1988 60 Hizb & Tafsir Winner | Nigerian Musabaqah
An haifi Mallam a shekarar 1968. Ya haddace Alkur'ani mai girma a sati ashirin.
Ya fara karatu a wajen Mallam Alhaji Gabari. Sannan ya ci gaba a hannun Mallam Madi Gabari har ya kammala.
Ya yi satu guda a hannun Mallam Labaran Gadon Kaya.
Ya yi karatun ilimi wajen Mallam Ahmad babban Malami Gabari da magajinsa Mallam Umar Bawa da Mallam Ibrahim Ruwaan Dorawa da Mallam Danlami Darma.
1981 Mallam ya shiga makarantar Ulumuddin a Koki.
1983 Mallam ya shiga S.A.S Kano. Daga cikin malamansa na wannan makaranta akwai Sheikh Kabir Sani Ayagi da Dr. Abbas Yakubu Abbas da Sheikh Dr. Abdulhamid Shu'aib Akaga da Sheikh Habibullah Adam Ilori.
Ya yi karatun ilimin tajwidi wajen Mallam Shehu Sulaiman Adam da Sheikh Sulaiman Khan al-Bakistani da Sheikh Aliy Zahrani al-Su'udiy.
Ilimin tajwidin da Mallam ya samu ne ya karfafa masa gwiwar shiga musabakar Alkur'ani Mai Girma.
MUSABAQAH
1986 - 60 Hizb - Bai samu wuce karamar hukuma ba.
1987 - 60 Hizb - Ya je ta Jaha daga Gumel Zone.
1988 - 60 Hizb da Tafsir - 1st Position a Jaha daga Minjibir.
An yi musabakar kasa a Kano 1988 inda Mallam ya samu nasarar mataki na farko, sai dai wannan shekarar yan Jahar Borno ba su turo yan takararsu ba kwata-kwata, kila sakamakon abinda ya faru a musabakar bara da ta gabata a can Bornon 1987.
1988 KANO REPRESENTATIVES | NIGERIAN NATIONAL MUSABAQAH
Male Participants:
60 Tafsir: Rufa'i Uba Hamza Gabari
60 Hizb: Muhammad Nasiru Yahya Ramadan (ya gama Madina da Sudan mai tafsir a Dutse)
40 Hizb: Muhammad Sani Armaya'u ( Chief Judge National Musabaqah)
20 Hizb: Abdussamad Isma'ila
2 Hizb da Tangimi: Auwalu Gwani Mukhtar
Female Participants:
20 Hizb: A'isha Mahmud Barnoma
10 Hizb: A'isha Muhammad Rabi'u
2 Hizb: Nafisa Isma'il
Kuma alhamdu lillah sai duk suka samu nasarar mataki na farko idan ban da Nafisa Isma'il yar izu biyu inda Fatima Zubair daga Katsina ta lashe kujerar.
Mallam daga nan ya wakilci Najeriya a musabakar duniya ta Sarki Abdul'aziz da ke Saudiyya shekarar 1989 inda ya samu nasarar mataki na shida.
DUBAI INTERNATIONAL HOLY QURAN AWARD
Mallam ne kuma dan Najeriya na farko da yayi wakilci a Musabakar Duniya ta Dubai izu sittin shekarar 1998/1999 inda ya zo na bakwai a karo na biyu da fara musabakar.
A yanzu kuma, kungiyar da Mallam yake shugabanta, Jam'iyyatu Ahlil Quran Fi Najeriya ce ke kai yan takara daga Najeriya zuwa musabakar Dubai, ofishinta na nan a titin B.U.K Old Site.
BAYAN MUSABAKAR DUNIYA 1988
Mallam ya karanta Hidayatil Murid wajen Sheikh Tijjani Rabi'u sannan ya auri Gwarzuwar Shekarar da su ka yi musabaka tare bangaren mata Mallama A'isha Mahmud Barnoma a 1990.
KARATUN ZAMANI
Gwamnatin Kano ta dauki nauyin Mallam inda yayi digiri na farko a Jami'ar Azhar da ke Misra, ya kammala 1995. A nan Jami'ar Mallam ya yi karatun Qira'atil ashr a wajen Sheikh Aliyu Ridha Salim, tare da Gwani Kabir Ya'aqub a saukar farko.
Ya kuma yi karatu wajen Sheikh Abdullah Atiyyah al-Bayyumiy, limami Ratibi a Jam'iar Azhar.
Ya yi babar Diploma a Masar shekarar 2008.
Ya yi digiri na biyu 2013 a Jam'iar Amerika dake Qahirah akan tafsirin Sheikh Muhammad Mutawallah Sha'arawi cikin Suratil Hajj da kuma digiri na uku a Jami'ar Musulunci da ke Malaysia 2018.
Risalarsa ta Ph.D aka mayar littafi (Tatawwur Ilmul Qira'at wal Shu'unil Quraniyya Fi Najeriya.
Littafin na nan ana samunsa a kasuwar Kurmi da kuma wajen Mallam din.
Haka nan Mallam ya yi karatun Diploma a F.C.E Kano da Kano State Polytechnic a matakai daban-daban har zuwa H.N.D.
Yanzu haka Malami ne Sa'adatu Rimi College of Education.
MAJLISIN KARATU
Mallam na karatu bayan Sallar Asuba ranar Jumu'a da Asabar da dalibai Mahaddata Alkur'ani akan ilimin tajwidi da Qira'at da kuma gyaran ada'i.
Wannan majilisi ba shakka ya fitar da zakarun Alkur'ani mai girma gida da wajen Najeriya.
Kamar yadda muka rubuta a tarihin Goni Kabir Ya'aqub, haka ya ke ga Sheikh Dr. Rufa'i Uba Hamza.
Za ka iya cewa daliban musabakar da suka samu nasara to hakika sun samu horo daga wajen Mallam ko kuma daga daliban Mallam.
Haka nan duk yan takarar da suka wakilci Najeriya zuwa musabakar Dubai to sun samu horo wajen Mallam.
Allah Ya saka masa da alheri.
Ga kadan daga cikin mutanen da wannan majisin ya yaye:
Mallam Abdulkadir Datti
Mallam Muhammad Sani Muhammad al-Minshawiy
Dr. Ahmad Tijjani Ramadan
Mallam Aliyu Abdulkadir
Mallam Abdullahi Sulaiman Kabara
Goni Idris Sa'id Alhassan
Goni Abdussamad Salisu Sani Adam
Mallam Ibrahim Muhammad Zakariyya
Mallam Shu'aib Habib Shu'aib
Mallam Munir Sani Inuwa, da mutane da yawa.
Allah Ya karbi aiyukan Mallam, Ya yafe masa laifukansa, Ya kiyayeshi duniya da lahira, Ya kyautata zurriyarsa, Ya kuma azurtashi da kyakkyawar cikawa.
Amin amin.
Video Credit: Ahlul Quran Tv
Rubutu: Tatawwur - Littafin da Malam ya rubuta da sauran takardu
No comments:
Post a Comment