Wednesday, 11 August 2021

2012 KATSINA NATIONAL MUSABAQAH RESULTS

2012 KATSINA MUSABAQAH RESULTS

26TH NATIONAL QUR’ANIC RECITATION COMPETITION

ORGANIZED BY MUSABAQAH FOUNDATION FOR QUR’ANIC RECITATION IN NIGERIA

CENTER FOR ISLAMIC STUDIES, USMANU DANFODIO UNIVERSITY, SOKOTO, NIGERIA.

FIRST CATEGORY: 60 HIZB & TAFSEER MALE SESSION

1st: Mujtaba Muhammad Ibrahim Katsina
2nd: Abu Zaid Hamza Nasarawa
3rd: Muhammad Dahiru Musa Khaleel Plateau
4th: Mahmud Muhammad Kebbi
5th: Adam Umar Ali Adamawa

FIRST CATEGORY: 60 HIZB & TAFSEER FEMALE SESSION

1st: Badi’atu Abubakar Usman Bauchi
2nd: Fatima Umar Harun Yunus Borno
3rd: Khadija Tanimu Abdullahi Plateau
4th: Zainab Yusuf Abubakar Abaji Abuja
5th: Zainab Ali Muhammad Sokoto

SECOND CATEGORY: 60 HIZB
MALE SESSION

1st: Abdulbasit Abdulkarim Isa Nasarawa
2nd: Abbas Muhammad Salis Zakariyya Bauchi
3rd: Yusuf Muhammad Sheikh Aliyu Kano
4th: Najeeb Alhassan Sa'id Adamawa
5th: Muhammad Sadis Harun Yobe

SECOND CATEGORY: 60 HIZB
FEMALE SESSION
1st: A’isha Abdulmuttalib Yobe
2nd: Zainab Gambo Salihu Muhammad Borno
3rd: Amina Auwal Muhammad Ahmad Kano
4th: Habiba Usman Usman Jibril Niger
5th: Maryam Shuaib Haruna Sulaiman Gombe

THIRD CATEGORY: 40 HIZB
MALE SESSION

1st: Aliyu Saleh Aliyu Dutse Jigawa
2nd: Muhammad Inuwa Adam Umar Kano
3rd: Abubakar Umar Balarabe Zaria Kaduna
4th: Nura Shehu Abubakar Al-Ulawi Zamfara
5th: Sadiq Alabi Akolade Kwara

THIRD CATEGORY: 40 HIZB
FEMALE SESSION

1st: Mujahida Sagir Bauchi
2nd: Sayyara Yusuf Ahmad Shitu Kano
3rd: Khadija Aliyu Hussain Adam Jigawa
4th: Rukayya Muhammad Ibrahim Katsina
5th: Maimunatu Adam Kaduna

FOURTH CATEGORY: 20 HIZB
MALE SESSION

1st: Abdullahi Ibrahim Bello Hassan Kano
2nd: Usman Lawal Abubakar Na'Allah Zamfara
3rd: Nazifi Muhammad Kebbi
4th: Aliyu Garba Ibrahim Sulaiman Birnin kudu Jigawa
5th: Aliyu Isma'il Muhammad Gombe

FOURTH CATEGORY: 20 HIZB
FEMALE SESSION

1st: Hajara Muhammad Auwal Niger
2nd: Safiya Umar Dago Kebbi
3rd: Shamsiyya Salihu Muhammad Adamawa
4th: Abida Muhammad Kaduna
5th: Hajara Abubakar Umar Plateau

FIFTH CATEGORY: 10 HIZB & TANGEEM MALE SESSION

1st: Jibril Sulaiman Hassan Plateau
2nd: Bukar Bukar Sadiq Ali Borno
3rd: Sani Abubakar Yar Adua Katsina
4th: Haruna Muhammad Yobe
5th: Abubakar Adamu Bauchi

FIFTH CATEGORY: 10 HIZB & TANGEEM FEMALE SESSION

1st: Asiya Yunusa Yusuf Muhammad Kano
2nd: Aminatu Hashim Bauchi
3rd: Aishatu Muhammad Ibrahim Katsina
4th: Aisha Bello Kaduna
5th: Rukayya Yahaya Tanko Jigawa

SIXTH CATEGORY: 2 HIZB
MALE SESSION

1st: Abubakar Abdulmalik Edo
2nd: Munir Ahmad Kebbi
3rd: Bolaji Umar Faruqi Olayinka Ogun
4th: Muhammad Al-amin Abdullahi Abuja
5th: Sameeru Abubakar Yaqub Kogi

SIXTH CATEGORY: 2 HIZB
FEMALE SESSION

1st: Hannatu Musa Yobe
2nd: Maryam Yusuf Adam Ringim
3rd: Aisha Muhammadul Amin Oyo
4th: Maryam Hashim Muhammad Gombe
5th: Hajaratu Abdulqadir Fulani Kwara

2011 JIGAWA NATIONAL MUSABAQAH RESULTS QUR’ANIC RECITATION COMPETITION

2011 JIGAWA MUSABAQAH RESULTS

https://web.facebook.com/AminuSakwaya/posts/2661518584065356

25TH NATIONAL QUR’ANIC RECITATION COMPETITION

ORGANIZED BY MUSABAQAH FOUNDATION FOR QUR’ANIC RECITATION IN NIGERIA

CENTER FOR ISLAMIC STUDIES, USMANU DANFODIO UNIVERSITY, SOKOTO, NIGERIA.

FIRST CATEGORY: 60 HIZB & TAFSEER MALE SESSION

1st: Tahir Mustapha Tahir Saleh Borno
2nd: Adam Umar Mayo Belwa Adamawa
3rd: Muhammad Dahir Musa Khalil Plateau
4th: Muhammad Bello Yobe
5th: Zahraddeen Abdallah Ali Kano

FIRST CATEGORY: 60 HIZB & TAFSEER FEMALE SESSION

1st: Khadija Yunus Ilyas Kano
2nd: Halima Sa’ad Sulaiman Adamawa (rahimahallah)
3rd: Aminatu Muhammad Yusuf Zamfara
4th: Khadija Tanimu Abdullahi Plateau
5th: Fatima Sharu Hudu Nasarawa

SECOND CATEGORY: 60 HIZB
MALE SESSION

1st: Aliyu Tukur Bakura Zamfara
2nd: Aliyu Harazimi Asim Lawal Kano
3rd: Abdurrahman Ahmad Salis Musa Kaduna
4th: Abdulbasit Abdulkarim Isa Nasarawa
5th: Rumaidu Ahmad Muhammad Sayyaed Borno

SECOND CATEGORY: 60 HIZB
FEMALE SESSION

1st: Zubaida Ibrahim Jibril Nasarawa
2nd: Fadimatu Bello Muhammad Zamfara (rahimahallah)
3rd: Asiya Usman Jibrilla Adamawa
4th: Shafa’atu Abdullahi Ibrahim Kano
5th: Musharrafa Isa Abubakar Bauchi

THIRD CATEGORY: 40 HIZB
MALE SESSION

1st: Abdullahi Adam Usman Assakawiy Jigawa
2nd: Abdurrahman Adam Isa Gwale Kano (rahimahullah)
3rd: Nazir Abubakar Sadiq Koko Kebbi
4th: Yusuf Salis Yusuf Muhammad Plateau
5th: Hafiz Hadi Aliyu Maikanti Zamfara

THIRD CATEGORY: 40 HIZB
FEMALE SESSION

1st: Amina Muhammad Auwal Kano
2nd: Fatima Mukhtar Abubakar Adamawa
3rd: Fa’iza Muhammad Ibrahim Edo
4th: A’isha Abdulmuttalib Yobe
5th: Khadija Ishaq Abdulkarim Nasarawa

FOURTH CATEGORY: 20 HIZB
MALE SESSION

1st: Sulaiman Mainasara Wambai Dutse Jigawa
2nd: Muhammad Sirajo Abdullahi Usman Zamfara
3rd: Muhammad Baba Hassan Nasarawa
4th: Muhammad Umar Yobe
5th: Muhammad Habeeb Suleiman Saminu Kaduna

FOURTH CATEGORY: 20 HIZB
FEMALE SESSION

1st: A’isha Dahiru Ibrahim Jigawa
2nd: Hajara Abubakar Umar Plataeu
3rd: Fatima Adam Yobe
4th: Ummu-Kulthum Muhammad Ilu Nasarawa
5th: Habiba Yaqub Yunus Borno

FIFTH CATEGORY: 10 HIZB & TANGEEM MALE SESSION

1st: Aliyu Usman Audi Kofar bai Katsina
2nd: Mansur Muhammad Isa Shinkafi Zamfara
3rd: Haruna Muhammad Muhammad Sokoto
4th: Muhammad Umar Abuja
5th: Saifullahi Abubakar Isa Inuwa Jigawa (rahimahullah)

FIFTH CATEGORY: 10 HIZB & TANGEEM FEMALE SESSION

1st: Hindu Bello Saleh Jigawa
2nd: A’ishat Muhammad Katsina
3rd: Sa’adiyya Ibrahim Umar Bauchi
4th: Humairah Muhammad Lumbi Taraba
5th: Rumaisa Muhammad Gidado Adamawa

SIXTH CATEGORY: 2 HIZB
MALE SESSION

1st: Sadiq Alabi Kwara
2nd: Abubakar Abdulmalik Edo
3rd: Salim Hashim Gombe
4th: Wakas Abu Saleh Musa Lagos
5th: Marwan Ishaq Mas’ud Osun

SIXTH CATEGORY: 2 HIZB
FEMALE SESSION

1st: Rukayya Muhammad Abdullahi Jigawa
2nd: A’ishatu Muhammad Sani Niger
3rd: Maimunatu Hussaini Abubakar F.C.T Abuja
4th: Maryam Abubakar Zuma Kebbi
5th: Ni’imatu Zakaria Ajoke Osun

TARIHIN MUSABAKAR SHEIKH JAFAR

TAKAITACCEN TARIHIN MUSABAKAR SHEIKH JA'AFAR MAHMUD ADAM KANO ( Rahimahullah)

Kafin mai karatu ya fara karantawa ya kamata ya san mai wannan rubutu ba masanin tarihi ba ne, mai binckike ne kawai akan harkar Musabaka. Sannan ya yi amfani da laccocin Mallam Ja'afar da Maganganun wasu Malaman Qur'ani kamar Gwani Yahuza Gwani Dan Zarga Kano da kuma littafai da aka rubuta. Wasu daga cikin littafan sun hada da ' Tatawwur ilmul Qira'at da Dr. Rufa'i Uba Hamza Gabari da kuma Ayyami na Dr. Muhammad Sani Rijiyar Lemo' wadanda suka kawo tarihin rayuwar Mallam Ja'afar.
Don haka mai rubutu ba ra'ayinsa yake kawowa ba.
Don Allah duk inda aka ga kuskure amanar ilimi ce a gyara. Don haka kada mutum ya yi shiru.
Abinda yake daidai kuwa to daga Allah ne.
Allah Ya ba mu ikon rubutawa daidai tare da ikhlasi.
Kafin mu fara kada mu manta Mallam Ja’afar Alaramma ne, Gwani ne a karatun Alkur’ani. Ya yi haddarsa da allo, kuma ya yi satu ba daya ba biyu ba a nan Fagge dake Kano a wajen Alaramma Dawud 1977 zuwa 1978.
An haifeshi a 1962 ko 1965.
Ya koyi Tajwidi a hannun wani Malami mutumin Misra Sheikh Abdul’aziz ali AlMustafa.
Da sunan Allah Mai Rahama Mai jin kai.
MUSABAKAR KASA TA FARKO 1986
Gwani Rufa'i ya kawo cewar a Musabakar Kasa ta farko wacce aka gudanar a Sakkwato 1986 Mallam Ja'afar yana daga cikin mutum ukun da suka wakilci Kano a izu sittin wanda shi ne kololuwar mataki a wancan lokacin tunda ba bu sittin da tafsiri. To a wannan lokaci Mallam Ja'afar sai yai na hudu a matakin Kasa kamar yadda Gwani Rufa'i ya fada a shafi na 699. Sai dai a shafi na 683 sunan Mallam Ja'afar ya zo a na biyar. Yayinda yan takarar Borno su ka zo na biyu, da na uku, da na hudu; su ne Idris Isa Idris, Sharif Dahir Musa da kuma Muhammad Dungus. Mallam Ja'afar kuma yazo na biyar daga Kano sai Marigayi Gwani Aminu Zaina ya zo na daya daga Kano. Gwani Aminu Zaina da Goni Idris Isa Idris su suka wakilci Nigeria a Musabakar Malik Abdul'aziz a Saudiyya sai dai sun je a makare, ba su samu damar sharakawa ba - kamar yadda Gwani Rufa'i ya kawo a 696 da 697.
MUSABAKAR KASA TA BIYU 1987
To a shekarar da ta gewayo, 1987, sai Mallam Ja'afar ya sake fafata Musabaka inda ya yi na biyu a Jahar Kano. Yayin da Gwani Nasiru Abdullahi Musa Kibiya ya yi na farko.
Wannan ya ba wa Mallam Ja’afar damar shiga cikin sahun mutane uku da za su wakilci Kano a Musabakar Kasar da za a gabatar a Maiduguri. Cikin ikon Allah da rahamarSa da zabinSa sai Mallam Ja'afar ya zo na daya yayinda yan takarar Borno suka zo na biyu da na uku. Daya daga cikin yan takarar Jahar Kano kuma sai ya zo na hudu, yayinda dayan dan takarar Borno ya zo na biyar. Yan takarar Bornon su ne Goni Jidda Muhammad Khalil (na biyu) da Goni Wali Ibrahim Kolomi (na uku) sai kuma Goni Jibril Haruna Abdullahi (na biyar). Dan takarar Jahar Kanon kuma shi ne Gwani Nasiru Abdullahi Musa ( na hudu).
To kaddarar Allah idan ta zo ba makawa sai ta faru. Wannan sakamako bai yi wa mutanen Borno dadi ba. To dama shi sakamako ba ya nuna wani ya fi wani. Akwai wanda ya san wane da wane sun fi shi karatu nesa ba kusa ba, to amma sai Allah Ya ba shi nasara a Musabaka bai ba wa wancan ba.
Saboda yan mintina ne kwata kwata ba su wuce ashirin mutum zai zo yai karatu. Wani ya tashi da danjoji da yawa wani kuma da danjoji kadan yayin da wani ya tashi ba ko danja daya!
Allah Ya na zabar wanda ya so cikin takara ya ba shi nasara ba don ya fi saura ba. A'a sai don dalilin da shi Allah din ya barwa kansa sani. Sannan Allah na iya zabar mutum Ya ba shi nasara domin Ya jarrabashi Ya ga ko zai yi takama da ji-ji da kai da girman kai ko ya rena mutane ko yana jin ya fi kowa karatu. Sannan Allah na jarrabar mutum kuma da rashin samun matsayi a Musabaka don ya ga ya ya zai yi? Zai ce wane da wane ne suka ka da ni ko kuma ya ce Allah ba ya sonsa ko ya kamata a ce shi yai na daya tunda ya fi saura karatu.
Shi ya sa ake son yan takara su kara sanya ikhlasi cikin karatunsa.
Allah Ya ba mu ikhlashi gaba daya.
To mu dawo maganar Sheikh Ja'afar rahimahullah.
Sakamakon musabakar 1987 bai yi mutanen Borno dadi ba. Wanna ta sanya hukumar Musabakar Borno fushi tare da kin shiga Musabakar da aka yi a shekarar da ta zagayo, 1988, a Kano.
( Hira da Gwani Yahuza Gwani Saleh dan Zarga da Goni Umar Al-Bashiri a tashar Talabijin ta Wisal Hausa Tv ).
Wannan kuma na iya shiga cikin dalilan da ya sanya lokacin da Mallam Ja'afar ya kammala Jami'ar Musulunci ta Madina a 1993 ya zo Borno a 1995 domin fara gabatar da Tafsiri a Masallacin Mallam Muhammad Indimi tasa ya hadu da kalubale da adawa mai yawa daga wasu daga cikin mutane da kuma malaman Borno (Sufaye) musamman idan sun tuna cewar shi ne fa kuma ya zo har gidansu ya lashe Musabakar, ga shi yanzu ya dawo yana kalubalantarsu da hujjoji.
Jama'a ku biyo mu in sha Allahu za mu sanya muku maganar Mallam Ja'afar da yake ba da labarin gaggan Malamai guda uku wanda ba bu ya su a Borno su ka je har wajen Abacha domin a hana shi Tafsiri - bayan sun je har wajen Gwamna ba su gamsu ba.
Dr. Gwani Rufa'i ya kawo cewar Mallam Ja'afar na yin Musabaka ne a wancan lokaci da salo irin na Sheikh Mahmud Khalil al-Husari - yayin da yan takabara ke kabbara saboda zalakar muryarsa.
MUSABAKAR DUNIYA TA SARKI ABDUL'AZIZ DAKE SAUDIYYA 1988
Sakamakon Musabakar Kasa ya nuna na daya da na biyu wato Sheikh Ja'afar da Goni Jidda Muhammad Khalil su za su wakilci Najeriya a Musabakar Duniya. To amma kamar muka kawo a sama mutanen Borno sun yi fushi don haka ba su yarda Goni Jidda ya wakilci Najeriya ba.
Wasu kuma na ganin Jami'ar Danfodio ya hana shi tafiya Musabakar Duniya saboda irin yanayi da kuma halin da kwamitin Jahar Borno ya nuna na kin amincewa da sakamakon Musabakar ta 1987.
To wanda yai na uku ma dan Borno ne wato Goni Wali Ibrahim Kolomi don haka ba za su yarda Cibiyar nazarin Addinin Musulunci ta Jami'ar Usmanu Dan Fodio dake Sakkwato (wanda sune suke gudanar da Musabakar) ta dauko shi ba.
A dalilin haka ya sanya Dan Fodio dauko wanda yai na hudu wato Gwani Nasiru Abdullahi Kibiya daga Kano domin su tafi tare da Marigayi Sheikh Ja’afar Mahmud Adam rahimahullah.
Gwani Dr. Rufa’i ya kawo cewar Gwani Ja’afar da Gwani Nasiru sun je Saudiya amma sai suka tarar akwai matakin izu sittin da tafsiri. To sai hukumar Dan fodio ta bukaci Mallam Ja’afar ya shiga wannan aji yayin da Gwani Nasiru zai tsaya a izu sittin.
Cikin ikon Allah Mallam Ja’afar ya yarda ya amince kuma ya yi kokari ya yi hobbasa ya rera karatu mai gamsarwa kuma ya amsa abinda Allah Ya kaddara zai amsa daga tafsiri – ba tare da ya yi shirin haka ba.
MATAKIN DA MALLAM JA’AFAR YA SAMU A MUSABAKAR DUNIYA
Dr Rufa’i ya kawo cewar Mallam Ja’afar bai samu matsayi ba wato daga na daya zuwa na biyar. Kuma daya daga cikin dalilan shi ne rashin sanin Mallam Ja’afar cewar zai yi Tafsiri har sai da aka bukata daga gare shi.
Gwani Yahuza kuma ya ce Mallam Ja’afar bai ci musabaka ba wato bai fito a na daya zuwa na biyar ba amma dai ya samu mataki na shida ne a Musakar Duniya – a hirar da akai da shi a Wisal Hausa Tv tare da Goni Umar Al-Bashir Borno.
A littafin ‘Ayyami’ na Dr Sani Rijyar Lemo ya kawo cewar Mallam Ja’afar ya samu mataki na uku a musabakar duniya.
WALLAHU A’ALAM.
Kuma Mallam Ja’afar ya fada darasinsa na saukar tafsirin Alkur'ani a Kano cewar an ba shi gagarumar kyautar naira dubu daya da ya ci musabaka. A ciki ya sayi Machine Suzuki naira dari bakwai da hamsin.
Allah Ya ji kansa da rahama.
BAYAN MUSABAKAR DUNIYA
Bayan dawowar Mallam Ja’afar daga Musabakar Duniya sai aka nada shi daya daga Alkalan Musabakar Kano a karamar hukuma 1988. Sai dai bai dade ba ya tafi Madina karatu.
A kuma wannan shekarar Sheikh Zarban ya zo Nigeria daga Madina domin yi wa wadanda suka kammala Sakandare mukabala ko za su samu damar shiga Jami’ar Madina. To sai aka ci rashin sa’a ya zo daidai da lokacin yan makaranta suna hutu. To daga nan sai aka nuna masa yan takarar da za su wakilci Kano a Musabakar Kasa ta 1988 a makarantar SAS Kano. To sai akai dace an dauki Mallam Ja’afar cikin mai ba su horo wato TADRIBI. Sheikh Zarban ya ce yana neman yan makarantar Gwale ko nan S.A.S. Sai aka nuna Mallam Ja’afar aka ce ga daya daga ciki.
Daga nan su ka je Masaukin Sheikh Zarban akai musu ‘interview’ su biyar. Mallam Ja’afar ne na karshen shiga kuma shi ne wanda ya samu nasara. Sheikh Zarban ya ce ‘duk abinda ake nema ka na da shi, ka cancanta sai dai idan ka yarda za ka maimaita Sakandare a can idan ka je tunda yanzu ba ka gama Sakandare ba’ – a lokacin Mallam Ja’afar saura shekara daya ya gama Sakandare.
Mallam ya ce ya yarda. Da ma shekara uku yana neman Madina bai samu ba. Shekara da ta zagayo aka aikowa Mallam Ja’afar ‘ADMISSION’. A ka ci sa’a kuma ya gama Sakandare a daidai lokacin. Da ya je Madina aka sake masa interview wasu mutane daban kuma su ka je lallai ya cancanci ya shiga Jami’a kai tsaye ba tare da ya shiga Sakandare a can ba.
( Interview da Mallam Ja’afar a gidan talabijin na Maiduguri).
Gwani Rufa’i ya fada a littafinsa cewar su biyu ne kadai aka gaiyata don tantancesu.
Mallam Ja’afar ya kammala Madina 1989 – 1993
Ya kammala Master Degree a Sudan.
Saura kadan ya kammala Ph.D a Jami’ar Usmanu Dan Fodio dake Sakkwato aka harbe shi a ranar Jumu’a yana jan Sallar Asuba 13 ga Afrilun 2007.
Allah Ya ji kansa Ya gafarta masa.

Za ku iya karanta tarihin musabakar Mallam Ja'afar a https://web.facebook.com/AminuSakwaya/posts/2577843915766157

Sunday, 15 September 2019

Privacy Policy

Privacy Policy
I developer sakwaya built this app as a free ad-supported app. This SERVICE is provided by me and is intended for use as is.

This page is used to inform my app users and/or website visitors regarding my policies with the collection, use, and disclosure of Personal Information if anyone decided to use my Service.

If you choose to use my Service, then you agree to the collection and use of information in relation with this policy. The Personal Information that I collect are used for providing and improving the Service. I will not use or share your information with anyone except as described in this Privacy Policy.

The terms used in this Privacy Policy have the same meanings as in my Terms and Conditions, which is accessible at my app, unless otherwise defined in this Privacy Policy.

Information Collection and Use

For a better experience while using my Service, I may require you to provide me with certain personally identifiable information, including but not limited to [users name | address | location | pictures | device identifier]. The information that I request is [retained on your device and will be retained by me and used as described in this privacy policy.

The app does use third party services that may collect information used to identify you. We’ll partner with Google and use a unique identifier on your device to serve only non-personalized ads. For information about how Google uses your mobile identifier please visit: https://policies.google.com/technologies/partner-sites.

Log Data

I want to inform you that whenever you use my Service, in case of an error in the app I collect data and information (through third party products) on your phone called Log Data. This Log Data may include information such as your devices’s Internet Protocol (“IP”) address, device name, operating system version, configuration of the app when utilising my Service, the time and date of your use of the Service, and other statistics.

Cookies

Cookies are files with small amount of data that is commonly used an anonymous unique identifier. These are sent to your browser from the website that you visit and are stored on your devices’s internal memory.

This Services does not uses these “cookies” explicitly. However, the app may use third party code and libraries that use “cookies” to collection information and to improve their services. You have the option to either accept or refuse these cookies, and know when a cookie is being sent to your device. If you choose to refuse my cookies, you may not be able to use some portions of this Service.

Service Providers

I may employ third-party companies and individuals due to the following reasons:

To facilitate my Service;
To provide the Service on my behalf;
To perform Service-related services; or
To assist us in analyzing how my Service is used.
I want to inform users of this Service that these third parties have access to your Personal Information. The reason is to perform the tasks assigned to them on my behalf. However, they are obligated not to disclose or use the information for any other purpose.

Security

I value your trust in providing me your Personal Information, thus i am striving to use commercially acceptable means of protecting it. But remember that no method of transmission over the internet, or method of electronic storage is 100% secure and reliable, and I cannot guarantee its absolute security.

Links to Other Sites

This Service may contain links to other sites. If you click on a third-party link, you will be directed to that site. Note that these external sites are not operated by me. Therefore, I strongly advise you to review the Privacy Policy of these websites. I have no control over, and assume no responsibility for the content, privacy policies, or practices of any third-party sites or services.

Children’s Privacy

This Services do not address anyone under the age of 13. I do not knowingly collect personal identifiable information from children under 13. In the case I discover that a child under 13 has provided me with personal information, I immediately delete this from my servers. If you are a parent or guardian and you are aware that your child has provided me with personal information, please contact me so that I will be able to do necessary actions.

Changes to This Privacy Policy

I may update my Privacy Policy from time to time. Thus, you are advised to review this page periodically for any changes. I will notify you of any changes by posting the new Privacy Policy on this page. These changes are effective immediately, after they are posted on this page.

Contact me

If you have any questions or suggestions about my Privacy Policy, do not hesitate to contact me.

Friday, 31 August 2018

AL-GHADIR: KALUBALE GA YAN SHI'A

AL-GHADIR:

KALUBALE GA ‘YAN SHI’A

✍ Dr. Mansur Sokoto
18/12/1434M
22/10/2013M

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

*INGANTACCEN LABARIN GHADIR:*

Ma’anar Ghadir:

Kalmar Ghadir a larabce, tana nufin wurin da ya tara ruwa da ciyawa.

“Ghadir Khum” sunan wani tafki ne da yake a yankin Juhfa, kilomita 15 daga Rabigh. Nisan sa daga Makka kilomita 160 ne.

Labarin Ghadir:

Annabi Sallallahu Alaihi wa Sallam ya aiki Khalid dan Walid a matsayin kwamandan rundunar da za ta yi yaki a kasar Yaman daf da fara aikin Hajjin shekara ta 10H, hajjin da Manzon Allah Sallallahu Alaihi wa Sallam da kansa ya jagoranta.

Bayan da rundunar musulmi ta ci nasara sai Manzon Allah Sallallahu Alaihi wa Sallam ya aika Sayyidi Ali don ya kula da sha’anin Ganimar da aka samu.

Ali Radhiyallahu Anhu ya raba Ganima, kuma ya cire hakkin Manzon Allah Sallallahu Alaihi wa Sallam na Khumusi kamar yadda Alkur’ani ya zayyana. Daga ciki kuma ya cire ma kansa wata kuyanga da ta ba shi shawa.

Sayyidi Ali bai bata lokaci ba ya zarce zuwa Makka don ya riski maigidansa Sallallahu Alaihi wa Sallam a wurin aikin Hajji. Ya kuma wakilta wani daga cikin sojoji akan sauran aikin da ya rage.

Domin ya dadada ran sojojin, wakilin Sayyidi Ali ya raba ma su tufafi kyawawa daga cikin abin da aka ganimanto. Ya kuma yi ma su izini kowa ya hau rakumin da yake so daga cikin kayan Ganima. Kafin haka, sojoji sun gabatar da bukatar haka ga Sayyidi Ali amma bai amince ba. Sai ya ce ma su, rabonku sai an je Madina.

Sojojin wannan runduna sun hadu da Sayyidi Ali tare da Manzon Allah Sallallahu Alaihi wa Sallam a kan hanyar su ta dawowa bayan gama aikin Hajji. Sayyidi Ali ya nuna rashin jin dadinsa a kan wannan rabo da aka yi kafin lokacin yinsa.  Nan take ya yi umurni duk su sauka daga rakuman, suka kuma mayar da tufafin da aka raba masu. Rayukansu sun baci matuka a kan haka kuma sun kai karar sa ga Manzon Allah Sallallahu Alaihi wa Sallam suna zargin sa da cewa ya kuntata masu.

Manzon Allah Sallallahu Alaihi wa Sallam ya iso Ghadir Khum, kuma ya lura da fushi a fuskar wadannan sojoji. Ya yi huduba yana tambayar su ((ألستُ أولى بالمؤمنين من أنفسهم))؟! “Ashe ban fi muminai cancanta da kawunansu ba?” Suka ce masa, haka ne. Sai ya ce, ((فمن كنت مولاه، فعلي مولاه)) “To, duk wanda nake majibincinsa Ali ma majibincinsa ne”. Ma’ana, bai dace ku bata ranku a kan hukuncin da ya yi ba.

Da wannan babban jagora ya kwantar da wannan rikici da rashin fahimta, ya kuma nuna wajabcin a yi ma jagora da’a, sa’annan ya bayyana matsayin dan uwansa Sayyidi Ali a wurin muminai. Sojojin suka ba shi hakuri, suka gane matsayinsa, suka wuce Madina tare da sauran ayarin mahajjata da suke tare da shi.

Wannan shi ne abin da ya faru. Illa iyaka.



TATSUNIYAR GHADIR

‘Yan Shi’a sun ribaci wannan abin da ya faru kuma ya zo ya wuce kamar sauran ire-irensa. Suka fankama shi, suka fadada shi, suka mayar da shi wani gagarumin bukin nadin sarauta. Suka kuma jefi duk Sahabban Manzon Allah Sallallahu Alaihi wa Sallam da kin Allah da kauce ma gaskiya, da jayayya da wannan nadi da suka ce an yi.

Wannan akidar ta Ghadir a matsayin ranar buki ba a san ta a cikin tarihi ba sai bayan sama da shekaru 340 gwamnatin Shi’a ta Buwaihawa ta kago wannan bidi’a a kasar Iraqi. Suka mayar da ranar 18 ga watan Dhul Hajji a matsayin ranar wannan buki ta kowace shekara. Sukan taru a wurin kaburburan manyansu suna ta kururuwa suna la’antar masoyan Allah wadanda suka ce sun kauce ma umurni Manzon Allah Sallallahu Alaihi wa Sallam da ya bayar na mika mulki ga maigida Sayyidi Ali.

Sun kago ruwayoyi barkatai a kan falalar wannan rana, cikin su har da cewa wai, Imam Ar-Ridha ya ce, da mutane sun san matsayi da falalar wannan rana da Mala’iku sun rinka musafaha da su har sau goma a kowace rana.

Haka kuma sun kitsa tatsuniyoyi masu nuna wai, manyan Sahabbai sun yi ma Ali mubaya’a amma a munafurce, sannan suka shirya makarkashiyar kashe Manzon Allah Sallallahu Alaihi wa Sallam. A cikin su kuma wai har da duk sauran tara daga cikin mutane goma da Manzon Allah Sallallahu Alaihi wa Sallam ya yi ma su bushara da aljanna.



KALUBALE GA ‘YAN SHI’A

Muna kalubalantar ‘yan Shi’a a kan wannan batu da wadannan tambayoyi:

1.      Idan wannan magana ta Manzon Allah Sallallahu Alaihi wa Sallam cewa “Duk wanda nake majibincinsa Ali ma majibincinsa ne” tana nuna wajabcin shugabantar da shi, to me za ku ce game da fadar Manzon Allah Sallallahu Alaihi wa Sallam “Ko wace al’umma tana da amintacce, mu kuma amintaccenmu a cikin wannan al’umma shi ne Abu Ubaida”? Wa ya fi cancanta a cikin su kenan?
2.      Idan har gaskiya ne an yi wannan nadin kamar yadda kuke cewa, me ya sa ba a umurci Sayyidi Ali da ya ci gaba da ba da Sallah ba musamman bayan da ciwon ajali ya kama Manzon Allah Sallallahu Alaihi wa Sallam?
3.      Me ya sa ba ayi wannan bukin a zamanin da Sayyidi Ali yake Khalifa ba ko Sayyidi Al-Hasan ko a zamanin duk Imamanku goma sha daya da suka rayu kafin Malam Na-boye (Mahadinku) ya zo duniya? Me ya sa sai lokacin da Buwaihi Bafarise mai kamun kifi ya kafa gwamnati sannan aka fara wannan buki a shekarar 352H?
4.      Idan hudubar Ghadir tana nufin nadin sarauta ne, me ya sa ba ayi ta a Makka ba in da duk alhazan duniya suka taru su sama da mahajjata dubu dari?
5.      Ashe Manzon Allah Sallallahu Alaihi wa Sallam bai yi hudubobi a can Makka da Minna da Arafat ba? Me ya sa bai ware huduba ta musamman a kan wannan babbar maganar ta halifancin Sayyidi Ali ba?
6.      Ashe Manzon Allah Sallallahu Alaihi wa Sallam bai yi huduba a kan jinainai da dukiyoyi a ranar babbar sallah ba? Ashe bai yi ma al’umma wasici da muhimman abubuwan da suke bukatar sani ba? Ita wannan maganar ba ta kai muhimmancinsu ba ne ya manta da ita? Me ya sa sai da aka watse, kowa ya bi hanyar garinsu saura mutanen Madina kawai suka rage sannan ya yi wannan magana a cikin sunkurmin daji a tafkin Ghadir?
7.      Ya ya aka yi Sahabbai suka riwaito wannan hudubar ta Ghadir alhalin kun ce sun boye kaso biyu cikin uku na Alkur’ani masu bayyana falalar Ahlulbaiti?
8.      Kun ce duk rikicin da musulmi suka shiga a tsawon tarihi dalilin kauce ma wannan umurni na ranar Ghadir ne da sahabbai suka yi. Me ya sa Alkur’ani ya yi biris da labarin Ghadir?
9.      Allah Tabaraka wa Ta’ala ya saukar da sura ta musamman a cikin Alkur’ani kan maganar Hudaibiya da mubaya’ar da sahabbai suka yi ma Manzon Allah Sallallahu Alaihi wa Sallam da har wuri da bishiyar da suka yi mubaya’a a karkashinta, kuma ya ce ya yarda da su a kan haka bisa ga abin da ke cikin zukatansu na imani da ikhlasi. Kuma ya ce, a lokacin da suke yi ma Manzon Allah Sallallahu Alaihi wa Sallam mubaya’a hannun Allah yana saman nasu. Me ya sa idan har an yi wannan mubaya’a Allah bai kawo ta ba a cikin Alkur’ani?
10.  Mubaya’ar da mata suka yi ma Manzon Allah Sallallahu Alaihi wa Sallam ita ma Allah ya kawo labarinta cikin Suratul Mumtahana. Shin ita wannan mubaya’ar ta Ghadir ba ta da muhimmanci ne irin wannan mubaya’ar mata ko kuwa?

‘Yan Shi’a ku ji tsoron Allah! Malamanku suna zargin Manzon Allah Sallallahu Alaihi wa Sallam da boye wannan bayani wai a cikin Makka har suna cewa a kan wannan boyewar da ya yi sai da Allah ya saukar da ayar ”Ya kai wannan manzo ka isar da sakon da aka saukar ma ka daga wurin Ubangijinka. Idan kuwa har ba ka yi ba to, ba ka isar da sakonsa ba. Kuma Allah zai kare ka daga mutane”. To, sannan wai, ya tsaya a Ghadir Khum ya isar da wannan sako. Ku ji tsoron Allah! Ku darajanta manzonsa, ku koma ga gaskiya.

Wallahi, Sayyidi Abubakar da Sayyidi Umar da Sayyidi Usmanu da ma duk sauran sahabbai almajiran Manzon Allah Sallallahu Alaihi wa Sallam ba su jiye ma Sayyidi Ali da kome. Kuma ba su da wani kwadayi ga duniya balle su nemi shugabanci. Allah Ta’ala da kansa cewa ya yi a kan su:

((للفقراء المهاجرين الذين أُخرجوا من ديارهم وأموالهم يبتغون فضلا من الله ورضوانا وينصرون الله ورسوله أولئك هم الصادقون))

“-A bayar da Fai’i- ga talakawa Muhajirai wadanda aka fitar da su daga gidajensu da dukiyoyinsu suna neman falala daga Allah da yarda, kuma suna taimakon Allah da manzonsa. Wadancan su ne masu gaskiya”

To, ka ji. An kore su daga garuruwansu, aka kwace dukiyarsu kuma a cikin zukatansu ba zaman gida ko mallakar dukiya ne a gabansu ba. Babban gurinsu shi ne taimakon Allah da manzonsa. Ka kuma ji Allah ya ce ma su masu gaskiya. Don Allah ta ina wadannan za su yi kwacen mulki kuma har su shirya ma Manzon Allah Sallallahu Alaihi wa Sallam makarkashiyar kisan sa?!

Ya Allah! Ka shiryar da bayinka, ka ceto su daga muguwar akidar da Farisawa ‘yan bautar wuta suka kago suka lullube ta da rigar musulunci don su halaka su. Allahumma Ameen.