TAKAITACCEN TARIHIN MUSABAKAR SHEIKH JA'AFAR MAHMUD ADAM KANO ( Rahimahullah)
Kafin mai karatu ya fara karantawa ya kamata ya san mai wannan rubutu ba masanin tarihi ba ne, mai binckike ne kawai akan harkar Musabaka. Sannan ya yi amfani da laccocin Mallam Ja'afar da Maganganun wasu Malaman Qur'ani kamar Gwani Yahuza Gwani Dan Zarga Kano da kuma littafai da aka rubuta. Wasu daga cikin littafan sun hada da ' Tatawwur ilmul Qira'at da Dr. Rufa'i Uba Hamza Gabari da kuma Ayyami na Dr. Muhammad Sani Rijiyar Lemo' wadanda suka kawo tarihin rayuwar Mallam Ja'afar.
Don haka mai rubutu ba ra'ayinsa yake kawowa ba.
Don Allah duk inda aka ga kuskure amanar ilimi ce a gyara. Don haka kada mutum ya yi shiru.
Abinda yake daidai kuwa to daga Allah ne.
Allah Ya ba mu ikon rubutawa daidai tare da ikhlasi.
Kafin mu fara kada mu manta Mallam Ja’afar Alaramma ne, Gwani ne a karatun Alkur’ani. Ya yi haddarsa da allo, kuma ya yi satu ba daya ba biyu ba a nan Fagge dake Kano a wajen Alaramma Dawud 1977 zuwa 1978.
An haifeshi a 1962 ko 1965.
Ya koyi Tajwidi a hannun wani Malami mutumin Misra Sheikh Abdul’aziz ali AlMustafa.
Da sunan Allah Mai Rahama Mai jin kai.
MUSABAKAR KASA TA FARKO 1986
Gwani Rufa'i ya kawo cewar a Musabakar Kasa ta farko wacce aka gudanar a Sakkwato 1986 Mallam Ja'afar yana daga cikin mutum ukun da suka wakilci Kano a izu sittin wanda shi ne kololuwar mataki a wancan lokacin tunda ba bu sittin da tafsiri. To a wannan lokaci Mallam Ja'afar sai yai na hudu a matakin Kasa kamar yadda Gwani Rufa'i ya fada a shafi na 699. Sai dai a shafi na 683 sunan Mallam Ja'afar ya zo a na biyar. Yayinda yan takarar Borno su ka zo na biyu, da na uku, da na hudu; su ne Idris Isa Idris, Sharif Dahir Musa da kuma Muhammad Dungus. Mallam Ja'afar kuma yazo na biyar daga Kano sai Marigayi Gwani Aminu Zaina ya zo na daya daga Kano. Gwani Aminu Zaina da Goni Idris Isa Idris su suka wakilci Nigeria a Musabakar Malik Abdul'aziz a Saudiyya sai dai sun je a makare, ba su samu damar sharakawa ba - kamar yadda Gwani Rufa'i ya kawo a 696 da 697.
MUSABAKAR KASA TA BIYU 1987
To a shekarar da ta gewayo, 1987, sai Mallam Ja'afar ya sake fafata Musabaka inda ya yi na biyu a Jahar Kano. Yayin da Gwani Nasiru Abdullahi Musa Kibiya ya yi na farko.
Wannan ya ba wa Mallam Ja’afar damar shiga cikin sahun mutane uku da za su wakilci Kano a Musabakar Kasar da za a gabatar a Maiduguri. Cikin ikon Allah da rahamarSa da zabinSa sai Mallam Ja'afar ya zo na daya yayinda yan takarar Borno suka zo na biyu da na uku. Daya daga cikin yan takarar Jahar Kano kuma sai ya zo na hudu, yayinda dayan dan takarar Borno ya zo na biyar. Yan takarar Bornon su ne Goni Jidda Muhammad Khalil (na biyu) da Goni Wali Ibrahim Kolomi (na uku) sai kuma Goni Jibril Haruna Abdullahi (na biyar). Dan takarar Jahar Kanon kuma shi ne Gwani Nasiru Abdullahi Musa ( na hudu).
To kaddarar Allah idan ta zo ba makawa sai ta faru. Wannan sakamako bai yi wa mutanen Borno dadi ba. To dama shi sakamako ba ya nuna wani ya fi wani. Akwai wanda ya san wane da wane sun fi shi karatu nesa ba kusa ba, to amma sai Allah Ya ba shi nasara a Musabaka bai ba wa wancan ba.
Saboda yan mintina ne kwata kwata ba su wuce ashirin mutum zai zo yai karatu. Wani ya tashi da danjoji da yawa wani kuma da danjoji kadan yayin da wani ya tashi ba ko danja daya!
Allah Ya na zabar wanda ya so cikin takara ya ba shi nasara ba don ya fi saura ba. A'a sai don dalilin da shi Allah din ya barwa kansa sani. Sannan Allah na iya zabar mutum Ya ba shi nasara domin Ya jarrabashi Ya ga ko zai yi takama da ji-ji da kai da girman kai ko ya rena mutane ko yana jin ya fi kowa karatu. Sannan Allah na jarrabar mutum kuma da rashin samun matsayi a Musabaka don ya ga ya ya zai yi? Zai ce wane da wane ne suka ka da ni ko kuma ya ce Allah ba ya sonsa ko ya kamata a ce shi yai na daya tunda ya fi saura karatu.
Shi ya sa ake son yan takara su kara sanya ikhlasi cikin karatunsa.
Allah Ya ba mu ikhlashi gaba daya.
To mu dawo maganar Sheikh Ja'afar rahimahullah.
Sakamakon musabakar 1987 bai yi mutanen Borno dadi ba. Wanna ta sanya hukumar Musabakar Borno fushi tare da kin shiga Musabakar da aka yi a shekarar da ta zagayo, 1988, a Kano.
( Hira da Gwani Yahuza Gwani Saleh dan Zarga da Goni Umar Al-Bashiri a tashar Talabijin ta Wisal Hausa Tv ).
Wannan kuma na iya shiga cikin dalilan da ya sanya lokacin da Mallam Ja'afar ya kammala Jami'ar Musulunci ta Madina a 1993 ya zo Borno a 1995 domin fara gabatar da Tafsiri a Masallacin Mallam Muhammad Indimi tasa ya hadu da kalubale da adawa mai yawa daga wasu daga cikin mutane da kuma malaman Borno (Sufaye) musamman idan sun tuna cewar shi ne fa kuma ya zo har gidansu ya lashe Musabakar, ga shi yanzu ya dawo yana kalubalantarsu da hujjoji.
Jama'a ku biyo mu in sha Allahu za mu sanya muku maganar Mallam Ja'afar da yake ba da labarin gaggan Malamai guda uku wanda ba bu ya su a Borno su ka je har wajen Abacha domin a hana shi Tafsiri - bayan sun je har wajen Gwamna ba su gamsu ba.
Dr. Gwani Rufa'i ya kawo cewar Mallam Ja'afar na yin Musabaka ne a wancan lokaci da salo irin na Sheikh Mahmud Khalil al-Husari - yayin da yan takabara ke kabbara saboda zalakar muryarsa.
MUSABAKAR DUNIYA TA SARKI ABDUL'AZIZ DAKE SAUDIYYA 1988
Sakamakon Musabakar Kasa ya nuna na daya da na biyu wato Sheikh Ja'afar da Goni Jidda Muhammad Khalil su za su wakilci Najeriya a Musabakar Duniya. To amma kamar muka kawo a sama mutanen Borno sun yi fushi don haka ba su yarda Goni Jidda ya wakilci Najeriya ba.
Wasu kuma na ganin Jami'ar Danfodio ya hana shi tafiya Musabakar Duniya saboda irin yanayi da kuma halin da kwamitin Jahar Borno ya nuna na kin amincewa da sakamakon Musabakar ta 1987.
To wanda yai na uku ma dan Borno ne wato Goni Wali Ibrahim Kolomi don haka ba za su yarda Cibiyar nazarin Addinin Musulunci ta Jami'ar Usmanu Dan Fodio dake Sakkwato (wanda sune suke gudanar da Musabakar) ta dauko shi ba.
A dalilin haka ya sanya Dan Fodio dauko wanda yai na hudu wato Gwani Nasiru Abdullahi Kibiya daga Kano domin su tafi tare da Marigayi Sheikh Ja’afar Mahmud Adam rahimahullah.
Gwani Dr. Rufa’i ya kawo cewar Gwani Ja’afar da Gwani Nasiru sun je Saudiya amma sai suka tarar akwai matakin izu sittin da tafsiri. To sai hukumar Dan fodio ta bukaci Mallam Ja’afar ya shiga wannan aji yayin da Gwani Nasiru zai tsaya a izu sittin.
Cikin ikon Allah Mallam Ja’afar ya yarda ya amince kuma ya yi kokari ya yi hobbasa ya rera karatu mai gamsarwa kuma ya amsa abinda Allah Ya kaddara zai amsa daga tafsiri – ba tare da ya yi shirin haka ba.
MATAKIN DA MALLAM JA’AFAR YA SAMU A MUSABAKAR DUNIYA
Dr Rufa’i ya kawo cewar Mallam Ja’afar bai samu matsayi ba wato daga na daya zuwa na biyar. Kuma daya daga cikin dalilan shi ne rashin sanin Mallam Ja’afar cewar zai yi Tafsiri har sai da aka bukata daga gare shi.
Gwani Yahuza kuma ya ce Mallam Ja’afar bai ci musabaka ba wato bai fito a na daya zuwa na biyar ba amma dai ya samu mataki na shida ne a Musakar Duniya – a hirar da akai da shi a Wisal Hausa Tv tare da Goni Umar Al-Bashir Borno.
A littafin ‘Ayyami’ na Dr Sani Rijyar Lemo ya kawo cewar Mallam Ja’afar ya samu mataki na uku a musabakar duniya.
WALLAHU A’ALAM.
Kuma Mallam Ja’afar ya fada darasinsa na saukar tafsirin Alkur'ani a Kano cewar an ba shi gagarumar kyautar naira dubu daya da ya ci musabaka. A ciki ya sayi Machine Suzuki naira dari bakwai da hamsin.
Allah Ya ji kansa da rahama.
BAYAN MUSABAKAR DUNIYA
Bayan dawowar Mallam Ja’afar daga Musabakar Duniya sai aka nada shi daya daga Alkalan Musabakar Kano a karamar hukuma 1988. Sai dai bai dade ba ya tafi Madina karatu.
A kuma wannan shekarar Sheikh Zarban ya zo Nigeria daga Madina domin yi wa wadanda suka kammala Sakandare mukabala ko za su samu damar shiga Jami’ar Madina. To sai aka ci rashin sa’a ya zo daidai da lokacin yan makaranta suna hutu. To daga nan sai aka nuna masa yan takarar da za su wakilci Kano a Musabakar Kasa ta 1988 a makarantar SAS Kano. To sai akai dace an dauki Mallam Ja’afar cikin mai ba su horo wato TADRIBI. Sheikh Zarban ya ce yana neman yan makarantar Gwale ko nan S.A.S. Sai aka nuna Mallam Ja’afar aka ce ga daya daga ciki.
Daga nan su ka je Masaukin Sheikh Zarban akai musu ‘interview’ su biyar. Mallam Ja’afar ne na karshen shiga kuma shi ne wanda ya samu nasara. Sheikh Zarban ya ce ‘duk abinda ake nema ka na da shi, ka cancanta sai dai idan ka yarda za ka maimaita Sakandare a can idan ka je tunda yanzu ba ka gama Sakandare ba’ – a lokacin Mallam Ja’afar saura shekara daya ya gama Sakandare.
Mallam ya ce ya yarda. Da ma shekara uku yana neman Madina bai samu ba. Shekara da ta zagayo aka aikowa Mallam Ja’afar ‘ADMISSION’. A ka ci sa’a kuma ya gama Sakandare a daidai lokacin. Da ya je Madina aka sake masa interview wasu mutane daban kuma su ka je lallai ya cancanci ya shiga Jami’a kai tsaye ba tare da ya shiga Sakandare a can ba.
( Interview da Mallam Ja’afar a gidan talabijin na Maiduguri).
Gwani Rufa’i ya fada a littafinsa cewar su biyu ne kadai aka gaiyata don tantancesu.
Mallam Ja’afar ya kammala Madina 1989 – 1993
Ya kammala Master Degree a Sudan.
Saura kadan ya kammala Ph.D a Jami’ar Usmanu Dan Fodio dake Sakkwato aka harbe shi a ranar Jumu’a yana jan Sallar Asuba 13 ga Afrilun 2007.
Allah Ya ji kansa Ya gafarta masa.
Za ku iya karanta tarihin musabakar Mallam Ja'afar a https://web.facebook.com/AminuSakwaya/posts/2577843915766157